Hausa Channel

Hausa Channel

Share

TARIHI DA AL-ADUN ƘASAR HAUSA

12/04/2026

Hauwa Mai Tuwo matar lado

Hajiya hauwa mai tuwo matar lado da Alhaji Mamman Shata katsina ya waƙe. Ga wasu Ƴan baituka Cikin waƙar Hauwa mai tuwo matar lado

"Hauwa mai tuwo matar lado
"Tsaya kuluwa matar lado
"Hauwa kuluwa Gwaggon dije
"In kinyi miyarki ta Ƴan birni ita za na siya na ba baki..."

Hajiya Hauwa Maituwo na daya daga cikin wadanda Dokta Mamman Shata ya wake a lokacin rayuwarsa,

Kuma ku bamu naku baitin cikin wakar hauwa mai tuwo matar lado.

12/04/2026

Sir Ahmadu Bello Sardauna sakkwato Firimiyan Yankin Arewacin Najeriya Cikin Shekarar 1960 a Cibiyar Nazarin ta Kasa ta Oak Ridge, ita ce cibiyar bincike ta farko ta duniya.

Oak Ridge birni ne, da ke a cikin gundumar Anderson da Roane a gabashin jihar Tennessee ta Amurka, kimanin mil 25 (kilomita 40) yamma da tsakiyar Knoxville.

Allah ya Kyautata Makwanci.

04/04/2026

JIYA BA YAU BA

Alhaji Yusuf Maitama SuleAbout this soundYusuf Maitama Sule (Taimako·bayani), Ɗan Masanin Kano An haifi Maitama a Shekarar alif dari tara da ashirin da Tara (1929), a unguwar Yola, cikin garin Kano. Maitama shi ne na uku a jerin ‘ya’ya a gidansu, sauran yan'uwa biyu mata ne; wato, Rabi, wacce ake kira Yaya ta Zagi, Maimuna wacce ake kira Yaya ta Bichi.

An sa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiran shi Abbana. Sunan Maitama kuwa an sa masa shi ne saboda Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da mak**ai sosai lokacin basasar Kano. Akan yi wa duk wani mai suna Yusuf laƙabin Maitama.

Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mai kula da dukkan al’amuransa na gida da kula da Dawakai. Maitama, yana dan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa, wacce ake kira ‘Yarkayi ta rasu. Ita ALLAH ya yi ta ne mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bikin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan bikin, halinta da iya maganarta Maitama ya gado

A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana dan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma k**a aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.

Maitama sun tsaya zabe da shi da tsohon Malaminsa a makaranta, Malam Aminu Kano, wannan zabe ya gudana ne a Central Office, wannan abu ya faru ne cikin shekara ta 1954.

Ya Rasu a Kairo, 3 ga Yuli, 2017 Muna fatan Allah ya yi masa Rahama kuma yagafarta masa, ya kuma sa aljanna tazama makomarsa

04/04/2026


Shekaru Sha Shida 16 Kenan da Rasuwar Alhaji Abubakar Rimi

‎A irin wannan rana ta 4 ga watan Afrilu shekarar 2010 Allah yayi wa tsohon gwamnan Jihar Kano, marigayi Alhaji Abubakar Rimi, rasuwar.

‎A lokacin da yake raye,Rimi ya yi fice a siyasar Najeriya, inda aka san shi da kishin talakawa da kuma ƙoƙarin kawo sauyi, abin da ya sa ake masa laƙabi da “Limamin canji”.

Ina an ce Abubakar Rimi me kuke tunawa?

03/03/2026

Gwamna Abubakar Rimi tare da Kwamishinan Kasuwanci da Masana'antu, Muhammad Adamu, a bikin baje koli na duniya na Kaduna, cikin shekarar 1980.

Allah ya jiƙan Magabatanmu

28/02/2026

Tsohon Shugaban Kasa Mulki Soji General Sani abacha yace duk matsalar tsaron da ta taso akayi 24hr sojoji basu dakileta ba to dasa hannun gwamnati a ciki✍️. Allah ka kawo Mana Karshe wannan zalunci

Allah ya Jikan magabatan mu

Photos from Hausa Channel's post 27/02/2026

JIYA BA YAU BA Gidan Sarkin zazzau kenan a Shekarar 1960. Allah ya jiƙan magabatan mu

27/02/2026

Waiwaye..

Al-ummar Musulmi Kenan a Wata Ranar Jumma'ar Shekarar 1959 yayin gabatar da Sallar Jumma'a a Babban Masallacin Birnin Kano. Shekaru sittin da Bakwai (67) Kenan da s**a Gabata.

Allah ya jikan Magabatanmu

27/02/2026

Masallacin Jumma'a Nomans Land, Sabon Gari a Kano, Tabbas Indai a Kano Kake kasan wannan Masallacin. Masallaci ne da Alhaji G. A. Bello (Criss Cross) ya gina da zunzurutun kuɗi ₦300,000, kuma aka buɗe shi ranar 26/02/1982. Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ne ya buɗe, yayin da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji
Muhammadu Abubakar Rimi, ya zama, babban bako a wajen bikin.


Allah ya jiƙan Magabatanmu

26/02/2026

Firaminista Tafawa Balewa yayin ziyarar sojan ƙasar nan da aka girke a Congo, ranar 12 ga watan Satumba na shekarar 1963.

26/02/2026

Gamji Uban Yan Boko Sir Ahmadu Bello Sardauna.

*Ya gina Bankin Arewa -
*Ya gina A.B.U Zaria,
* Ya gina Polytechnic a Kaduna.
* Ya gina gidan rediyon Najeriya a Kaduna
*Ya gina Cibiyar Nazarin Dabbobi a Vom, -
*Ya gina Arewacin Najeriya - Investments Ltd (NNIL).
*Ya gina filin wasa na Ahmadu Bello mai kujeru 16,000, Kaduna -
* Ya gina Kwalejin Aikin Noma a Yandev. -
* Ya gina Makarantar koyon aikin jinya a Malumfashi. -
* Ya gina Kwalejin Larabci a Kano. -
* Ya gina makarantar horas da sojoji ta Najeriya a Kaduna. -
*Ya gina Makarantar Soja a Zariya.
* Ya Gina Arewacin Najeriya - Kamfanin Raya Kasa A Kaduna,
*Ya Gina Defence Industrial Corporation a Kaduna
*Ya gina jaridun New Nigeria a Kaduna
* Ya gina kamfanin buga littattafai na Arewacin Najeriya a Zariya
* Ya gina kamfanin ci gaban Arewacin Najeriya (NNDC).

Allah ya kyautata makwanci

26/02/2026

An ɗauki wannan hoto jim kaɗan bayan karɓar 'yancin Kan Nigeria, 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kofar Nassarawa
Kano