RADIO IDI
Radio Idi, shiri ne don matasa domin su Isar da muryarsu ga Duniya. Radio Domin Matasan mu na Zamani Mussaman mabiya Shafukan Sada Zumunta na Internet.
15/10/2021
+238023625113
01/10/2021
JIYA BA YAU BA ...
Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, tare da Marigayi Firaminista Abubakar Takawa Ɓalewa, suna zagayawa a titunan garin Kaduna a shekarar 1959.
01/10/2021
Happy independence, Nigeria @61,
Matsalar gaba....
Daga bakin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (Rahimahullah).
Ayi sauraro lafiya, kuma in har an ƙaru, a yaɗa ko zamu faɗakar da juma.
31/08/2021
ALLAH MAI IKO...
Wata yarinya 'yar shekara 20 ta haifi jariri mai suffar tsoho ɗan shekara 80....Ita wannan Yarinya 'yar shekara 20 da har yanzu ba a bayyana sunanta ba ta haifi jariri mai suffar tsoho ɗan shekara 80 da haihuwa.
A cewar rahoton, yarinyar, wacce ke Afirka ta Kudu ta haifi wannan jariri wanda a ido kai kace kakanta ne, ko kuma mahaifita.
Labarin wanda ya kasance tare da hotunan mahaifiyar da jaririn ya haifar da cece -kuce da yawa a yanar gizo inda da yawa ke yiwa yarinyar fatan alheri yayin da wasu ke yi mata jan kunne da cewa anya wannan Mutum ne kuwa?
(c)browngh.com
Saƙo mai muhimmanci daga bakin Sheikh Muhammad Nuru Khalid zuwa ga Shugaban kasar Najeriya.
26/08/2021
26 ga watan Agusta.
Wacce karin magana kuke da ita a yau ta .
08/08/2021
Shugaban Ƙaramar hukumar Amuwo Odofin a jahar Legas yayi alƙawarin naɗin muƙamai ga Al'ummar Arewa, a lokacin da s**a ziyarce shi.
Ƙungiyar Arewa Community Ta Gaskiya Association dake yankin ƙaramar hukumar Amuwo Odofin a jahar Legas, ta taya shugaban karamar hukumar Amuwo Odofin, Dr Valentine Oluwaseyu Buraimoh murnar sake zaben sa. A lokacin da s**a ziyarci Shugaban, kungiyar ta gabatar da Sabo kuma Zaɓaɓɓeɓen Sarkin Hausawa na Festac H.R.H Alh. Mustapha Musa ll (Uban Tafiya), wanda kuma shine shugaban kungiyar Arewa Community Ta gaskiya Association ƙaramar hukumar Amuwo Odofin, ga Dr Buraimoh .
Da yake jawabi, Sarkin Yakin Festac, Dakta Isa Jimeta ya ba da tabbacin cikakken biyayya ga al’ummar Arewa a karamar hukumar Amuwo Odofin, ga sabuwar gwamnatin Dr Buraimoh. Da yake ba da gudummawa, Sabon Sarkin Hausawa na Festac, H.R.H Alh Mustapha Musa ll (Uban Tafiya) ya sake tabbatar wa Shugaban cewa membobinsa za su tallafa wa Gwamnatinsa ta hanyar ba shi cikakken haɗin kai. Sarkin Hausawa ya shaidawa Shugaban cewa mutanen sa za su kasance masu bin doka da oda.
A nashi jawabin Shugaban Ƙaramar hukumar ya shaidawa
membobin kungiyar Arewa Community don nuna goyon bayan su ga All Progressive Congress, APC, da kuma addu'o'i da s**ayi a zabukan da aka gudanar kwanan nan a jihar. Shugaban ya yi alƙawarin tallafa wa membobin Ƙungiyar Arewa kuma ya tabbatar musu cewa zai naɗa ɗaya daga cikinsu don ya kasance cikin Gwamnatin sa. Dangane da rushe kasuwar (2nd gate) da aka fi sani da kasuwar Agboju, shugaban ya yi alƙawarin dubawa da kuma yin wani abu game da rushe wannan kasuwar ga membobin Arewa Community, waɗanda abin ya shafa .
06/08/2021
Wai ina aka kwana da labarin wakar Dubu Ɗaya ta masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari?
06/08/2021
"Yaɗa hotunan da bidiyoyinta da Ire-iren hotunan laifi ne"
"Ɗiyar Sarkin bata fi ƙarfin doka ba, kuma ya kamata ace ta nuna ita ƴar gidan manya ce idan tana neman al'barka a aurenta."
A faɗar Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Lagos
Opening Hours
| Monday | 10:00 - 17:00 |