Blueprint Hausa

Blueprint Hausa

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Blueprint Hausa, Media/News Company, Katsina.

Blueprint Hausa jarida ce mai kawo ingantattun labarai cikin harshen Hausa domin ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa daga gida Nijeriya da ƙasashen waje don sanin halin da duniya take ciki.

Photos from Blueprint Hausa's post 19/04/2026

Gudunmawar Pantami wajen Sabunta Hanyar Gombe–Kumo–Billiri–Kaltungo zuwa Cham–Numan (Yola)

A ranar 26/08/2022, an ƙaddamar da muhimmin aikin hanyar Gwamnatin Tarayya a garin Gombe wacce ta haɗa Gombe–Kumo–Billiri–Kaltungo zuwa Cham–Numan (Yola), a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, GCFR, wanda Professor Isa Ali Pantami ya wakilta. Wannan nasara ta biyo bayan ƙoƙari da jajircewarsa wajen bibiyar matsalolin hanyoyin Gombe, musamman hanyar Cham zuwa Numan, wadda ta daɗe tana tafiyar hawainiya tun bayan bayar da aikin a shekarar 2017.

Ta hanyar tuntuba da Ministocin Ayyuka tare da gabatar da hujjoji kan matsalolin fasaha da s**a haɗa da Black Cotton Soil da buƙatar sake gina gada, an samu amincewar ƙarin kuɗi sama da Naira biliyan 7.6 domin tabbatar da ingantaccen kammala aikin.

Titin ya haɗa muhimman yankuna da s**a haɗa da Gombe, Kumo, Billiri da Kaltungo, tare da ƙarfafa alaƙa tsakanin jihohin Gombe, Adamawa da Taraba. Wannan haɗin kai ya sauƙaƙa zirga-zirga, ya bunƙasa kasuwanci, tare da inganta rayuwar al’umma, musamman manoma da ‘yan kasuwa da ke anfani da hanyar a kullum. Hanyar na daga cikin muhimman ayyukan more rayuwa da ke ƙara tabbatar da tasirin wakilci da himmar Pantami wajen jawo ayyukan ci gaba zuwa jiharsa.

Maigirma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, da Lamido Akko na daga cikin manyan baƙi da s**a halarci bikin ƙaddamarwar. Kasancewar su ya nuna muhimmancin aikin da kuma yadda haɗin gwiwar gwamnati ke samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’umma. Wannan aiki ya zama shaida a fili cewa nagartaccen wakilci da hangen nesa na iya haifar da ainihin sauyi a rayuwar jama’a.

Akwai wasiƙar da tsohon Ministan Sadarwa, Prof. Isa Ali Pantami, ya rubutawa Ministan Ayyuka na wancan lokaci, Raji Fashola (SAN), a ranar 16 ga Satumba, 2019, kan buƙatar ƙarin tallafi domin kammala wannan muhimmin aikin hanya a yankin Arewa maso Gabas. Za a kawo cikakken bayani kan wannan wasiƙa nan ba da jimawa ba, in sha Allah.

26/02/2026

Da Ɗumi-Ɗumi:- Dole Ne Nasiru Elrufa'i Ya Fuskanci Hukunci - Inji Kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya

Ƙungiyoyin fararen hula daga Arewacin Najeriya da kuma kudancin kasar nan sun jaddada kiran cewa dole Elrufa'i ya fuskanci dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, babu wani tsohon shugaba da yafi karfin doka ko waye shi.

Abubuwan daya aikata lokacin da yake kan karagar mulki tun daga kwace kadarorin al'umma, take hakkin dan'adam, k**a mutane ba gaira ba dalili, ya zama dole yanzu ya fuskanci hukuncin abinda ya aikata.

Daga Nura Jamilu
Shugaban masu rajin kare demokradiyya na Kaduna

18/02/2026

Dole Elrufa'i Ya Rufewa Mutane Baki Ya Fuskanci Tuhume-tuhumen Da Ake Masa ~ Inji Kungiyar DWI

Kungiyar Democracy Watch Initiative (DWI) ta yi kira dangane da binciken da ake yi wa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. A halin yanzu yana fuskantar bincike daga hukumomin yaki da cin hanci da kuma hukumomin tsaro da dama, ciki har da Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) da Department of State Services (DSS). Kungiyar ta ce kokarinsa na karkatar da hankalin jama’a daga wadannan manyan zarge-zarge ba gaskiya ba ne, kuma hakan na iya zama barazana ga tsaron kasa.

