Gwammaja Development Forum
Gwammaja
21/04/2026
Gwammaja Development Forum(G.D.F)
AMadadin shuagabancin wannan ƙungiya muna farin ciki gayyatarku zuwa wajen bikin Comrade Usaini Sani Adamu senator mai wakiltar Gwammaja B²
17/04/2026
SAƘON TAYA MURNA NA MUSAMMAN
A madadin Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Gwammaja Development Forum (GDF), muna miƙa saƙon taya murna ga abokin gwagwarmaya, Malam Fatihu Sani Imam, bisa samun wannan matsayi na zama cikakken Alkali a Kotun Shari’a.
Wannan nasara ba ƙarama ba ce, kuma alama ce ta ƙwazo, amana da jajircewa. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba shi ikon sauke wannan babban nauyi da aka ɗora masa cikin adalci, hikima da tsoron Allah.
Allah Ya sa wannan matsayi ya zama alheri ga al’umma baki ɗaya, Ya kuma ƙara masa ɗaukaka da nasara a rayuwarsa.
Allah Ya taya shi riƙo, Ya kuma sa ya zama abin koyi na nagarta. Ameen.
16/04/2026
GAYYATA TA MUSAMMAN DAGA GDF
Muna farin cikin gayyatar ku zuwa taron rantsar da daya daga cikin shugabannin Gwammaja Development Forum (GDF), Fatihu Sani Imam, a matsayin Alqalin Kotun Shari'a.
Rana: Juma'a, 17/04/2026
Lokaci: 10:00 na safe
Wuri: Ceremonial Court, High Court (Audu Bako Secretariat), Kano.Allah ya taya shi riko, ya sa ya gama lafiya. Amin. 🤲🏾✨
06/04/2026
GWAMMAJA DEVELOPMENT FORUM (GDF)
WALIMAR SALLAH DA YIWA KASA ADDU’A
A jiya ne ƙungiyar Gwammaja Development Forum (GDF) ta gudanar da walimar Sallah tare da yi wa ƙasa addu’o’i na musamman, kamar yadda shugabannin ƙungiyar s**a saba tsarawa a kowace shekara.
Taron ya gudana cikin yanayi na farin ciki da haɗin kai, inda wakilai da mambobin ƙungiyar s**a hallara domin ƙarfafa zumunci tare da tattauna muhimman batutuwan da s**a shafi cigaban al’umma.
A yayin taron, an yi addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Shugabannin ƙungiyar sun jaddada muhimmancin ci gaba da haɗa kai wajen gina al’umma mai ɗorewa.
Hakazalika, mahalarta taron sun bayyana jin daɗinsu bisa wannan shiri tare da yaba wa ƙungiyar GDF bisa jajircewarta wajen haɗa kan al’umma da kuma ƙoƙarin kawo cigaba a yankin Gwammaja.
Abubakar Tahir Musa
Media aid GDF
GDF @2026
20/03/2026
GWAMMAJA DEVELOPMENT FORUM (GDF)
SAKON BARKA DA SALLAH
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh
Cike da farin ciki da godiya ga Allah (SWT), muke mika sakon taya murna ga daukacin al’ummar Musulmi, musamman mazauna unguwar Gwammaja, bisa zagayowar wannan rana mai girma ta Eid al-Fitr.
Wannan rana ta zo ne bayan kwanaki na ibada, hakuri da juriya. Muna rokon Allah Ya karɓi dukkan ibadunmu, Ya gafarta mana kura-kuranmu, Ya sanya mu cikin bayinSa da Ya yanta daga wuta.
A wannan lokaci mai albarka, muna kira gare ku da ku kara dankon zumunci, ku rika taimakon juna, tare da yada zaman lafiya da kaunar juna a cikin al’umma.
Allah Ya maimaita mana irin wannan lokaci cikin koshin lafiya, imani mai karfi da yalwar arziki.
BARKA DA SALLAH
Taqabbalallahu minna wa minkum
— Gwammaja Development Forum (GDF)
13/03/2026
SAKON BARKA DA JUMA’A TA ƘARSHE A WATAN RAMADAN DAGA GDF
A wannan Juma’ar ƙarshe ta watan Ramadan mai albarka, GDF na taya daukacin al’ummar Musulmi murnar kaiwa wannan lokaci mai girma.
Wannan rana tana tunatar da mu muhimmancin ƙara ƙoƙari wajen ibada, neman gafarar Allah, da taimakon juna. Ramadan wata ne na rahama, gafara da ‘yantarwa daga wuta, don haka mu yi amfani da ragowar kwanakin wajen ƙara kusanci ga Ubangiji.
Muna roƙon Allah (SWT) Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kura-kuranmu, Ya kuma sa mu dace da falalar Lailatul Qadr.
Barka da Juma’a ta ƙarshe a Ramadan.
Allah Ya maimaita mana shi cikin koshin lafiya da zaman lafiya.
— GDF
23/02/2026
SAKON TAYA MURNA NA MUSAMMAN
Kungiyar Gwammaja Development Forum (GDF) na mika sakon taya murna ga daya daga cikin iyayenta, Alhaji Nura Abubakar (Ever), bisa samun karin girma zuwa mukamin Senior Manager (Audit) a Nigerian Independent System Operator (NISO).hukumar da ke kula da tsarin wutar lantarki na kasa.
Wannan karin girma wata babbar shaida ce ta kwarewa, rikon amana da jajircewa a aiki. Hakika, an dora kwarya a gurbinta.
Muna addu’ar Allah Ya kara daukaka, Ya sanya albarka a cikin wannan sabon matsayi, Ya kuma ba da ikon sauke wannan nauyi.
21/02/2026
18/02/2026
Allah yasa mu fara a Sa'a
Sakamakon Musabaka (Final) tsakanin makarantar Ta'alimuddin islamiyya da Nurul yakeen wadda Zauren Hadakar makarantun islamiyyun Gwammaja Magariba/isha hadin gwiwa da kungiyar Gwammaja Development Forum suke jagoranta daga bakin Alqali Fatihu sani Imam
08/02/2026
INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJI’ŪN
Mun samu labarin rasuwar Malam Aminu Rabiu Gwammaja, daya daga cikin iyayen ƙungiyoyi kuma jagora mai sadaukarwa ga matasa, musamman a Al-Ansar da Kwango Youth Development Association.
Marigayin ya rayu ne da jajircewa da himma, yana sadaukar da kansa wajen kawo ci gaban al’umma. Duk ayyukansa sun kasance na alheri, ba don yabo ba, sai don amfanin jama’a.
Kishinsa ga al’umma da hangen nesa sun sa ya zama ginshiƙi mai daraja a zukatan mutane.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa, Ya kuma ba iyalansa da al’umma haƙuri da juriya.
Āmīn.
06/02/2026
Gwammaja Development Forum (GDF)
BARKA DA JUMA’A
Yayin da watan azumi mai albarka ke gabatowa, muna roƙon Allah Ya kai mu lafiya, Ya ba mu ikon ibada, Ya kuma karɓi ayyukanmu na alheri.
Allah Ya sa wannan Juma’a ta zama mai cike da rahama, gafara, da amsawar addu’o’i. Ya tsarkake zukatanmu, Ya gyara al’amuranmu, Ya kuma shiryar da mu hanya madaidaiciya.
Kada mu manta cewa azumi dama ce ta gyaran hali, dama ce ta kusantar Ubangiji, kuma dama ce ta taimakon juna da yafiya.
Juma’a Mubarak.
اللهم بلغنا رمضان
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kofar Wakili Gwammaja Special Primary School
Kano