Alfidson Automotive Inventor
B.ENG AUTOMOTIVE ENGINEERING
NATIONAL PRESIDENT AUTOMOTIVE ENGINEERING STUDENTS
SMNSE|SMAUTOEI|SMNIPES|SMIAENG
13/09/2026
Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah.
All praise belongs to Allah Subhanahu wa Ta’ala for giving me life, good health, strength, wisdom, and the opportunity to complete this journey. What once felt like a distant dream has finally become reality.
To my parents, thank you for your prayers, sacrifices, and love. To my uncle, thank you for standing by me and supporting my education when I needed it most. May Allah reward you abundantly.
To my entire family, thank you for always being there for me.
To my lecturers, I sincerely appreciate your knowledge, guidance, corrections, and support. A special appreciation to my HOD, Engr. Prof. Abdullahi Ahmed, for your leadership and encouragement throughout this journey.
To my school and classmates, thank you for being part of this chapter. And to anyone I may have offended or disappointed along the way, I sincerely apologize and ask for your forgiveness.
To the entire AUTOEI family, whom I had the honour of serving as National President, thank you for your trust, support, and understanding. It was a privilege to serve and I will serve more.
And today, I cannot celebrate this achievement without remembering my late mother.
Mum, I wish you were here to see this day. Your absence is deeply felt, but your memory remains a part of me. I pray that Allah forgives you, has mercy on you, grants you eternal peace, and rewards you with Jannatul Firdausi. May Allah make this achievement a source of reward for you too. Ameen.
Today, I close one chapter with gratitude and open another with hope, humility, and determination.
Alhamdulillah. Automotive Engineering DONE.
ABDULHAKIM ALIYU HUSSAIN (ALFIDSON)
GMAUTOEI | GMNSE | MNIPES
NATIONAL PRESIDENT AUTOMOTIVE ENG
16/08/2026
Alhamdulillah! 🤲
Industrial visit ɗinmu na farko ya kasance cikakken darasi da kwarewa ta zahiri. A matsayina na ɗalibin Automotive Engineering kuma National President na ɗaliban, abin farin ciki ne ganin yadda muka samu damar fita daga cikin aji zuwa inda ake amfani da ilimin da muke koya a aikace.
Mun koyi abubuwa da dama daga practical skills, hanyoyin aiki, safety, har zuwa mu'amala da manyan ƙwararrun masana masu shekaru masu yawa na gogewa. Ba wai kawai mun ji bayani ba ne; mun gani, mun gwada, mun fahimta, kuma mun rayu da abin da muka koya.
Wannan shi ne ainihin manufar industrial visit: juya ilimin littafi zuwa ilimin aikace. 💯
Ina matuƙar godiya ga dukkan membobinmu da s**a samu damar shiga wannan tafiya. Kun nuna jajircewa, haɗin kai da kishin neman ilimi. Ina taya kowa murna da wannan sabon ilimi da kwarewar da muka samu. 🎓👏
Musamman, muna cike da godiya da ƙauna ga ƙwararrun facilitators ɗinmu da s**a ba mu lokacinsu, iliminsu da practical experience. Muna matuƙar godiya gare ku bisa yadda kuka koya mana cikin haƙuri, kulawa da sadaukarwa Allah Ya saka muku da alheri, Ya ƙara muku ilimi da albarka a rayuwarku.
Wannan ba ƙarshen tafiya ba ne farkon wasu manyan abubuwa ne da ke tafe, Insha Allah. 🚀
Alhamdulillah for a successful industrial visit.
More knowledge. More experience. More opportunities. More impact.
Alfidson Automotive Inventor
14/08/2026
🔥 ENGINEERS KUMA DOCTORS🔥
Akwai ɗan bambanci mai zurfi tsakanin Automotive Engineering da sauran rassan Engineering saboda Automotive Engineers suna da wani abu da ya yi k**a sosai da aikin likitoci.
Likita yana gano matsalar mara lafiya, mu kuma muna gano matsalar mota. Mota ba ta iya magana ta ce “ga inda nake jin ciwo,” amma ta hanyar sauti, vibration, warning lights da gwaje-gwaje, muna fahimtar abin da ke damunta.
Muna bincikarta, gyarata, gina ta, ƙirƙirarta da inganta rayuwarta.
Likita yana fahimtar abin da mutum ba zai iya faɗa ba; Automotive Engineer kuma yana fahimtar abin da mota ba za ta iya faɗa ba. ❤️🔧
Alfid Son
05/08/2026
FROM THE CLASSROOM TO THE INDUSTRY!
Alhamdulillah! On Monday, 10th August 2026, we will embark on our first-ever Industrial Visit with the final-year students of the Department of Automotive Engineering to the Aliko Dangote Modern Skill Acquisition Centre (ADUMSAK) widely recognized as one of the leading and most advanced skill acquisition centres in West Africa.
As the National President of the Automotive and Locomotive Engineers Institute (AUTOEI) National Student Forum, my mission is to bridge the gap between engineering students and the industry by creating opportunities for practical learning, innovation, and career growth.
This visit is more than a trip it's an investment in our future as engineers. We look forward to gaining hands-on experience, building industry connections, and opening doors to greater opportunities.
Keep us in your prayers for a successful and safe journey.
Alfid Son
Alfidson Automotive Inventor
Akwai haske with my Chinese person mr li-wei
27/07/2026
KURAKURAI 10 DA FASINJOJI KE YI A CIKIN MOTA BA TARE DA SUN SANI BA
Mutane da yawa suna tunanin direba ne kaɗai ke da alhakin tsaron mota. Amma gaskiyar ita ce, halayen fasinja ma na iya shafar tsaro da aikin mota.
1. Rashin saka seat belt.
Shi ne kuskuren da ya fi haɗari.
2. Buɗe ƙofa ba tare da dubawa ba.
Zai iya jawo haɗari ga masu babur, masu keke ko sauran motoci.
3. Katse hankalin direba.
Yawan surutu ko jan zance lokacin da direba ke buƙatar hankali yana da haɗari.
4. Fitar da hannu ko kai ta taga.
Wannan na iya jawo mummunan rauni.
5. Zama ba daidai ba.
Rashin zama yadda ya k**ata yana rage tasirin seat belt da airbag idan haɗari ya faru.
6. Ajiye kaya masu nauyi ba tare da tsari ba.
Lokacin haɗari, irin waɗannan kaya na iya zama haɗari ga fasinjoji.
7. Taɓa sitiyari ko gear lever ba tare da buƙata ba.
Wannan na iya katse ikon direba wajen sarrafa mota.
8. Rashin bin umarnin direba.
A lokacin gaggawa, haɗin kai tsakanin direba da fasinjoji yana da matuƙar muhimmanci.
9. Jefa shara ta taga.
Baya ga gurɓata muhalli, hakan na iya jawo haɗari ga sauran masu amfani da hanya.
10. Tsallake daga mota kafin ta tsaya gaba ɗaya.
Wannan kuskure ne da kan jawo raunuka masu tsanani.
Darasi
Tsaron mota ba aikin direba kaɗai ba ne. Fasinja mai hankali yana taimakawa wajen kare kansa, direba da sauran masu amfani da hanya.
Wanne daga cikin waɗannan kurakurai ka fi gani mutane suna yi a kullum?
26/07/2026
DUK WANDA YA FAHIMCI JIKIN ƊAN ADAM, ZAI FI SAURIN FAHIMTAR MOTA.
Mutane da yawa suna ganin jikin mutum da mota abubuwa ne guda biyu da ba su da alaƙa. Amma idan ka duba da idon Automotive Engineering, za ka ga cewa akwai k**anceceniya mai ban mamaki a tsakaninsu.
Kwakwalwa tana sarrafa jiki, k**ar yadda ECU (Engine Control Unit) ke sarrafa engine.
Zuciya tana tura jini zuwa dukkan sassan jiki, yayin da fuel pump ke tura mai zuwa engine.
Huhu yana samar wa jiki iskar oxygen, yayin da air intake system ke samar wa engine iskar da yake buƙata domin ƙonewar mai.
Ƙashi (Skeleton) shi ne ginshiƙin jiki, yayin da chassis shi ne ginshiƙin mota.
Tsokoki suna ba jiki ƙarfi da motsi, yayin da suspension system ke rage girgiza tare da tabbatar da daidaiton mota.
Haka kuma, jijiyoyin jiki (nervous system) suna isar da saƙonni zuwa dukkan sassan jiki, k**ar yadda wiring harness da sensors ke isar da bayanai zuwa ECU domin mota ta yi aiki yadda ya k**ata.
Darasi
Allah Ya halicci jikin ɗan Adam cikin cikakken tsari. Yawancin fasahohin da injiniyoyi suke amfani da su a yau suna da alaƙa da yadda halitta take aiki. Saboda haka, idan ka fahimci jikin mutum, za ka fi fahimtar yadda tsarin mota yake aiki.
Tambaya
A ganinka, wane sashe na jikin mutum ya fi k**a da gearbox, kuma me ya sa?
Ka Follow Alfidson domin samun ilimin Automotive Engineering cikin Hausa kowace rana.
Alfidson
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Kano
Opening Hours
| Monday | 09:00 - 17:00 |
| Tuesday | 09:00 - 17:00 |
| Wednesday | 09:00 - 17:00 |
| Thursday | 09:00 - 17:00 |
| Friday | 09:00 - 17:00 |
| Saturday | 09:00 - 17:00 |
| Sunday | 09:00 - 17:00 |