Isah Rabe Kambarawa

Isah Rabe Kambarawa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Isah Rabe Kambarawa, Politician, Katsina.

12/06/2026

Barka da Ranar Dimokuraɗiyya Mai girma Gwamnan Talakawa Dr. Dikko Umaru Radda

BARKA DA RANAR DIMOKURAƊIYYA 2026

A madadin shugabancin Building Your Future Ambassadors’ Initiative (BYFAI) na Jiha, Shiyyoyi uku (3), Ƙananan Hukumomi talatin da huɗu (34), Mazaɓu ɗari uku da sittin da ɗaya (361) da kuma Rumfunan Zaɓe dubu shida da ɗari shida da hamsin da biyu (6,652), muna miƙa saƙon taya murna ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON, tare da ɗaukacin al’ummar Jihar Katsina bisa zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, 2026.

BYFAI na ƙara jaddada mubaya’arta ga Katsina State Government ƙarƙashin jagorancin Gwamna Raɗɗa bisa ƙoƙarin sauke nauyin amanar al’umma gwargwadon iko ta hanyar aiwatar da Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka (Building Your Future Strategic Policy – BYFSP), wanda ya zama ginshiƙin tafiyar cigaba a Jihar Katsina.

Ko shakka babu, kwalliya na cigaba da biyan kuɗin sabulu idan aka yi la’akari da ɗimbin nasarori da aka samu a kusan kowane fanni na rayuwar al’umma, musamman a ƙarƙashin manyan ginshiƙan BYFSP guda takwas: Gyaran Tsarin Gudanar da Ayyukan Gwamnati, Ilimi da Bunƙasa Ƙwarewa, Kula da Jin Daɗin Al’umma, Ƙananan da Matsakaitan Sana’o’i da Tattalin Arzikin Cikin Gida, Kiwon Lafiya, Noma da Bunƙasa Masana’antu, Tsaro, da kuma Haɓaka Kuɗaɗen Shiga na Cikin Gida (IGR).

Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara wa Mai Girma Gwamna lafiya, hikima da jagoranci nagari domin ci gaba da hidimtawa al’ummar Jihar Katsina, tare da ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da cigaba a faɗin jihar.

Barka da Ranar Dimokuraɗiyya!









Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Katsina State Television KTTV
Katsina State Radio Service -KTRS
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State
GMTD

10/06/2026

Masha Allah

MUJALLAR GINA MAKOMARKA TA BUƊE DAMAR KARƁAR MAƘALOLI KAN CIGABAN JIHAR KATSINA

Mujallar Gina Makomarka (MGM), wadda ke mayar da hankali wajen tattaunawa da nazarin matakan cigaba, nasarori, ƙalubale da kuma ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi wajen aiwatar da Daftarin Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka (Building Your Future Strategic Policy), ta sanar da buɗe damar karɓar maƙaloli daga jama'a domin bayar da gudunmawa ga ci gaban jihar.

Wannan dama ta shafi duk masu sha'awar bayar da gudunmawar ilimi, bincike, tunani da shawarwari kan fannoni daban-daban na rayuwa da s**a haɗa da ilimi, lafiya, noma, tattalin arziƙi, sana'o'i, muhalli, fasaha, zaman lafiya, harkokin matasa da mata, da sauran batutuwan da s**a shafi ci gaban Jihar Katsina.

Mujallar ta bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce bai wa 'yan jihar damar bayyana ra'ayoyinsu da shawarwarinsu cikin tsari mai ma'ana, tare da taimakawa wajen samar da mafita ga matsalolin da ke addabar al'umma da kuma ƙarfafa manufofin cigaban da gwamnatin jihar ke aiwatarwa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON.

An kuma jaddada cewa masu rubutu su nisanci cin mutumci, kalaman ɓatanci, cin zarafin gwamnati ko wani mutum, tare da kauce wa fadanci da banbaɗancin siyasa. Maimakon haka, ana ƙarfafa marubuta su mayar da hankali kan gabatar da hujjoji, bayanai da shawarwarin da za su taimaka wajen inganta rayuwar al'umma da ci gaban jihar.

Za a rinƙa wallafa zaɓaɓɓun maƙaloli a sabon shafin da Mujallar Gina Makomarka ta tanada domin karɓar gudunmawar marubuta, wanda zai kasance wani dandali na tattaunawa da musayar ra'ayoyi kan makomar Jihar Katsina.

Masu sha'awar aika maƙalolinsu za su iya yin hakan ta hanyoyi kamar haka:

1. Adireshin E-mail
2. Lambar WhatsApp: 08064175765

Mujallar ta yi kira ga malamai, masana, ɗalibai, ma'aikata, 'yan kasuwa, masu sana'o'i da sauran masu kishin jihar da su yi amfani da wannan dama wajen bayar da tasu gudunmawa domin gina Katsina mai ɗorewa da wadata ga kowa.

Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors (BYFA)
10 ga Yuni, 2026
24 ga Dhul-Hijjah, 1447 AH

Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Katsina State Government
Mustapha Shehu
Ibrahima Kaulaha Mohammed
Katsina State Television KTTV
Katsina State Radio Service -KTRS

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 09/06/2026

Alhamdulilllah

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 08/06/2026

Masha Allah
Allah Ya ƙara jagoranci Dr. Dikko Umaru Radda

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 04/06/2026

Allah Ya ƙara shiga lamuran Building Your Future Ambassadors
Dr. Dikko Umaru Radda 2027 Insha Allah

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 01/06/2026

Allah Ya ƙara jagoranci Building Your Future Ambassadors

Dr. Dikko Umaru Radda

01/06/2026

Mujallar Gina Makomarka @40

01/06/2026

The Architect of Building Your Future Strategic Policy Dr. Dikko Umaru Radda

01/06/2026

The Architect of Renewed Hope Agenda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Dr. Dikko Umaru Radda
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Katsina