Labarai24

Labarai24

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Labarai24, Media/News Company, Kano.

27/01/2026

APC ta musanta yi wa Bello Turji rajista a Zamfara

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya reshen jihar Zamfara, ta musanta yi wa riƙaƙƙen ɗanbindigar nan Bello Turji rajista a matsayin mamban jam'iyyar.

Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar a Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce ɓata-gari ne s**a kirkiro da katin na bogi domin ɓata wa jam'iyyar suna.

"Hankalin mu ya kai ga wani katin jam'iyyar mu na bogi da ake yaɗa wa ɗauke da hoton Bello Turji, inda ake cewa an yi masa rajista a jam'iyyar mu. Wannan ba gaskiya bane," in ji sanarwar.

Yusuf ya ce idan aka yi duba na tsanaki za a iya gane cewa katin na bogi ne.

"Babu wani mutum da za a iya yi wa rajista ba tare da lambar katin ɗan ƙasa ba wanda shi kuma Turji ba shi da ita. Don haka koƙari da wasu ke yi na shafa wa jam'iyyar bakin fenti bai yi nasara ba," in ji kakakin jam'iyyar ta APC a jihar Zamfara.

Binciken farlko da aka gudanar ya nuna cewa wannan kati na bogi da ake yaɗa wa na alaƙa da wani Babangida Aliyu Shinkafi wanda aka dakatar a baya bayan-nan daga shiga shirin yin katin laturoni na jam'iyyar a jihar saboda wasu ɗabi'u mara kyau da yake nuna wa.

An kuma alaƙanta shi da katin ne saboda a shafinsa na Facebook a fara ganin katin jam'iyyar.

Photos from Labarai24's post 27/01/2026

Tinubu ya yi tuntube ya fadi a ƙasar Turkiyya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi tuntube ya fadi na dan lokaci a ranar Talata a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da Shugaba Tinubu ke tafiya tare da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, a lokacin tarbar da aka shirya masa.

27/01/2026

Zargin badakalar Naira biliyan ɗaya: Kotu ta tsare shugaban hukumar KANSIEC da wasu mutane biyu

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), Sani Malumfashi, tare da Sakataren hukumar, Anas Muhammed Mustapha, da Ado Garba, mataimakin darakta, bisa zargin badakalar kuɗi har Naira biliyan ɗaya.

Mai shari'a James Omotosho ya umarci a tsare su a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, bayan sun musanta laifuka guda shida da hukumar ICPC ta tuhume su da su.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga Janairu domin duba buƙatar belinsu.

ICPC ta zarge su da karɓar kuɗaɗe Naira miliyan 450, Naira miliyan 310 da Naira miliyan 260 ba bisa ƙa’ida ba, tsakanin Nuwamba da Disamba 2024, wanda aka ce na haram ne.

19/01/2026

DA DUMI-DUMI: Gwamna Abba na ganawa da Tinubu a yayin da yake shirin sauya sheƙa zuwa APC

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a yanzu haka na ganawa da shugaban ƙasa Tinubu a fadar shugaban ƙasa dake Abuja kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Gwamnan sanye da jar hula da babbar riga ya isa fadar shugaban ƙasa da karfe 4:10 na yammacin yau.

02/01/2026

Da Dumi Dumi: Wata Babbar Kotu a Kano ta tabbatar da nadin Hon Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin mukaddashin Shugaban Jam'iyyar NNPP na Jahar Kano

Kotun ta amince da dakatarwar da aka yiwa tsohin shugaban jam'iyyar Dr. Hashimu Dungurawa yayin da ta umarce shi da kar ya kara shiga cikin lamarin ta har sai an saurari karar.

Shugabannin jam'iyyar daga Karamar Hukumar sa ne dai s**a dakatar da shi a cikin wannan satin, kuma s**a shigar da kara in da kotun ta sanya ranar 19 ga watan Janairu domin fara sauraron karar.

08/12/2025

Nan da 2026 Nijeriya za ta rika ba da bashin kudi ga wasu kasashen, in ji Remi Tinubu, uwargidan shugaban Nijeriya

Mene ne hasashenku?

Photos from Labarai24's post 06/08/2025

Yanzu - Yanzu

Ministan Tsaro Dr Edward Omane Boamah da Ministan Kula da Muhalli Dr Ibrahim Murtala Mohammed na ƙasar Ghana tare da wasu mutum shida sun rasa rayukansu a sanadiyar haɗarin helikwafta wanda ya auku ɗazu a yankin Ashanti na ƙasar.

