Muhammad Ibrahim Matasa Mu Farka
Wannan shafi anyi shi ne domin wayar da kan matasa domin sune ƙashin bayan al-umma. Idan sun gyaru to al-umma ta gyaru
Rashin samun bayanai ke saka matasa su tsaya jira se gwamnati ko yan siyasa sun taimake su! Akwai matasan da suna gida amma sunfi karfin 10M a wata guda! Bincike zaka yi tuƙuru sannan ka zage dantse wajen aiki
Duk wanda Allah yake so ya shiryar dashi sai ya buɗe zuciyarsa domin ya amshi musulunci.
Matasa sune ƙashin bayan al'umma! Kada kayi sake wajen inganta rayuwarka
Idan kunce anyi mana ba dai dai ba wajen zaɓen waɗanda zasu wayar wa al'umma da kai akan sabon tsarin haraji sai ku tambayi kanku, manyanku suna ina aka ware ku? Da aka ware ku mene s**a yi a kai? Sabida haka ku sake shiri.
Babu Al'ummar da zata cigaba kota rabauta matukar matasan ta basa naiman ilimi da addini da kuma na sana'a tuƙuru dai dai da zamanin ta! Babu alkhairi ga matasan da basa neman ilimi
Babu alheri ga matasan da basu da sana'ar yi.
Babu alkhairi ga matasan da basu da aikin yi sai sata, ƙwace/fashi ko shaye shaye!
Ya ku al'umma ku tashi tsaye kudauki mataki akan gyara da saita lamarin matasa tun kafin su gagare kowa a gari ko anguwa.
Allah ka shiryatar mana da matasan mu ka gyara lamuranmu
Yana da matukar amfani mu kasance mutane masu hangen nesa da zurfin tunani sannan mu zamto tsintsiya ma daurin ki daya.
Al-ummar da kanta a hade yake to abu ne mai wuya kaga an keta tsakanin ta.
Menene dalilin da yasa kake/kike gani ya jawo mana rashin haɗin kai a yau?
26/09/2025
Wajibi ne ko wani matashi ya dage da neman na kan shi, kada ka taba tunanin roko ko daukar abin wani zai yaye maka talauci se dai ya sake jefa ka cikin kunci da tashin hankali.
25/09/2025
ALHAMDULILLAHI
Yan uwa mun samu ƙaruwa na 'yan biyu maza
Muna rokon ku saka su cikin addu'o'inku tare da mahaifiyarsu.
Nagode
Wannan shafi ba'a kafata don siyasa ba. Aikin ta shine wayar da kan matasa
Duk abinda zai damu musulmi Allah ka yaye mai.
Idan tunanin matasa ta sauya to sauyi ta samu.
Menene ke kawo sauyi cikin tunanin matasa?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Address
Zaria