Excellency DailyTrust
News for all days from myself
10/03/2026
YAƘIN IRAN.....
Al'amura na neman rincaɓewa bayan da NATO ta fara fusata.....
Ga halin da aka wuni zuwa yammacin yau.....
IRAN
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yace Tehran tayi matuƙar shiryawa yaƙi saboda haka babu gudu babu ja da baya, a dai dai lokacin da yaƙi yake shiga kwana na 9 ( Al'Arabiyya English )
UAE
Ministan tsaron hadaddiyar daular Larabawa yace ƙasar ta kakkaɓo mizayil 12 da jirgi maras matuƙi 17 a sararin samaniyar kasar a hare haren da Iran ta kaddamar. ( Al'Arabiyya English )
TURAI
Tarayyar Turai tace babu wani ƙaramcin man fetur da nahiyar ke fuskanta a sakamakon yaƙin dake gudana a gabas ta tsakiya ( EU )
RASHA
Putin yace zasu baiwa sabon shugaban addinin Iran Mojtaba khamene'i gudunmawar data dace iya karfin su ( Vladimir Putin )
KUWAIT
Rundunar sojin saman Iran ta kaddamar da harin jirgi maras matuƙi a wani ɓoyayyen sansanon sojin Amurka a Kuwait a ranar Litinin ɗinnan. ( Irna News Agency )
GERMANY
Wani cansala a Jamus Friedrich Merz yace Iran ce cibiyar ta'addanci ta Duniya, kuma ya zama dole a shafe tarihin ta matukar Duniya tana neman zaman lafiya. ( Friedrich Merz X )
NATO
Kungiyar tsaro ta NATO ta lalata wani makami mai linzami da aka harbo daga Iran a gaɓar tekun Bahar Rum yayin da wasu ɓaraguzen makamin s**a faɗo a sassan wurin inji ma'aikatar tsaron Turkiyya. ( Al'Arabiyya News )
TURKEY - NATO
Turkiyya tace Nato ta sake kakkaɓo wani makami mai linzami na Iran a karo na biyu, "abinda ake fargabar cewa wani tarko ne na kokarin shigar da Nato yaƙin" ( Reuters )
AMURKA - TEHRAN
Jaridar Middle East Monitor ta wallafa wani faifan Videon harin Amurka a wata makaranta a Iran wanda aka rawaito a kalla yara 175 sun mutu, abinda Amurka tace adadin bai kai haka ba. ( Middle East Monitor )
UKRAINE
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce kasashe 11 sun nemi taimakon Kyiv kan yadda za a dakile jiragen saman Iran marasa matuka, wadanda Tehran ta harba a duk fadin Gabas ta Tsakiya a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren
09/03/2026
Anyi Zaben Supreme leader a Iran Wato magajin Ali khamenei alhussaini Jagoran juyin juya Hali na addinin musuluncin kasar Iran
Zuwa yanzu majalisar koli batafitar da sunaba anbar karnukan yahudawa Sunata cika Baki
Trump na Kasar American yace dole yakasance cikin masu zaben kokuma yacigaba da Neman rayuwar Wanda zasudaura
Israel tace duk Wanda yayadda aka nadasa a kujeran ayatollah Ali khamenei to dolene ta farauci rayuwarsa har sai Tayi nasarar kashesa
Zuwa yanzu suna baifitoba
Wasu sufito s**e Mujitabba Ali khamenei ne
Wasu Kuma s**e Ayatollah Ahmad Alamolhoda ne
Dadai wasunsu ma cewa suke Sabbin Jagoran na tsoron Harin Israel da American yasa suna ta tsoron karba
Bari sukuma yahudawan dangin birrai sugama cika Bakinsu Akan Iran tana tsoron bayyana Jagoran juyin juya Hali
Karabb zasuga anbayyanasa Nanda bada jimawa ba domin babu tsoro alamarin Iraniyawa
Yahudawa ke tsoron mutuwa
Munajiran muga wanene wannan da duk duniya tasa Ido akansa da baabayyanaba
Allah yasa Wanda yamaye gurbinsa yafi Wanda aka kashe zafi da Tsauri da fikira Amin
09/03/2026
🛡️ Lallai Duniya kice take da abubuwan mamaki. 🤔🤯
Jirgin ruwa na Dufuna mai shekaru kusan 8,500 yayin da ake tono shi a Jihar Yobe, Arewacin Najeriya, a shekarar 1987.
An gano wannan jirgin ruwa ne daga hannun wani makiyayi Bafillace yayin da yake haƙa rijiya kusa da ƙauyen Dufuna, a cikin Jihar Yobe State ta yanzu.
An sassaka jirgin ruwan daga gindin itace guda ɗaya na African mahogany, kuma wata ƙungiyar masu binciken tarihi ta Najeriya da Jamus ce ta tono shi daga ƙasa.
Binciken radiocarbon ya nuna cewa jirgin ruwan yana da shekaru kimanin 8,000 zuwa 8,500 (wato kusan 6000 K.Z.), wanda ya sa ya zama jirgin ruwa mafi tsufa da aka sani a Afirka, kuma na biyu mafi tsufa a duniya—bayan Pesse Canoe daga Netherlands, wanda aka kiyasta yana da shekaru kusan 10,000 (kimanin 8040 K.Z.).
