Shaheed Qasim Memory
Shaheed Qasim
10/08/2026
Sanarwa!!
Muna gayyatar yan'uwa da Abokan Arziki zuwa wajen zanen sunan Jikar Shahid Qasim wadda Allah ya azurta su ta hanyar ɗanshi M. Muhammad Qasim.
05/08/2026
Allah ya azurta Shahid Qasim samun ƙaruwar Jika ta Mace, ta wurin ɗan sa Mallam Muhammad Qasim. Muna roqon Allah T ya raya ta rayuwa mai kyau. Mu baran addu'arku.
05/08/2026
Ƙarin hotuna daga maukibin Shahid Qasim da ya gudana a tattakin Arba'een na bana a yankin Funtua
03/08/2026
MAUKIBIN SHAHEED QASIM SOKOTO.
An ciyar da masu tattakin Imam Husaini (a.s) a Maukibin Shahid Qasim Sokoto. Maukibin ya ciyar da masu tattakin Arba'in mutum dubu. Tun da safe, maukibin ya samar da shayi ga masu tattakin. Daga bisani, bayan an samar da zangon ƙarshe na masu tattakin, maukibin ya ciyar da mutum dubu.
Fatanmu shi ne Allah Ya karɓa, Ya kai ladan wannan ciyarwa ga Shahid Qasim Sokoto.
,Iraq
02/08/2026
Tattakin Yaumul Arba'een.
.
31/07/2026
وَعَلَىٰ أَصْحَابِ ٱلْحُسَيْنِ
25/07/2026
25th July💔
09/07/2026
Update
Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya sauka birnin Mashhad, Jamhuriyar Musulunci ta Iran, don halartar jana'izar Al-Shaheed Imam Khamene'i (QS).
Daga Najaf Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya biyo ayarin da s**a dauko Imam Al-Shaheed (QS) da za'a bizne a Haramin Imam Reza (AS).
09/07/2026
27/06/2026
Muminai suna buƙatar nagartaccen Malami wanda zai kusantar da zukatansu ga juna, ba wanda zai rarraba su ko ya haifar da gaba a tsakaninsu ba. Suna buƙatar wanda harshensa ba ya gina ƙiyayya a zukatan wasu a kan wasu; wanda manufarsa ita ce gaskiya, ba son zuciya ko bin mutane ba; wanda burinsa shi ne neman yardar Allah, ba neman wani abin duniya ba.
Rashin irin wannan mutum babban gibi ne a cikin al'umma Mumina. Wannan ne ya sa kullum muke jin kewar Babban Uba, Shaheed Sheikh Qasim (R), a tsakiyarmu. Ya tsaya wa Allah da cikakkiyar niyya, sai Allah Ya ɗaukaka ambatonsa, Ya ba shi ɗaukaka a duniya da lahira.
_Mahdi Dahiru Sanda
https://t.me/Mahdisanda
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Website
Address
Sokoto
62668835