El-Rufai ya amince cewa sun kutsa cikin hanyoyin sadarwa wayar National Security Adviser (NSA), abin da ya nuna rashin mutunta dokoki da tsarin tsaron kasa. DWI ta ce wannan ba siyasa ba ce kawai, illa keta doka da kuma cin amana da aka dora wa shugabanni.

A wani bayani da ya fitar, El-Rufai ya ce ya nemi karin haske daga NSA kan rahotannin shigo da sinadarin thallium sulphate mai matukar hadari. Duk da cewa gaskiya da rikon amana suna da muhimmanci, hanyar da ya bi ta jawo tambayoyi maimakon bayar da amsoshi. Maimakon ya maida hankali kan tuhumar da ake masa, sai ya nemi sauya labari domin ya nuna kansa a matsayin mai kishin kasa, alhali yana karkashin bincike.

DWI ta jaddada cewa babu wanda ya fi karfin doka, komai mukaminsa ko tsohon matsayinsa. Ta bukaci El-Rufai ya fuskanci doka domin tabbatar da adalci da kare tsaron kasa. Doka ita ce ginshikin dimokuradiyya, kuma dole ne kowa ya dauki alhakin ayyukansa.

Kungiyar ta kuma roki hukumomi su hanzarta bincike ba tare da tsangwama ba, tare da kare mutuncin cibiyoyin kasa. Ta gargadi jama’a da kada su bari siyasa ta dauke musu hankali daga manyan batutuwan tsaro da adalci.

A karshe, DWI ta sake jaddada bukatar a binciki dukkan matakan da El-Rufai ya dauka tare da tabbatar da ya amsa tambayoyi kan sak**akon ayyukansa. Ta ce sai an tabbatar da gaskiya da rikon amana ne kawai za a samu Najeriya mafi tsaro da dimokuradiyya ga kowa.

14/02/2026

Ba Ribadu Ne Matsalarka Ba: Gwamnatin Jihar Kaduna Ce Ta Kai Ka Gaban Hukuma Ka Tafi Ka Amsa Laifukan Da Ake Tuhumarka

Ya k**ata ka Fuskanci Zarge-Zargenka, Ka Daina Ɗorawa Wasu Laifi.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, dole ne ya daina yaudarar jama’a ta hanyar karkatar da akala daga ainihin batun da ake tuhumarsa da shi.

Zarge-zargen cin hanci da rashawa da almundahana da s**a taso daga mulkinsa ba ƙananan batutuwa ba ne da za a shafe su da siyasa ko surutai.

Abin da ya fi ba jama’a mamaki shi ne yadda yake ƙoƙarin janyo sunan Nuhu Ribadu cikin wannan rikici, alhali ba shi ne ya kai ƙarar ba. Gwamnatin Jihar Kaduna ce da kanta ta miƙa batun ga Independent Corrupt Practices Commission (ICPC) da kuma Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) domin a bincike shi.

Don haka duk wani yunƙuri na jefa wani cikin wannan batu wata dabara ce ta neman kawar da hankali daga gaskiya.
A lokacin mulkinsa a Kaduna State, an sha fama da zarge-zargen karkatar da kuɗaɗen jama’a, rushe gidaje ba tare da adalci ba, da yanke shawara ba tare da bin ƙa’ida ba.

Yanzu da aka buɗe bincike, abin da ya k**ata shi ne ya fito ya kare kansa a gaban doka, ba ya ɓoye a bayan siyasa ba.
Idan yana da gaskiya, kotu da hukumomin yaƙi da cin hanci za su tabbatar. Amma idan akwai laifi, dole ne ya fuskanci hukunci k**ar kowane ɗan ƙasa.

Bayan zarge-zargen cin hanci da rashawa, Elrufa'i ya kasance mutum mafi take hakkin mutane a lokacin da yake mukin jihar Kaduna, cikin waɗanda ya gallazawa har da su tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani.

Irin wannan mutanen ba su cancanci tausayawa agun talakawa ba ko kaɗan, Yak**ata su fuskanci hukunci mai tsauri akan abubuwan da s**a aikata.

Daga matashin Ɗan gwagwarmaya
Muhammad Nur Kaduna.

09/02/2026

Kogunan Gusa Shine Amsa A Jihar Zamfara 2027

A yau Jihar Zamfara na bukatar shugaba nagari, mai hangen nesa, mai tausayi ga talaka, kuma wanda ya san halin da al’umma ke ciki.

Ba kowa ba ne zai iya ɗaukar wannan nauyi, sai mutumin da Allah ya horewa baiwa da basira, kwarewa, da kuma kishin jama’a. Daga cikin irin wadannan mutane, sunan Kogunan Gusau ya fito fili ba tare da shakka ba.

Kogunan Gusau mutum ne da ya shahara wajen taimakon jama’a, gina al'umma, da tsayawa tsayin daka wajen kare muradun al’umma. Tarihinsa ya nuna cewa shi shugaba ne mai sauraron jama’a, wanda ke da fahimtar matsalolin tsaro, tattalin arziki, ilimi da walwalar al’umma. Ba wai kawai a iya magana ya tsaya ba, faɗa da aikatawa sunanshi.

A tsawon lokaci, Kogunan Gusau ya nuna jajircewa, hakuri da kwarewa a harkokin shugabanci da siyasa. Yana da fahimta mai zurfi game da jihar Zamfara daga karkara zuwa birane, kuma yana da zuciyar haɗa kan jama’a ba tare da nuna bambanci ba. Wannan shi ne irin shugabancin da Zamfara ke nema a wannan lokaci mai muhimmanci.

Muna kira gare ka, Kogunan Gusau, da ka amsa kiran al’umma. Ka tsaya ka fafata domin karɓar kujerar Gwamnan Jihar Zamfara a 2027 insha Allahu, domin mutane da dama sun yarda kai ne mutumin da ya dace da wannan aiki.

Zamfara na bukatar shugaba mai tsoron Allah, gaskiya, hangen nesa da kuma karfin gwiwar kawo sauyi, kuma wadannan siffofi suna tare da kai.

Allah Ya taimaka, Ya ba da nasara, kuma Ya sanya abin da ya fi alheri ga Jihar Zamfara da al’ummarta.

Muhammad Nura
Chairman Koguna Alheri Ne

Photos from Blueprint Hausa's post 01/02/2026

Ɗaruruwan matasa magoya bayan Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya kuma Wazirin Pantami) sun gudanar da taro a karamar hukumar Funakaye, jihar Gombe.

A yayin gudanar da taron an kara wayar da kan matasan kan abunda ya shafi harkar rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta da wayar da kansu.

Haka zalika matasan Funakaye sunyi kira tare da roko ga Professor Isa Ali Pantami da ya daure ya fito takarar Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.

Mutanen Funakaye sunyi dan-dazo Mazansu da matansu sun fito daga kowane yanki na fadin karamar hukumar, domin nuna soyayya da kaunarsu ga Majidadin Daular Usmaniyya.

Wannan yake kara nunawa da tabbatar da cewa mutanen jihar Gombe na kowane yanki a shirye suke domin bada gudummuwarsu na ganin Professor Isa Ali Pantami, ya zama Gwamnan jihar Gombe a zaben 2027.

Photos from Blueprint Hausa's post 16/01/2026

An Jaddada Yaƙi Da Shan Miyagun Ƙwayoyi Da Jagoranci Nagari A Babban Taron Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya "CNG" A Birnin Sakoto

Ƙungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) ɓangaren ɗalibai ta samu gagarumar nasara wajen shirya laccar bai ɗaya da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato.

An gudanar da laccar ne ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba HRH Farfesa Sambo Wali Junaid (Wazirin Sakkwato), inda manyan masu jawabi s**a yi jawabai masu armashi kan batutuwa masu muhimmanci da s**a shafi kyakkyawan jagoranci nagari, illolin shan miyagun kwayoyi, da kuma mummunan tasirin "Hate speech" a makarantun gaba da sakandare da ma al’umma baki ɗaya.

Taron ya samu halartar ɗalibai masu yawa daga fannoni daban-daban, abin da ke nuna yadda matasa ke da ƙwazo da sha’awar rungumar kyawawan ɗabi’u, haɗin kai da jagoranci nagari.

Hakika, laccar ta ilmantarwa ta kuma yi tasiri sosai, inda ta haɗa zukatan matasa masu burin gina kyakkyawar makoma mai ɗorewa da ci gaban al’umma.

07/01/2026

Masu Yada Karya Akan Gwamna Bauchi Bala Muhammad Ba za su yi nasara ba - Arewa Democratic Agenda

Muna jan hankalin jama’a game da wani labari na ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin cewa an bai wa wata ƙungiya da ake alaƙantawa da ta’addanci kuɗi daga Gwamnatin Jihar Bauchi. Wannan labari ba shi da tushe, b***e Malama, babu hujja, kuma ƙarya ce tsagwaronta.

Babu wani lokaci da Gwamnatin Jihar Bauchi, ko Mai Girma Gwamna Sanata Bala Mohammed, ya amince ko ya ba da umarnin bai wa kowace ƙungiya da ke da alaƙa da ta’addanci kuɗi, ko ta kowace hanya. Wannan zargi an ƙirƙire shi ne kawai domin ɓata suna, yaudarar jama’a, da tayar da fitina.

Haka kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da irin waɗannan labaran ƙarya, su kuma guji yaɗa bayanan da ba su tantance ba.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta himmatu wajen tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da bin doka da oda, tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro na ƙasa.

Duk wanda ke yaɗa wannan labari na ƙarya, yana da niyyar ɓata sunan shugabanci da ya samu amanar jama’a, kuma hakan ba zai hana gwamnati ci gaba da ayyukan alheri da ci gaban jihar Bauchi ba.

Gaskiya ce za ta yi nasara a kowane lokaci.

05/01/2026

Kungiyar Arewa Media Writers Ta Yi Kira Ga Shugaba Tinubu Da Ya Gaggauta Sauke Ministan Abuja, Nyesom Wike

…Kungiyar ta ce dole ne a dakatar da duk wani yunkuri da ke barazana ga dimokaradiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Daga Kungiyar “Arewa Media Writers”

Kungiyar Marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Comr. Haidar H. Hasheem (Kano), ta nuna matuƙar damuwa tare da yin Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin k**a-karya, nuna wariya da cin zarafin ‘yan ƙasa, da ake zargin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, na aikatawa.

Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda ake zargin Ministan da amfani da ƙarfin iko wajen cuzgunawa ‘yan Arewa da ‘yan adawa, musamman saboda banbancin ra’ayin siyasa, abin da hakan ke tauye ‘yancin ‘yan ƙasa tare da zama barazana ga tsarin dimokaradiyyar Najeriya.

A cewar ƙungiyar, ana zargin Wike da amfani da hukumar EFCC da jami’an tsaro wajen tsoratarwa da musgunawa abokan hamayya, lamarin da ke haifar da fargaba, rashin adalci da rashin amincewa ga hukumomin gwamnati.

Kungiyar Arewa Media Writers ta kuma nuna damuwa kan yadda Ministan ke yin furuci da ayyuka masu ɗauke da wariya ga al'ummar Hausawa/Fulani, inda ta jaddada zargin da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya yi a baya-bayan nan, wanda yace ya samu wata masaniya daga mai jiya mai tushe dake nuna cewa hatta hukumomin EFCC, Wike ke amfani da su wajen matsin lamba ga yan adawa, haka kuma ya tabbatar dasa hannun Ministan wajen ƙoƙarin bata masa suna ta hanyar jingina shi da zargin ɗaukar nauyin ta’addanci a kotu.

Kungiyar ta bayyana cewa irin waɗannan zarge-zarge ba komai ba ne illa kiyayya ta kabilanci da siyasar adawa, wanda hakan ya saba wa ruhin haɗin kan ƙasa. Idan baku manta ba tun a lokacin da Wike ke Gwamnan Jihar Rivers, an samu rahotannin rusa masallatai, rufe shaguna da gidajen ‘yan Arewa, tare da korar su daga jihar, abin da har yanzu ke ci wa zukatan al’umma tuwo a ƙwarya.