A halin yanzu, an adana Dufuna Canoe a wani gidan adana kayan tarihi da ke Damaturu a Jihar Yobe.
09/03/2026
A LAHADI......
Ga halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya........
IRAN
Wani harin jirgi maras matuƙi na Iran yayi ajalin sojin Amurka 7 a Kuwait, tare da jikkata wasu da dama da lalata dukiya mai yawa ( Iran Military )
MALAYSIA
Firaministan Malaysia yace hare haren da Amerika da Isra'ila suke kaiwa Iran, take hakkin dan Adam ne da kuma keta dokokin ƙasa. ( Irna News Agency )
IRAN/KUWAIT
Iran ta kai wani mummunan harin jirgi maras matuƙi zuwa ginin social building dake Kuwait, da kuma na'urar kare harin sama a sansanin Al'salam na Amurka dake Kuwait ɗin. ( Iran English )
SOUTH KORE/SPAIN
Dandazon masu zanga zanga a biranen Seoul da Malaga a ƙasashen sun fito kan tituna suna nuna adawa ga Amurka da Isra'ila, suna dauke da kwaleyen da aka rubuta Iran tana da ikon kare kanta. ( Irna News Agency )
US/ISRAEL
Sun kaddamar da hari kan wata matatar mai a birnin Tehran na Iran, abinda ya haddasa malalar man fetur a kan tituna tare da tashin gobara. ( Al'Arabiyya News )
IRAN
Ana hasashen ƙasar Iran ta zaɓi sabon shugaban addini a hukumance sai dai har yanzu bata bayyana sunan sa ba. ( Gulf News )
AMURKA
Trump yace yanada hujjar tura dakarun ƙasa zuwa Iran domin cimma burin sa na hamɓarar da gwamnatin kasar. ( Donal Trump )
US/BRITISH
Trump yace Ingila ta bashi kunya akan matsayar data ɗauka a yaƙin Iran, bayan da Birtaniya tace dole ne ayi taka tsantsan domin gudun keta dokar ƙasa. "amma masu sharhi na ganin Ingila tana gudun asarar ne bayan da Iran ta kaddamar da hari akan sansanin sojojin ta dake Cyprus" ( Pentagon News )
UAE
Daular Larabawa tace Amurka ta kakkaɓo mizayil 16 na Iran data harba Abu Dabi ( Gulf News )
IRAN
Ta sake kai harin mizayil sansanin sojin saman Amurka a Bahrain, ana fargabar mutuwar gomman sojoji da jikkata wasu da dama ( TRT Word )
Idriss M Idriss Damaturu Ɗan jarida ✍️
09/03/2026
UPDATE
A Yau Litinin Ga Abinda Aka Wayi Gari A Yaƙin .......
NIGERIA-IRAN
Iran tace a shirye take ta tallafawa Nigeria wajen yaƙi da ƴan ta'adda mutum ƙasar ta buƙaci haka. " Sai dai a yanzu haka akwai sojojin Amurka a Nigerian da s**a shugo domin taimakawa kasar yaƙi da yan ta'adda" ( DW )
IRAN
Dandazon al'umma a birane daban daban na Iran sun fito kan tituna don murna da nuna goyon bayan su bayan ayyana Mujtaba Khamene'i a matsayin sabon jagoran addinin ƙasar ( Irna News Agency )
IRAN
Ta kaddamar da wani kazamin hari kan cibiyar makamashi a Bahrain abinda ya lalata dukiya mai yawa, adai dai lokacin da farashin man fetur keci gaba da tashi a sassan Duniya. ( Al'Arabiyya English )
ABU DABI
Mutum biyu sun mutu a daular larabawa bayan da ƙasar ta kakkaɓo mizayil na Iran a kusa da wani sansanin sojin Amurka. ( Al'Arabiyya English )
IRAN/ISRAEL
Wani mummunan harin roka na Iran ya faɗa tsakiyar birnin Tel'aviv na Isra'ila abinda ake fargabar yayi mummunan asara ga mazauna gidaje, "sai dai duniya na nuna damuwa kan keta dokokin yaƙi na Duniya kan fararen hula" ( Daily Iran Military )
CHINA
Beijing tace tana taya Mojtaba khamene'i murnar zama sabon shugaban addinin Iran kuma lallai Tehran tayi kyakkyawan zaɓi. ( China Army )
IRAN
Ta sake jaddada matsayinta na cewa bata da niyyar kaddamar da hare hare akan Turkiyya da Azrabijan da Cyprus, saboda haka ƙasashen su kwantar da hankalin su. ( Al'Arabiyya News )
AMURKA
A ƙalla sojojin Amurka 600 ake fargabar an kashe tun bayan fara yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila amma Washington tace wannan labari shaci faɗi ne. ( Gulf News )
IRAN
Ministan harkokin wajen Iran yace zasuci gaba da yaƙi iya ƙarfin su, amma Duniya ta shirya sayan gangar man fetur a akan dala $200. ( Iran English )
Idriss M Idriss Damaturu Ɗan Jarida ✍️
04/07/2025
Memories♥️📌
01/12/2024
Memories✅🙏
01/10/2024
2nd
25/05/2024
24/05/2024
Memory 💥
10/04/2024
Alhamdulillah🙏
For another memories👌
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Address
Kanawa, Kirfi
Bauchi