Bauchi Daily Post

Bauchi Daily Post

Share

Jarida ce da za ta riƙa kawo muku labaran jihar Bauchi da kewaye daga 5STARS MEDIA PRODUCTION.

12/09/2026

Allah ya yi wa fitaccen attajirin nan na Nijeriya kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP Alhaji Bamanga Tukur rasuwa yana da shekaru 90.

Iyalen marigayin sun shaida wa TRT Afirka cewa ya rasu ne ranar Asabar a gidansa da ke Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Ana sa ran za a yi jana'izarsa a ranar Asabar din nan a Fadar Lamidon Adamawa, da ke Jihar Adamawa. Marigayin ɗan kasuwar, ya rasu ya bar 'ya'ya 17.

Marigayin ya yi gwmanan tsohuwar Jihar Gongola (Adamawa da Taraba a yanzu) a zamanin Jamhuriyya ta Biyu.

Bamanga Tukur ya yi ministan masana'antu a lokacin gwamnatin Sani Abacha, sannan ya taɓa neman tsayawa takarar shugabancin Nijeriya.

12/09/2026

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Tsohon Gwamnan Gongola (Adamawa/Taraba), Kuma Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Na Ƙasa, Bamanga Tukur ya rasu.

Allah Ya gafarta masa.

12/09/2026

ZAƁEN GWAJI – BAUCHI STATE 2027

🟢 APM — Yakubu Adamu PhD
🔵 APC — M.A
🔴 PRP — S. BUBA
🟠 ADC — DOKAJI
🔵 PDP — SUPI
⚫ NDC — KASHIM

Photos from Dass TBalewa Bogoro TV's post 12/09/2026
12/09/2026
Photos from Bauchi Daily Post's post 25/12/2025

RABON KAYAN KIRSIMETI :
Uwargidan Gwamnan jahar Bauchi Dr. Aisha Bala Mohammed ta Sanya farinciki wa al'umman kiristoci a jihar Bauchi a yayin bikin kirsimeti.

Uwargidan gwanmnan Tayi rabon kayan abinci wa yan uwa ma abota addinin kirista don ganin cewa kiristoci a jihar sunyi bikin na bana cikin farin cikin.

Photos from Bauchi Daily Post's post 20/10/2025

Yanzu-yanzu

Mashigar Abuja daga Nyanya ta cushe, matafiya da ma’aikata sun maƙale cikin cunkoson ababen hawa a yanzu haka sakamakon tsaurara matakan tsaro da gwamnati ta yi kan zanga-zangar da ake yi na neman sakin jagoran ƴan neman kafa ƙasar Biyafara Nnamdi Kanu.

19/10/2025

DA DUMI-DUMI: Shahararren Mawakin Gargajiya Na Bauchi, John Zuya, Ya Mûtû

An bayyana mutuwar fitaccen mawakin gargajiya kuma mai barkwanci daga garin Tafawa Balewa, jihar Bauchi, John Zuya, wanda aka fi sani da John Mai Molo, bayan da ake zargin an sa masa guba.

Rahotanni sun nuna cewa John Zuya, wanda kwanan nan ya dawo daga jihar Lagos inda ya je yin sana’arsa ta waka, ya rasu da safiyar jiya bayan da wasu da ake zargin abokansa ne s**a kai shi gidan cin abinci, s**a sanya masa guba mai karfi ba tare da ya sani ba.

Shaidu sun bayyana cewa mamacin ya fara nuna alamun ciwo mai tsanani kafin daga bisani ya riga mu gidan gaskiya. An kai gawarsa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, domin gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwarsa da kuma wadanda ke da hannu a lamarin.

Marigayi John Zuya ya kasance mutum ne mai fara’a, barkwanci da baiwa ta musamman a fagen waka. Ya shahara a yankin Bauchi da sauran sassan ƙasa saboda irin wakokinsa na gargajiya da nishadantarwa.

19/10/2025

Ina yan Bauchi, kun ganesu kuwa?

Want your business to be the top-listed Media Company in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Ahmadu Bello Way
Bauchi
740102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bauchi Daily Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Bauchi.