06/08/2025

Kwamishinan da ya yi belin wanda ake zargin dilan miyagun kwayoyi ne a Kano, ya yi murabus

Kwamishinan sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye mukaminsa bayan da aka kammala bincike kan rawar da ya taka wajen bayar da beli ga wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.

Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta nuna cewa kwamishinan ya yi murabus ne domin kare mutuncin gwamnatin Kano da ke da akidar yaki da fataucin kwayoyi da sauran laifuka.

10/06/2025

In da na ci zaɓe nima sai na cire tallafin man fetur amma ba farar-ɗaya irin na Tinubu ba - Obi

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya ce da ya ci zaɓen da shi ma sai ya cire tallafin man fetur kuma ya kyale Naira ta neman wa kan ta daraja, kamar sai yadda shugaba Bola Tinubu ya yi.

Da ya ke magana a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a jiya Litinin, Obi ya ce da zai aiwatar da manufofin a hankali a hankali ba farar-ɗaya ba gaba-gaɗi irin na Tinubu ba.

Tsohon gwamnan na Anambra ya ce kowa ya san cewa dole ne a kawo karshen "baƙala da cin hanci da rashawa" da ke tattare da tsarin tallafin man fetur.

Obi ya yi tambaya kan inda kudaden da ake tarawa cire daga tallafin man fetur suke tun lokacin da aka cire shi, ya kara da cewa kudaden ya kamata a sanya su wajen yin aiyukan samar da "mahimman kayan more rayuwa".

Ya ce ba a samu wani gagarumin ci gaba ba tun bayan cire tallafin man fetur.

Ya kara da cewa da zai yi shawarwari da masu gudanar da aiki kan ingantaccen tsarin farashi na samfurin.

09/06/2025

Fitaccen Jarumi a masana'antar Kannywood Adam A. Zango ya yi haɗari a hanyar Kaduna zuwa Kano.

Mun samu labarin babu wanda ya rasa rai a haɗarin, sai dai an jikkata sosai, mota kuma ta yi ratsa-ratsa. Allah ya kyauta gaba, amin.

09/06/2025

Mijina bai yi sata ba kuma duk kudin da ya tara wa Nijeriya sun yi ɓatan-dabo - Maryam Abacha

Maryam Abacha, matar marigayi Janar Sani Abacha, tsohon shugaban soja na Najeriya, ta ce mijinta ya ajiye wa Najeriya kudi, amma aka wawashe su bayan rasuwarsa.

A wata hira da aka yi da ita a gidan talabijin na TVC, wacce jaridar TheCable ta rawaito, Maryam ta bukaci a kawo hujja da ke nuna cewa mijinta ya boye kudaden sata a kasashen waje.

Abacha ya mulki Najeriya a matsayin shugaban soja da kuma kwamandan rundunar sojin kasa daga 1993 zuwa 1998, kafin rasuwarsa a ranar 8 ga Yuni, 1998.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kwato wasu kaso-kaso na kudaden da ake zargin Abacha ya boye a bankunan kasashen waje.

A cewar rahotanni, daga shekarar 2020, an kwato sama da dala biliyan 3.624 daga cikin kudaden da Abacha ya boye.

“Wa ne shaida na kudaden da ake cewa an boye?” in ji Maryam.

“Ka ga hannu ko shaida cewa kudin na waje ne? Kuma kudin da mijina ya adana wa Najeriya, cikin 'yan watanni sun bace. Babu wanda ke magana a kan hakan.”

Ta ce yadda ake ci gaba da zargin mijinta alamar wani mummunan hali ne da ke addabar al’umma.

“Me yasa kuke dora wa wani laifi? Ko kabilanci ne ko bambancin addini ne ko me ke damun 'yan Najeriya?” in ji ta.

26/05/2025

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar babban baturan yan sanda na karamar hukumar Rano sakamakon wata hatsaniyar da ta faru da safiyar wannan ranar ta litinin bayan da wasu fustattuan matasa s**a afkawa babban baturan yan sandan.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan ya fitar SP Abdullahi Haruna ya ce babban baturan yan sandan na karamar hukumar ta Rano CSP Muhammad Baba Ali ya rasu ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Kano
700104