Haka kuma ƙungiyar ta yi tsokaci kan sauke Sakataren Ilimi na Abuja, Dr. Danlami, wanda ɗan Arewa ne, inda ta ce yadda aka yi hakan ya ƙara nuna amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba, tare da mayar da shi aiki bisa wasu sharudda.

Ba wannan kaɗai ba, kungiyar ta kuma nuna damuwa kan zargin amfani da jami’an tsaro wajen tarwatsa rikici a helkwatar jam’iyyar PDP, inda aka ce har aka yi amfani da hayaki mai sa hawaye ga wasu gwamnoni ciki har da Seyi Makinde da Bala Muhammad, lamarin da bai dace ba ga shugabanni da kundin tsarin mulki ya tanadar musu da rigar kariya.

Kungiyar Arewa Media Writers ta jaddada cewa tsarin shugabancin Najeriya bai ginu kan kabilanci, wariya ko ramuwar siyasa ba, illa adalci, daidaito da mutunta ‘yancin kowa.

A ƙarshe, Kungiyar Arewa Media Writers tana kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta dakatar da duk wani yunkuri da ke barazana ga dimokaradiyya Najeriya, taka wa Ministan Abuja burki, ko kuma a sauke shi daga mukaminsa, domin kare martabar dimokaradiyya, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Arewa Media Writers za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya, adalci da kare haƙƙin al’umma.

✍️✍️
Comr Nura Siniya
Chairman Arewa Media Writer's Katsina Chapter

02/01/2026

GWAMNAN JIHAR BAUCHI BALA MUHAMMAD YA FALLASA ASIRIN MINISTAN ABUJA NYESOM WIKE

Maigirma Gwamnan jihar mu na Bauchi Senator Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Daular Usmaniyyah) ya fallasa asiri na makircin da Ministan Abuja Nyesom Wike yake kulla masa da jihar Bauchi gaba daya

Maigirma Gwamna yayi wannan fallasa ne a cikin shirin Sunrise Daily na Channels TV dazu da safe, yace akwai wanda yake shirya min makirci, kuma na san shi, shine Ministan Abuja na yanzu Nyesom Wike, ya fada wa duniya cewa zai kunna wuta a jihata na Bauchi

Kauran Daular Usmaniyyah yaci gaba da cewa; na fahimci Wike ne yake bada umarni wa hukuma irin na EFCC wajen batani, yana bawa mutane cin hanci, yana sayar da filayen Abuja yana amfani dasu wajen cimma burinsa, ba sabon abu bane a gareni saboda na taba rike mukamin Ministan Abuja na shekaru 6 na san komai

Gwamnan Bauchi yaci gaba da cewa; yana da hujjoji daga majiyarsa na sirri dake EFCC wanda s**a tabbatar masa da cewa Wike ne yake tsara duk abinda yake faruwa da ‘yan adawar siyasa a Nigeria

Kaura yace tsohon Accountant General dinsa na jihar Bauchi yaci amanata, ni na kaishi Kotu da kaina domin a masa hukunci, daga bisani Kotu ta bada belinsa, to a yanzu Wike ne yake aiki dashi a Kotu wajen bada shaida na karya akan mukarrabaina da aka k**a

A matsayina na Gwamna wanda na rike manyan muk**ai tun daga Sanata har Minista, ina shugaban al'ummah ta ya zai kasance ina daukar nauyin ta'addanci, ana min wannan sharri ne saboda ina cikin manyan 'yan adawa

Zan bi duk matakan da s**a dace domin na kare kaina, na rubuta wa Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya takardan korafi, tare da sanar da hukumomin tsaro, kuma zan kai korafina zuwa ga hukumonin Majalisar dinkin duniya, inji Maigirma Gwamna

Sannan Gwamna Bala yace Shugaban Kasa Tinubu yana kewaye da 'yan daba, 'yan damfara wadanda suke son ha||akashi a siyasance irinsu Wike

Muna rokon Allah Ya kare jihar Bauchi daga wadanda suke neman jingina mana ta'addanci, Allah Ya sa mugun nufinsu ya kare a kansu da iyalansu kadai.

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Katsina