Samaha SMCS

Samaha SMCS

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Samaha SMCS, Business service, Kano.

29/04/2024

MALAMI DA DALIBINSA: PROF SALISU SHEHU & ABDULLAHI LAMIDO

Jiya nai kasida don nsa kare sunna
Bisa kan Tamalmatu wacce anka yi karya

Mai shekarunta dubu bakwai don shirme
Na fatattake su na wargaza musu karya

Sai Malamina Shehu yai yi kasidu
Yai jinjina ya fito ya goyan baya

Ga nan abinda ya ce cikin wakenai
In ka karanta sai ka bi ni a baya

"Allahu Akbar Allah kara basira,
Lamido ka zama Sha'iri fa na gaskiya

Abdallah tabbas ka cira mana tuta,
A wajen ginin shi'ri fa sam tankiya.

Kullum ka kan shiryo kasida qayyima,
Don kare Islama tafarkin gaskiya."

Babban liman ya karfafa mini baya
Masani na Ku'ani da ma tarbiyya

Bayan da nag na abinda Shehu ya tsaro
Ni ga abinda na ce ina godiyya

"Duk ƙoƙarin da muke a harkar da'awa
Ai ku ku kai mana dukkanin tarbiyya

Kuka bamu horo don mu k**a karatu
Ilimi da ƙwazo duk a gunku na koya

Ɗa ba shi yin kirki ya yo albarka
Sai in iyaye sun yi mar tarbiyya

Ku kun ce ma tsaya bisa Tauhidi
Mu rike kitabu mu ƙyale hanyar ƙaarya

Kuka sa mu ƙyam mu riƙe tafarkin Sunna
Mu guje wa musu ko yawan jayayya

Duk duniya ta san fa ni Abdallah
Ai Shaihunai ne sun ka sa ni a hanya

Kuma ko ina ne zam faɗi ba shakka
Kuma za ni nanata da babbar murya

Cewa a gunku na samu duk horona
Na zubo rubutu har da yin ƙafiyya

Roƙon Ilahu nake ya kare min ku
Ya tsare mu ranar lahira jin kunya

Ya saka mu firdausinsa mu da Habibu
Mu haɗe mu taru a can cikin soyayya"

29/04/2024

GOMBE WATER SCARCITY: THE NEED FOR GOVERNMENT INTERVENTION

I wrote about the immense hardship people face due to water scarcity just a few days ago. While I know it's not unique to Gombe, it's the situation here that I witness firsthand. The water shortage in Gombe has undeniably reached a critical level, demanding emergency measures from the government.

I have full faith in His Excellency the Governor's well-known concern for the people's plight. I trust he is already formulating a bold plan, as is his nature, to squarely address this issue. Your Excellency, with all due respect, your people are truly suffering. We know you care deeply for them. Water is life, and it's simply unavailable to many. Urgent intervention is needed.

However, let's remember that the state government cannot shoulder this burden alone. We must complement their efforts. Anyone with the means to dig a borehole should do so without delay. Purchase and distribute pure water bags. Donate a generator to a community borehole project. Contribute fuel to allow communities to pump water from their boreholes. Share what little you have with your neighbors. One sachet of pure water may save a life. Never underestimate that. Water is life, after all.

Amir Abdullahi
Lamido

28/04/2024

ANGON TAMALMATU

Ƙissar Tamalmatu yau nake yiwa sharhi
Tatsuniyar gizo ce da ƙoƙi ya shirya

Angon Tamalmatu mai ta zo ta mu jita
Sheikh mai Tamalmatu shugaban 'yan ƙarya

Shi ba shi kunya yai fita ta limamai
Ya tara ɗifgaggu yana zuba ƙarya

In ka gane shi k**ar cikakken Shehi
Ya ɗaura ɗan rawani da jallabiyya

Sai shaƙe murya tai yake ya dage
Har dariya yake ba ya jin ko kunya

Ya shirya ƙarya ya zuba ta ga Ɗaha
Sai shirga labarai yake ba kunya

Ya ce Tamalmatu da daɗe nan dunya
Wai shekarunta dubu bakwai har ɗoriya

Da ɗari bakwai saba'in bakwai duka cif cif
Ƙara yininta guda bakwai nan dunya

Lamarudu har hamana har Fir'auna
Duk ta gane su da ma su Annabi Yahya

Wai tai karo da Rasulu Musa da Isa
Har ma da Manzannin daban daga baya

Tsoho kawai ya ɗauki shirmen banza
Ya karkace ya tuɓe rigar kunya

Kuma ma abun kunya abin ban haushi
Wai shi ya auri Tamalmatun daga baya .

Su ko na zaune labarbari s**a jerin
Sun bashi lasisi yana zuba ƙarya

Tsoho ya je ya shi ya tuba Kar ya yi letti
Don lahira can kar ya je sji kunya

Mannzonmu ya yi barazana mai ƙarfi
Ga wadannda za su fito suna masa ƙarya

Ya ce su tanadi shunfiɗarsu ta zafi
A cikin jahannama can ake musu suya

Tilas mu tashi mu kauda yan shirmen na
Mus haɗa su s**an

Ilimin hadisi wajibie lallai
Domin a tantance hadisan ƙarya

Mu yi maganin ɓarna kawai tun farko
Su mujamala mu aje mu dawo hanya

Allah tsare mu shiga ɓata har kullum
Mu zamo muna tafiya a tsarin shiriya .

Roƙon da nai maka Rabbana mai fenti
Allah tsare mu da son hadisan ƙarya

Abdallah Dan Lamido ne ya yi baitin
Domin kashade kar a bar mu a baya

26/04/2024

KU TAIMAKA WA JAMAA DA RUWAN SHA

Yanzu na je ofis dinmu na Zakka da Waqafi a Gombe. Sai na ga waɗansu yara suna fita daga da'irar gidan da bokitai, k**ar za su yi kuka saboda basu samu ruwa ba. Sai na bada umarni maza a sayi mai, a tada inji, a kuma bar ruwa a kunne sai bayin Allah sun wadata da ruwa. Kawai sai na tuna cewa fa shi wannan borehole ɗin wani bawan Allah ne ya tambaye mu me zai yi na waqafi sai na ce masa ya tona bohol. A take ya tura kuɗi a account ɗinmu. Yanzu haka duk anguwar fada da ma wassu anguwanni na maƙwabta a nan suke ɗiban ruwa. Haka kuma masu zuwa salla a babban masallacin Sarki. Ka kwatanta irin lada da bawan Allah ɗin nan yake kwasa.

Sai na tuna da hadisin Sahabi Sa'ad Ibn 'Ubbadah (RA). Bayan mahaifiyarsa ta rasu sai ya zo ya sami Annabi (SWA) ya ce masa, "Mahaifiyata ta rasu. Shin zan iya yi mata sadaqa"? Sai Annabi (SAW) ya ce masa "Eh". Sai ya ce masa "Wace sadaqa ce ta fi falala?" Sai Annabi (SAW) ya ce masa "Shayar da ruwa".
Daga nan sai Sayyiduna Sa'ad ya fara tona rijiyi a unguwanni. Duk inda ya ji masu buƙatar ruwa sai ya je ya tona rijiya, sai ya ce musu "Wannan rijiyar Mahaifiyar Sa'ad ce".

Kai ma ka nemi mabuƙatan ruwa. Ka tona rijiya ko bohol. Ko ku haɗa kuɗi tare da wassu ku tona rijiyar ko bohol. Ko aƙalla ka sayi ledar fiya wata ka bawa mabuƙata. Idan ka ga wata unguwa suna l da bohol amma babu injin tura ruwa, sayi ka bayar. Akwai bohol amma babu man inji, sayi ka bayar a samu wadata bayin Allah da ruwa. Mu shayar da ruwa ko Allah zai shayar da mu ruwan Alkausara.

Abdullahi Abubakar Lamido
Gidauniyar Zakka da Waqafi

25/04/2024

Land for Tree Planting

Many people dream of planting trees but lack the space. Their homes may be small, but their passion, willingness, and resources abound. Here's a strategy to bridge the gap: partnerships between landowners and those eager to contribute.

