Ambo Rabbitary
A. Ambo
Rabbit Lover and Rabbit Farming mentor
29/03/2026
SHIN KANA BA MA ZOMAYENKA DUMAR RAFI?
Abu mai muhimmanci ne ka shanya ta sha iska kamin ka basu,
saboda gudun matsalolin kumburin ciki.
26/03/2026
A kullum idan Allah ya jarrabe ka da rashin Zomaye
sai ka tuna ni'imar da Allah ya yi maka dasu, ko dai sayarwa ko yankawa.
Sai ka yi dogaro
21/03/2026
MATAKAI DA ZAKA BI YAYIN DA ZOMANYAR KA TA HAIHU A ƘASA KUMA TAƘI KULA DA ƳAƳA.
1. Ka gaggauta kwashe su sannan ka samu roba, jarka da ka yanke samanta, tukunyar ƙasa, akwati ko wata container mai tsafta.
2. Ciyawa busasshiya: zaka saka a inda zaka musu sheƙar.
3. Ka samu auduga (Cotton wool): Ka saka a kan ciyawar don su samu laushi sosai.
4. Idan ka zuba ƴaƴan a kan audugar, sai ka samu auduga pale-pale marar nauyi ka saka a kan ƴaƴan don su samu ɗumi.
5. Bayan sun huta na awanni sai ka ɗauka uwar ka danne ta sannan ka ɗaura ƴaƴan a kanta su sha.
6. Idan kuma ta haihu a cikin wajen ne Amman batayi sheƙa ba, zaka iya yi mata sheƙar a inda ta haihu sai ka cire gashin ta ka haɗa da audugar sannan ka dinga dubawa ko ta shayar dasu.
Wannan abu ne mai sauƙi da zaka iya a matsayin ka na mai kiwo don ceto rayuwarsu.
Allah yasa albarka
Havana × New Zealand Breed
16/03/2026
Wannan cutar Mange ce, idan ka ganta a zomonka, ka bashi ɗauki na gaggawa sannan ka raba shi da ragowar.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano