Zazzau Da Kewaye
Wannan page mun kirkireshi domin wayar dakan Jama'a dangane da Iliminsu, Lafiyarsu da addininsu, dakuma Tarihinsu.
12/04/2026
Makarantar Barewa College Zaria ta samar da:
1. Shugaban ƙasa har guda 6
2. Gwamnonin jihohi 27
3. Ministoci 69
4. Jekadun ƙasashen waje 42
5. Farfesa 72
6. Gwamnonin babban banki 3
7. Sarkin Musulmi 3
8. Janar na rundunar sojoji, yan kasuwa, attajirai, da masu mulkin da basuda adadi.
11/04/2026
Hoton Tarihi
Marigayi Sarkin Zazzau Alh. Muhammadu Aminu tare da Wakilin Tarihin Zazzau Alh. Shehu Ahmad Ahmed. Allah yajiƙan Sarki Aminu shi kuma Wakili Allah yaƙara masa Lafiya.
10/04/2026
Marigayi Dr. Rilwanu Lukman:
Babban masanin tattalin arziki da man fetur wanda ya kafa tarihin da ba za'a taba mantawa dashi ba a Najeriya da ma duniya baki daya.
An haife shi a ranar 26 ga watan Agusta, 1938 a birnin Zariya dake Jihar Kadunan Najeriya.
Ya fito daga gidan mutunci da ilimi a masarautar Zazzau.
Dr. Rilwanu Lukman ya kasance babban kwararren Engineer wanda yayi karatu a manyan makarantun duniya:
*Bayan kammala karatun firamare ya wuce zuwa Kwalejin Gwamnati ta Zariya wato Barewa College Inda yayi karatun sakandare.
A Kwalejin Fasaha ta Zariya (yanzu ABU Zaria): Ya fara karatunsa na gaba da sakandare.
*Sannan ya wuce Imperial College London, Inda ya sami digirinsa na farko a fannin hakar ma'adanai (Mining Engineering).
*Daga nan ya wuce University of Mining and Metallurgy (Austria), Yayi karatu a fannin hakar ma’adanai.
*Sannan ya wuce McGill University (Canada), inda ya kara samun horo na musamman a fannin sarrafa ma'adanai.
*Sannan sai Digirin Digirgir (PhD):* Inda ya sami lambobin girma na digirin digirgir (Doctorate) daga jami'o'i daban-daban saboda kwazonsa.
Ya rike manyan mukamai wadanda kadan ne 'yan Najeriya s**a taba rikewa ya fara rike:
Ministan Ma'adanai da Lantarki a shekarar (1984–1985).
Ministan Man Fetur, Ya rike wannan mukamin sau biyu (1986–1989 da kuma 2008–2010).
Ministan Harkokin Waje daga shekarar (1989–1990).
Sannan ya zama Sakatare Janar na Kungiyar OPEC ta duniya, Shine dan Najeriya na farko kuma daya daga cikin mutanen da s**a fi dadewa suna jan ragamar kungiyar kasashen dake fitar da man fetur (OPEC) a duniya tsakanin 1994 zuwa 2000.
Ya taba zama mashawarci na musamman kan harkokan man fetur ga Shugaba Olusegun Obasanjo.
😭😭😭😭
Rasuwa.
Dr. Rilwanu Lukman ya riga mu gidan gaskiya a ranar *21 ga watan Yuli, 2014, Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya bayan gajeriyar jinya a birnin Vienna na kasar Austria, inda yake zaune lokaci zuwa lokaci saboda ayyukansa na kasa da kasa.
04/04/2026
JAN-KUNNI JAN-KUNNI JAN-KUNNI
mahukunta wannan shafi mai albarka suna kira da babban murya zuwa ga ɓata garin da suke buɗe shafuka a kafofin sada zumunta da sunan Wannan shafi domin yaudara, Cuta da ha'intar Jama'a, wannan ba daidai bane. Muna kira su daina kuma su goge shafin, idan kuma sunƙi to lallai zamu ɗauki matakin hukuma kamar yadda Shari'a ta tsara.
mungode
Sanarwa: daga mahukunta wannan shafi
03/04/2026
WASU DAGA CIKIN ZURI'AR HAUSAWA
1. Adarawa
2. Katsinawa
3. Kanawa
4. Agalawa
5. Gobirawa
6. Birmawa
7. Abagayawa
8. Zazzagawa
9. Kurfayawa
10. Auyokawa
11. Guddurawa
12. Rafewa
13. Damagaramawa
14. Hadejawa
15. Ranawa
16. Daurawa
17. Garewa
18. Kabawa
19. Gwandarawa
20. Zamfarawa
Daga ciki wacce zuri'a ka fito?
Daga Fadar Zazzau wajen naɗin sarauta
15/03/2026
Ayau 26 ga watan Ramadan 1447AH wanda yayi daidai da 15 ga watan March 2026 Marigayi Yallabai Sanusi Gambo Alu Ɗan Sidi yake cika kwana arba'in da rasuwa, ana barar addu'a ga yan uwa musulmi dafatan Allah ya jaddada rahama agareshi Amin
01/03/2026
Farashin Kayan Gona A Kasuwar Giwa Ta Jihar Kaduna A Yau Lahadi; 01/03/2026
Masara Jaa 29/30k
Masara Fara 27/28k
Dawa 28k
Waken Soya 60/62k
Farin Wake Zapa 75/78
Farin Wake Sabo Misra 80k
Shinkafa (Mai Bawo) 37/38k
Gero 40k
Dauro 45k
Allah Ubangiji Ya H**e Ma Kowa Abun Siya. Amin
17/02/2026
Da ɗumi-Ɗumi: Anga watan azumin Ramadan na shekarar 1447 a Najeriya.
Fadar Sarkin Musulmi dakuma Fadar Shehun Borno sun sanar da Gobe Laraba a matsayin ɗaya ga watan Ramadan.
Allah yasa mu fara a sa'a Amin.
12/02/2026
Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Rajiuun
Babban Jikan Sarkin Zazzau Alu Ɗan Sidi Ya rasu 😭, bayan kwana tara da rasuwar ƙaninsa Yallabai Sanusi Gambo Alu Ɗan Sidi mai shekaru 96 a duniya.
Za'ayi Jana'izar a Fadan Mai Martaba Sarkin Zazzau da misalin karfe 5:00 na yamma.
Muna rokon Allah ya jikansa yasa ya huta.
03/02/2026
Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Rajiuun
Allah yayima Babban Masanin Tarihin Gidajen Sarautar Zazzau Kuma Mahaifin Ɗaya daga Cikin Shugabannin wannan Shafi Rasuwa Wato Yallabai Sanusi Gambo Alu Ɗan Sidi. mutumin kirki Baya goya Marayu.
Muna roƙon Allah yayi masa Rahama
02/02/2026
Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Rajiuun
Shaikh Usman Kusfa Rigi-Rigi Zaria ya rasu bayan Fama da Jinya a Asibitin Sojoji na 44 dake Kaduna. Za'ayi Jana'izarsa da ƙarfe 4:30 na yamma a Filin Low-cost dake daura da Kusfa Zaria, Muna roƙon Allah yajiƙan malam yayi masa Rahama Amin.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Address
Kofar Fada
Zaria