Become a Steward of the Earth:
1. Land Donation: Contribute a plot, a hectare, or even fertile land – every bit counts.
2. Joint Waqf: Pool resources with friends or family to purchase land for tree planting as waqf (Islamic endowment).
3. Waqf Fund Donation: Contribute to a dedicated fund used to buy land for our ongoing plantation project at Zakah and Waqf Foundation initiatives.

Remember, the rewards for your contribution extend far and wide:
1. Reward for Land Waqf: You receive ongoing blessings for donating land.
2. Reward for Initiating Action: You're rewarded for starting the tree-planting process.
3. Reward per Tree Planted: Every tree planted on the land brings you additional reward.
4. Reward for Inspiration: You're rewarded whenever someone replicates your initiative.
The chain of reward stretches far. Don't hesitate to invest in your hereafter.

Join the Tree Waqf Project:
Our target is 10,000 trees this year. N5000 can plant and nurture a tree for you. But you can donate any amount you can afford – N200, N1000, N2000, and so on. What truly matters is being part of this rewarding endeavor and reaping everlasting blessings, insha Allah.
Here are the account details:

Zakah and Waqf Foundation
Jaiz Bank
0015286420

Abdullahi Abubakar Lamido
Chairman, Zakah and Wawf Foundation
07037578248

21/04/2024

One person, one tree,every year.

One house, one tree

Abdullahi Lamido

20/04/2024

Me Ka Gabarta Wa Iyayenka na Samun Lada Mai Dorawa?

Bayan sun haife ka, iyaye su s**a rene ka s**a maka tarbiyya har ka girma. Amma meye ka yi musu na sadaƙatul jariya (waqafi) wanda zai amfane su bayan mutuwarsu? Kana iya musu abinda ake ƙira Waqful Walidaini, wato Waqafi domin Iyayenka biyu wanda zai ci gaba da aika musu lada cikin ƙabarinsu. Misali, ka/ki dasa bishiyoyin mangwaro biyu don Baba da Mama. Idan da hali, dasa musu bishiya 20 na kashu, ko guda 40 na dabino. Idan Itatuwan nan s**a haifar da 'yaya, ko s**a bada inuwa ko waninsu ya amfani bayin Allah, ko s**a bada mafaka ga suntsaye, to duk ladar na mahaifanka ne! Idan kai baka ƙware ba ko ba ka da filin yin dashe a gidanka, ko ba ka da lokacin lura da su, samu wassu amintattu su wakilce ka wajen dasawa. Kana iya ba da wakilci ga Gidauniya e Zakka da Waqafi. Za a iya saya itace a dasa a masa ban-ruwa a kula da shi har ya girma a Naira 5000 kacal, Insha Allah. Komai ƙanƙanta abinda ka bayar zai yi amfani daga Naira 100 har zuwa miliyan. Allah ya bamu iko, kuma ya jikan iyayenmu ya musu rahama.

Abdullahi Abubakar Lamido, Shugaban Gidauniya Zakka da Waqafi (07037578248)
Ga account don sanya abinda ya sauwaƙa
Zakah and Waqf Foundation
Jaiz Bank
0015286420

18/04/2024

A Tree for Your Parents!
They gave birth to you. They raised you. They nurtured you. They educated you. You are now grown up. What have you done for them that perpetual generates reward for them? A practical everyone can do is to make for them what is called waqf al-walidayn; an endowment in honour of parents intended to provide ongoing source of rewards for them. They generate pertual rewards from the welfare activities financed from the income of the fruit bearing trees. So, think of 2 mango trees for dad and 2 for Mum. Plant 20 cashew trees or 40 date trees for each of them. They bear fruits, protect the environment, prevent desert encroachment, make the environment cool, provide "descent accommodation for birds, improve food security and beautify the environment. All the rewards go to Baba and Mama. If you don't have the skills, space and/or time to do it, get it done through reliable organizations. Zakah and Waqf Foundation can raise and nurture a tree for your parents at N5,000, Insha Allah.

Abdullahi Abubakar Lamido (07037578248)
Chairman Zakah and Waqf Foundation
Jaiz Bank
0015286420

18/04/23

14/04/2024

Mu Koma Gona

MATASA DA AGRICULTURE

Abdullahi Abubakar Lamido

Da sunan Rabbi wanda ya kagi nature
Ya aiko Annabawa da scripture
Ya baiwa duniya best architecture
A yau zan wake harkar agriculture

Cikin Enghausa ne zan tsara baiti
Gama Enghausa yaren na da beauty
Ana yi yau cikin kauye da city
Da Hausa da Ingilishi anka mixture

A yau a Arewa ko ta ina talauci
Da kidnapping da tsabar cin mutunci
A kullum rayuwarmu cikin takaici
Gaba daya al’umar sam babu future

Kudanci dogaronsu yana ga fetur
Arewa ko ga kasar nomarmu lebur
Mu dau noma mu daina batu na fetur
The new oil fa shi ne agriculture

A noma mun tsaya kyam a production
Gaba daya ba batun value addition
Muna noma kwai bisa wrong assumption
Cikin nomarmu dole mu canza culture

Matashi dan Musulmi za ka ganshi
Yana nan zaune ba aiki gabanshi
Kawai sai tsabaragen Ingilishi
Zugum ka ganshi ba Magana ta future

Matashi lafiyayye ga shi jobless
Ka gan shi kawai cikin komensa hopeless
Rashin aikinsa ya maisai speechless
Talaucin rayuwa ya ba shi torture

Matasa yanzu dole ku kara himma
Ku dau ilimi da kiwo ku riki noma
Ku bamu hatsi da shinkafa da nama
Cikin noma Arewa ta ke da future

Cikin noma ake samun abinci
Da shine ma ake korar talauci
A samu kudi a samu dadin mutunci
A kan haka sai mu rungumi agriculture

Da shi aka wa talauci alleviation
Da shi aka ba wa yara nutrition
Da shi ne maganin duka inflation
Na duke yana da big nomenclature

Cikin noma matasa na da aiki
Akwai access to 'ya'yan nan na banki
Akwai damammaki ninkin ba ninki
Idan kuka bar shi kun ga akwai fracture

Cikin noma da tarun employment
Akwai damammaki fiye ma da government
Idan burinmu shi ne fa development
Dukanmu kawai mu koma agriculture

Matasa dole ne mu yi calculation
Mu wa juna fada mu yi motivation
Mu dau noma da kiwo da education
Da su ne za mu zam mun samu future

Idan dai har muna son yin mutunci
Idan niyyarmu magance talauci
Da motsi don mu ba wa kanmu 'yanci
Ashe to wajibi ne canza culture

Zaman banza da shirme yanzu dole
Da wasanni da chatting duk mu kyale
Idan kuma mun ki ma sha gwale-gwale
Talauci zai zamo a gare mu nature

Today mun kwashi lakcar Dakta Tilde
Ta allura a kan aiki a ladde
Idan muka dau nasihun nan na Tilde
Fa tilas ne mu zam mun canza culture

Idan burinka shi ne employment
Idan ka so ka tashi ka fara movement
Idan da ba bu mai maka encouragement
A yau dai ga shi nan an baka lecture

Bayanai ga su an maka su laziza
Tunani yanzu na san za ya canza
Ka dage don ka ba wa kanka izza
From now sai ka koma agriculture

Amir Lamido nan ne za ni huta
Ina fata ilahu ya ban fahimta
Ya kara min tsayawa kan bajinta
Ya sa ni cikin wadanda suke da future

Amir Lamido
11/10/21

Amir

28/08/2017

Second batch of layya program was successfully delivered. Alhamdulillah

27/08/2017

Alhamdulillah.
Samaha successfully distributed the 1st batch of layya program, where interested members drive home happily with Ram/cow earlier applied.

02/02/2017

Samaha IIIBF BUK

Want your business to be the top-listed Business in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano
00234