Mua Express Sewing Machines Ent
Mu na sayar da kayayyaki kala-kala online
Ka biya kudi online, kayan ka su zo ,a kowane gari ka ke a
08/05/2026
MUA EXPRESS SEWING MACHINES 07017967787
IBB WAY KANO
29/04/2026
MAULANA SHEHU ABDULKADIR ZARIYA, MAHAIFIN SHEIKH SANI KHALIFA ZARIYA
A tarihi babu mutumin da ya yaɗa ilimin addinin musulunci a cikin kabilar Nufawa k**ar Shehu Abdulkadir Zariya
An haifi Shehu Abdulkadir Zaria a garin Agaie dake jihar Neja a shekarar 1909, shekaru dari da sha daya (111), ya taso a gidan karatu domin mahaifinsa malami ne mai karantarwa allo da ilimi.
Bayan ya girma Allah ya sa mishi son yin karatun ilimi mai zurfi, hakan ya tursasa mishi barin mahaifarsa, garin Agaie zuwa kasashen hausa dan neman ilimi mai zurfi.
Bayan ya zama teku a fannonin ilimin addinin musulunci k**a daga Fiqhu, Nahwu, Balaga, Sarfu, Lugga, Mandik, Qur'an da Hadisi(ruwaya da diraya), Tajwidi, Arud, da Tauhidi sai ya zo Zariya inda ya kara karatu kuma Allah ya nufe shi da zama a Zariya, inda ya kafa babbar jami'rsa ta ilimin addini a Anguwan Limancin Iya, dalibai daga fadin Najeriya da kasashen ketare s**ai ta tururuwar zuwa neman ilimi a wannan jami'ar ta sa.
Daga nan sai Shehu Abdulkadir Zariya ya koma garin Agaie inda yake zuwa lokaci lokaci. Yayi jihadi ya rabasu da wasu munanan al'adu na jahilci da suke aikatawa k**ar rashin kullen mata da rashin riko da addini da tsafi, ya kuma yada ilimin addini a cikin al'umar Nufawa, saboda Shehu ya shiga kauyuka da birane kwararo kwararo na Nufawa tsakanin Neja da Kwara da Kogi yana shiryar da su bin tafarkin shari'a madaidaiciya. A sanadiyyarsa dubannin nufawa sun zamo malamai, a yanzu dai zai yi wuya ka samu wani Malami banufe a yankin Neja da Kwara da Kogi wanda a karatunsa bai da alaqa da Shehu Abdulkadir Zaria. Ba iya nan ba Kusan a fadin Najeriya babu jihar da bai da almajirin da ya koyar ilimi.
Yana daya daga cikin malaman da s**a sallamawa maulana Shehu Ibrahim Inyass RTA. Shi ya kawo Shehu Ibrahim Inyass garin Zariya.
Bayan karfafa darikar tijjaniyya a yankin nufawa, shi ya kai faidar Shehu Ibrahim Inyass yankin wanda yanzu za'a iya samun nufawa sama da miliyan wadanda suke danganta kansu da faidar Shehu RTA. .
Ya wallafa littafai da dama a fannonin ilimi k**ar Fiqhu da Yabon manzon Allah saw da fannin Ilimin Alqur'ani da Sufanci d.s.
Ya bar duniya a shekarar 1980. Wadanda s**a gaje shi bayan wafatinsa daga cikin almajiransa akwai 'ya'yansa k**ar haka :
*Khalifa Sheikh Tijjani Abdulkadir Zaria
*Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria
*Sheikh Yusuf Sheikh Abdulkadir Zaria
Daga cikin almajirai akwai :
*Sheikh Idris Fogun Bida
*Sheikh M. Nasiru Sheikh Abdulkadir Zaria
*Sheikh Fadalu Gwargwaje
*Sheikh M.Magaji Banufe
*Sheikh M. Idi Kaura
*Sheikh M.Sani Dandume
Daga cikin almajiransa wadanda s**a yi fice a duniya akwai :
*Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda yayi karatun ma'arifa da azkarul tarbiyya a wajensa.
*Maulana Sheikh Abubakar Chiota RTA.
One Head Monogram Machine 12 Needle
25/04/2026
MUA BROTHER Es5 Embroidery Machine Monogram Designs
Available at MUA EXPRESS SEWING MACHINES IBB WAY KANO 07017967787
https://whatsapp.com/channel/0029VaF0q6B23n3YCnz9zI1p
LPG Gas iron Available Jaafar Jaafar Aminu Koki Muawiyya Aminu Koki Magaji Mega Ali Tela Abubakar Wada Kadi
1.25kg
3kg
4kg
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano Municipal
Kano
720001
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |
| Saturday | 09:00 - 17:00 |
| Sunday | 09:00 - 17:00 |