Daily Observer Hausa
wannan shafi an budeshine domin kawomuku labarai daban daban, da kuma tsage gaskiyar lamari.
21/01/2026
Allahu akbar! Mahaifiyar da wasu masu busassun zukata s**a hallaka tare da kafatanin 'ya'yanta shida (6). Allah Ta’ala ya jikan su da rahama, yasa Aljannah Firdausi ce matabbatar su, amiin.
01/05/2024
Fatima mai Zogale kenan a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, a yayin da take kan hanyar komawa birnin tarayya Abuja.
01/03/2024
Daga Shafin Ja'afar Ja'afar
Tun da gwamna bai ba wa na kusa da shi dama ko fuska su ba shi shawara ba, to kuwa lallai haƙƙi ya rataya a kan duk mai kishin Kano ya faɗa masa gaskiya.
Mai girma Gwaman Kano Abba K. Yusuf sai ka gyara mu’amillar ka da mashawartanka da kuma masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Zancen da mu ke ji shi ne kwamishina sai ya yi wata da watanni ya na son ganin gwamna kan abu mai muhimmanci amma ya kasa gani ko magana da gwamna ta waya. Wannan bai k**ata ba, domin kuwa hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
Binkicen da na yi ya nuna cewa Mallam Daurawa ya yi yunƙurin ganin gwamna don tattaunawa da shi kan matsalar Murja Kunya amma gwamna bai ba shi dama ba. Ya yi yunƙurin yi masa bayani ta waya, nan ma abin ya ci tura.
Sukar da gwamna ya yi wa Hukumar Hisba jiya a bainar jama’a k**ar mutum ne ya daɓa wa kansa wuka, domin kuwa gwamnatinsa ya zaga. Kuma dole jama’a su ce saboda Hisba ta k**a Murja Kunya gwamna ya yi wannan magana — domin kuwa a lokacin da Hisba ta ke k**a masu baɗala ta na jefa su a bayan mota gwamna bai ce uffan ba sai bayan an k**a wannan yarinya.
Duk mai hankali ya san cewa akwai hannun gwamna (ba wani gwamnati, GWAMNA) dumu-dumu a fitar da murja daga gidan yari ba bisa doron doka ba. ‘Yan watannin baya k**ar mu haukace saboda ana yunƙurin kawar da gwamnatinka ba bisa doron doka ba, amma abin takaici kai kuma ka yi wa doka hawan ƙawara saboda wata ballagaza bankaura.
The recipe for losing popularity as a leader is putting your interest on collision course with public interest. Governor Yusuf should not take this for granted.
07/06/2023
A wannan yammacin na ranar Laraba, Allah Ya yiwa Limamin waje, Sheikh Nasir Muhammad Nasir (Wazirin Kano Murabus) rasuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa za'a yi Jana'izar sa da misalin karfe 9:00 na safiyar gobe Alhamis, a Kofar Kudu dake fadar Sarkin Kano.
ALLAH Ya jiqan sa, Ya gafarta masa tare da iyayen mu da dukkan 'yan uwa Musulmi da s**a rigamu gidan gaskiya. Allah ya kyautata namu zuwan, Allahumma amiin.
28/01/2023
2023: Zamu sakawa Ganduje da halacci – Baba Musa Kwankwaso Bashir Ishaq Muhammad Mak**an Karaye kuma hakimin Madobi, Alhaji Baba Musa Kwankwaso, yace zasu duba domin aiwatar da abinda ya k**ata wajen ganin sun sakawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da halacci, dangane da irin kauna da kulawa da yake nunawa gare su.Advertisement Mak**an Karayen ya furta hakan....
02/11/2022
Sa6ani Tsakanin Garo Da Doguwa: Jam'iyyar APC A Dunkule Take - Mataimakin Gwamna
Mataimakin Gwamnan Kano kuma 'Dan takarar Gwamna a jam'iyyar APC mai mulki Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da lamarin da ya afku na sa6ani tsakanin 'Dan takarar mataimakin gwamna Alhaji Murtala Sule Garo da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya Hon. Alhassan Ado Doguwa.
Mataimakin Gwamnan yace abinda ya farun a daren ranar Litinin a gidansa dake Miller Road a Unguwar Bompai tsakanin jiga-jigan jam'iyyar biyu, lamari ne mara dadi, sai dai yace sa6ani ne da kan iya faruwa tsakani, sak**akon ajizanci na 'Dan Adam, a saboda haka yace suna bin dukkan makatai na kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.
Dr. Nasir Yusuf Gawuna wanda yayi magana ta bakin babban Sakataren Yada labaran sa Malam Hassan Musa Fagge, yace Jam'iyyar APC a dunkule take a matsayin uwa daya uba daya.
A saboda haka ya bukaci magoya baya daga bangarorin jagororin biyu da su mutumta dokokin jam'iyyar ta hanyar kiyaye lafuzan su, cewar nasarar jam'iyyar APC itace abin sanyawa gaba domin cigaban jihar Kano da al'ummar ta.
02/08/2022
Muna taya Hon. Abubakar Musa DK mataimaki na musamman a bangaren kafar sadarwa ta zamani, ga mataimakin Gwamnan Kano, Dr. Nasir Yusuf Gawuna, murnar auren sa da aka daura a ranar Asabar din karshen makon da ya gabata, tare da amaryar sa Haleematu Sadiya.
Muna rokon Allah ya sanya alkhairi a cikin auren, ya kuma azurta su da zuriyya dayyiba. Haka zalika muna addu'a ta fatan alkhairi ga dukkan auren da aka daura.
18/12/2021
Majiya- Daga Shafin Shugaba Buhari
Yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yanka cake ranar Jumu'ah a kasar Turkiya domin bikin murnar cikar sa shekaru 79 da haihuwa.
A cewar shugaba Buhari k**ar yadda ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya bayyana cewa a halin yanzu yana jiran zuwan shekarar 2023 ne inda wa'adin mulkin sa zai kare ya koma gida mahaifar sa domin cigaba da kulawa da gidan gonar sa.
Kafin hakan, shugaban yace daga yanzu zuwa wancan lokacin zaiyi dukkan mai yiwuwa wajen kyautata Najeriya da rayuwar al'ummar cikinta, ta hanyar tafiyar da ayyukan sa k**ar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Sai dai da dama al'umma na ganin cewa abin kunya ne da takaici aga shugaban yana irin wadannan bukukuwa, alhalin al'ummar da yake jagoranta na fuskantar nau'uka daban-daban na barazanar tsaro, kuma musamma yadda aka hango shugaban cikin hoto a kasar ta Turkiya ya daga wuka ya dabawa cake din mai dauke da hoton Tarayyar Najeriya, wanda hakan ya dada saka shakku a zukatan mutane na irin salon soyayyar sa ga kasar.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin bin diddigin al'amarin AbdulJabbar Sheikh Nasuru Kabara har zuwa karshensa, tare da tabbacin cewar "…babu shakka wannan yaki ne namu duka gaba daya." Ya yi wannan alwashin ne lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga Halifan Darikar Qadiriyyah, Sheikh Qariballah Sheikh Nasiru Kabara, a Gidan Qadiriyyah da ke Kabara, a Kano, ranar Juma'a da tawagarsa....
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano