Mdsmart
°°I,am Mohd Dalhat Ismail°°
"Proudly Muslim"
"Prophet Muhammad S. A. W is My Role Model"
I'am Mohd Dalhat Ismail, the norther photographer and Digital artist...... The Social Media Journalist and Blogging
With MD Smart – I'm on a streak! I've been a top fan for 5 months in a row. 🎉
10/09/2024
SUBHANNALLAH, ALLAH Y BADA TAIMAKONSA
Don Allah wanda suke cikin gari, wanda abin bai shafa ba su taimaka, idan akace antsaya jiran agajin gwamnatin al’umma zasu halaka.
Da yawan mutane suna cikin ruwan babu abinda za’a dauko su a wasu guraren k**ar post office da sauran su, Tashar bama kwale-kwale ne guda daya babu jami’an agaji ana bukatarsu a wannan guri.
Misalin titin post office zuwa General Hospital akwai wanda sun makale a gidajen sama sun gaza sauka, kuma ruwa zai shanye gidajen da mu ta ne a ciki…
02/07/2024
CIKAKKIYAR NUTSUWA!
Za ka ɓata lokacinka kuma ka wahala matuƙar kana tunanin samun aminci da nutsuwa a wurin wani. Ko da ka ga ka samu to taƙaitacce ne ko kasasshe, ko waye wannan mutumin kuwa.
Jama'a mu k**a hanyar Allah, a cikinta dukkanin nutsuwa da aminci yake. Domin duk wani da mu ka ga mun amintu kuma mun nutsu da shi huwacewa ce ta Allah, Ya sanya sinadarin nutsuwar Ya kuma nutsar da mu ɗin da shi.
Ya Allah Ka nutsar da mu da abinda Ka azurta mu da shi amin.
09/06/2024
Wasiyyata gareku…
Lura da yadda mutanen zamanin nan ke fama da cutar tsoma baki a komai, Wasiyyar Dazan muku itace,ku lazimci yawan Shiru ckn lamuranku ..
فالإنسان يحتاج إلى عامين فقط ليتعلم الكلام، وإلى خمسين عاما ليتعلم معنى الصمت
Shi Mutum Shekara 2 kaɗai yake bukata yake koyar magana, Amma zai iya Shafe shekara 50 bai gama sanin ma'ana da fa'idar dake ckn "Shiru" ba.
Shi "SHIRU" baya nufin "RASHIN MAGANA" kmr yadda galibi aka dauka, shi "SHIRU" yare ne, kuma ba kowa ke fahimtarsa ba sai "Al-Uzama'u" (Manyan mutane), domin shi fage ne da babu Mai Kewayawa ciki sai Ma'abota kwakwalwa da Zurfin Tunani. Sai yasa wata Maganar hatta Kalmomi sukan Gaza Isar da Saƙonta amma shiru kaɗan sai ya iya isarta ckn takaitaccen lkc,
Sai yasa Ni SHIRU Yare ne a wajena, yare da nake jin Daɗinsa fiye da sauran yaruka da harshe na ke furtawa😌, Ni Shiru sifa ta ce, kuma na Ɗauke shi rabin mazaaj(feeling) Ɗi nah.
ba ga kowa nake magana ba kuma ba akan komai nake magana ba, A yaren SHIRU Na koyi Ƙarancin sharhi da explain ɗin komai ga mutanen dake tare dani, Sbd nayi imani Masoyina na gaskiya zai fahimci magana ta koda ina ckn shiru, saɓanin wanda ke ƙina ko dama asalin zatonsa gareni mummuna ne😕 na riga nasan in zan shuɗe zamani wajen masa bayani ba fahimta ta zai ba.
Ku Kiyaye SHIRU, hakika shi Aboki ne da baya Ƙarya kuma baya ha'inci, sai yasa duk maganar data futo bayan zama dashi sai ka ji ta cike da Gaskiya.
Saida safen ku ‘yan uwan musulunci.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Dorayi Qtrs
Kano