Amintacciya

Amintacciya

Share

Amintacciya

Zaku iya aiko mana da sahihan Labarai daga ko ina a fadin Duniya, ko wani saƙo da kuke son isarwa ta wannan number 👉07012613017 ko ta Email dinmu ✉️ 👉[email protected]

Photos from Amintacciya's post 14/09/2026

ALLAH SARKI: Yadda wata matashiya ta fashe da Kuka kenan lokacin da taje yiwa mahaifinta godiya a garejin sa bisa tsaya mata har ta kammala karatun ta da yai

14/09/2026

Yanzu haka Ana ruwa barayi sun shiga wani kauye da ake Kira Unguwar daudu duke word Funtua LG a jihar Katsina kamar yadda mazaunin yankin ya tabbatar mana

Photos from Amintacciya's post 14/09/2026

Zamfara Ta Cika Makil Yayin Da Marafa Ya Kaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa

ZAMFARA: Jihar Zamfara ta cika makil da dandazon jama’a a daren Litinin, yayin da ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NDC, Sanata Kabiru Marafa, ya kai ziyara jihar domin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa.

A yayin gangamin, Marafa ya gwangwaje wasu jiga-jigan jam’iyyar da manyan motoci na alfarma, inda ya bayyana cewa kowace mota da ya bayar ta yi daidai da motoci 100 da, a cewarsa, ’yan jam’iyya mai mulki ke iya bayarwa.

Marafa ya ce ’yan jam’iyya mai ci ba sa iya yin irin wannan kyauta, yana mai cewa tun bayan ficewarsa daga jam’iyyar ne aka daina yi wa talakawa da al’ummar Zamfara alheri.

Ya bayyana cewa yanzu da ya dawo, zai ci gaba da tallafa wa jama’a, yana mai cewa ya san idan ya fara, ’yan jam’iyya mai mulki za su kwaikwaye shi.

Dan takarar ya kuma bayyana cewa zai raba motoci har sau biyar, ga rukuni biyar na jiga-jigan yaƙin neman zaɓensa da na jam’iyyar NDC, daga sama har ƙasa.

Ya ƙara da cewa matasa da mata ma za su amfana da tallafin da zai bayar, domin rage musu matsin rayuwa da suke fama da shi a ƙarƙashin gwamnati mai ci.

Marafa ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi aiki tare da taimaka wa jama’a, yana mai cewa sauran bayanai za su biyo baya, yayin da zai ci gaba da ganawa da al’ummar Zamfara domin, a cewarsa, share musu hawayensu.

Ya kuma gode wa dandazon jama’ar da s**a halarci taron, tare da ba su haƙuri kan jinkirin da aka samu. Ya ce tun safe ya shigo jihar, amma yawan jama’ar da s**a tarbe shi ya hana shi ci gaba da gudanar da shirye-shiryensa har zuwa bayan ƙarfe 8 na dare.

14/09/2026

Ga kasashe 10 da s**a fi Arahar fetur a duk faɗin Afrika, Libya ce ta ɗaya Nigeria ta 10

Photos from Amintacciya's post 14/09/2026

GWANIN SHA'AWA: Yadda Sanatan Kano Takudu Kawu Sumaila ke gwangwaje Al'ummar wani kauye mai suna Zamba/Raya dake karamar hukumar Sumaila da hanya kenan bayan ganin halin da hanyar tasu ke ciki.

Al'ummar yankin sun bayyana wa jaridar Amintacciya cewa tunda suke babu wani shugaba da ya taba kawo koda ƙasa mota daya ne da niyyar yimusu hanya sai Sanatan.

Wacce fata kuke masa ?

14/09/2026

Wadannan sune jerin ƙasashe 10 mafi tsadar Fetur a ƙasashen Afrika, Malawi ce ta 1, South Africa ta 10

14/09/2026

A Libya Dari 7 (700 )ake full tank na mots akudinsu, wanda in aka canzashi akan kudin Nigeria baze kai dubu daya da dari 4 ba (1400).

Kuma har yanzu haka kasar ba tada shugaba mai cikakke iko mutum biyu ne ke riƙe da kasar matsayin cikin kwarya

Daga Abdulazeez Bin Ali

14/09/2026

INNALLAHI 🙆: Yanzun nan nayi full tank a 120k.

Kuma fa masu gidan man saida na fada musu ni dan jam'iyyar APC ne amma s**a ki suyi min ragi.

Inji Aliyu Auwal Danzaki

14/09/2026

TIRKASHI: Kasa da sa’o’i biyar da bude Siyar da Hannun Jarin Kamfanin Dangote Refinery, an saka hannun jari da ya kai kusan ₦1.5 tiriliyan.

Lallai, kasar nan akwai masu kudi!

Daga Abba Sani Pantami

14/09/2026

Idan kayi rashin sa’a da auren kyakkyawar mace mai munanan hali, na rantse duk wani abu mai kyau sai ya daina burgeka a duniya.

Hatta riga mai kyau sai ta fita a ranka, b***e azo kan motoci da sauran abubuwa.

Ji zakai a ranka ai duk wani abu mai kyau ba abun kirki bane.

Allah ka hadamu da abokan zama na gari, mutanen kirki, kuma masu tsoron ka.

Daga Mamuda Wappah

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amintacciya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kano.