SHURA TV
SHAFIN FASAHAR SADARWA NA MAJLISAR SHURA TA DARIQAR TIJJANIYYA.
مجلس الشورى لطريقة التجانية
ZIKIRIN JUMA'A DAGA ZAWIYYAR MAULANA SHAIKH MAL. AMINU MAI DIWANI Tudun wada bompai Nasarawa KANO
26/12/1447
12/6/2026
'ani
12/06/2026
Amincin Allah Ya Tabbata Ga Sayyida Amina Mahaifiyar Manzon Allah Kuzo Mu Nemi Albarkacinta 👇https://www.facebook.com/share/p/18VP3WrWht/.
Dabbobima Sun San Girman Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam 👇
https://www.facebook.com/share/p/1E3HGZKFxq/.
11/06/2026
Allah ya ƙarawa Khalifa Sheikh Fatuhu Sheikh Gibrima lafiya.
11/06/2026
ZIKIRIN JUMA'A ! ZIKIRIN JUMA'A !! ZIKIRIN JUMA'A !!! A GARIN GAYAWA UNGOGO L.G.A. A madadin wannan Zawiyya mai Albarka ta Maulanmu Sheikh Tijjani bin Usman Zangon barebari Kano Nig, Mai girma Khalifa Sayyidi Muhammadul Bashir Sheikh Tijjani bin Usman zai jagoranci Zikiriin juma'a. Rana: Juma'a 26-12-1447 B-H daidai da 12-06-2026 wuri: Zawiyyar Sheikh Muhammad Musa ( Baban makaranta Gayawa ) Gayawa Ungogo L.g.a . Loƙaci 5:00 pm izuwa Sallar Issha.
10/06/2026
DOLE CE TAKE SAKAWA A CE WANI ABU
Akwai maganar da ake yi ba dan wanda za a yi maganar ya kai ya isa ba. Ana yi ne saboda bawa ilimi haƙƙinsa ko kuma fitar da al'umma daga wani duhun da wannan shaiɗani yake da burin son ya turasu Lalle ya tabbata Maulana Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini ya yi magana a kan Ja'afar na Kano amman ba dan wani abu ba wai ko dan ya kai ko ya isa ba. Domin ko Mahmud Gumi shi kansa ya san wanene Sharif ba wai irinsu Ja'afar ba.
Kafin nan Ja'afar ya dinga yiwa ɗaukacin malamn Najeriya rashin kunya wanda dama ita s**a gada. Dalilin da ya sanya aka kula shi domin wani lokacin shiru ma yarda ce.
Wannan shi ne maganar da Sharif ya kawo a cikin littafinsa mai suna الإقتصاد في تصحيح قواعد الإعتقاد Sharif a wata gaɓa ya ke cewa;
قلت: ولقد انتشرت بدعة الخوض في المتشابهات في هذا العصر في كل أنحاء العالم، وخاصة في بعض بلدان غرب إفريقيا، ويجوز أن يكون حظ نيجيريا من ذلك الأكبر والأسوأ بسبب عدم الاستقرار السياسي والاقتصادي، ومن أمثلة ذلك أنه ورد إلى مدينة ميدغري في الآونة الأخيرة طالب متعالم وهو غمر يتميز بالجرأة والوقاحة ممن يقلد مذهب التجسيم والتشبيه وبدأ ينشر باطله بين العامة وقد نفق سوق بهرج بضاعته الزائفة بين الغوغاء والجهلة، وحين أنكر عليه علماء أهل السنة من أهل الاختصاص والمعرفة في البلد صار يطالب العلماء بأن يبرزوا له للمناظرة مع أنه لا يعرف من المناظرة أصلاً ولا فرعاً، بل حتى لا يعرف لا اسمها ولا رسمها، بل ولا شيء وإنما حمله على ذلك غروره وتصديقه ما سولته له شياطينه ووسوست إليه به نفسه، لأن رفض العلماء لمقابلته أو مناظرته إنما هو من أجل استهجانهم لأمره واستهانتهم لما تظاهر به من فجوره، فظن المسكين أنه غلب بباطله حق المسلمين الموحدين التابعين لأهل السنة والجماعة ذلك لأن الجلوس مع أمثاله يوحي بالاعتراف بباطله أو بعلمه الذي ادَّعاه وادَّعاه له الغاغة¹ زوراً وإمعاناً في الوقاحة والضلال، ورفضوا أيضاً الجلوس مع هذا المتطفل عملاً بمذهب الإمام مالك رحمه الله الذي على مذهبه جميع المسلمين في هذه البلاد، وهو ينكر الخوض في المتشابهات بين يدي العامة، قال الحافظ بن حجر العسقلاني رحمه الله في فتح الباري - عند كلامه على باب من خص بالعلم قوماً دون قوم كراهية ألا يفهموا - تعليقاً على قول الإمام علي كرم.
Mu dan yi tarjamar ma'anonin kalmomin saboda sauƙaƙa karantawa
Lallai bidi'ar zurfafa bincike a kan ayoyin da ma'anarsu ba ta fito fili ba (Al-Mutashabihat) ta yadu a wannan zamani a ko'ina cikin duniya, musamman a wasu ƙasashen Yammacin Afirka. Mai yiwuwa ma kason Najeriya ya kasance mafi girma kuma mafi muni saboda rashin kwanciyar hankali na siyasa da tattalin arziki.
Daga cikin misalan hakan akwai cewa, a kwanakin baya wani dalibi mai nuna kansa a matsayin masani ya zo birnin Maiduguri; mutum ne marar gogewa kuma marar wani matsayi a ilimi, amma ya shahara da ƙarfin hali da rashin kunya. Yana koyi da tafarkin masu siffanta Allah da siffofin halitta (Al-Tajseem) da masu kwatanta Shi da halittunsa (Al-Tashbeeh). Ya fara yada batancinsa a tsakanin talakawa, har ma bogin iliminsa ya samu kasuwa a tsakanin jahilai da taron wawaye.
A lokacin da malaman Ahlussunnah masu ƙwarewa da sani a garin s**a yi masa inkari, sai ya fara neman malamai su fito su yi muhawara da shi. Alhali kuwa shi bai san asali ko wani reshe na ilimin muhawara ba; kai, bai ma san sunanta ko yadda ake bayyana ta ba, ballantana wani abu daga cikinta. Abin da ya jefa shi cikin hakan kuwa shi ne girman kansa, da gaskata abin da shaidanunsa s**a kawata masa, da kuma abin da zuciyarsa ta yi masa waswasi.
Domin kuwa, ƙin da malamai s**a yi na ganawa da shi ko yin muhawara da shi ya samo asali ne daga ƙyamatar lamarinsa da raina abin da ya fito yana nunawa na fajirci. Sai wannan miskinin ya yi zaton cewa batancinsa ya rinjayi gaskiyar musulmai masu kadaita Allah, mabiyan Ahlussunnah wal Jama'ah. Hakan kuwa saboda zama da irinsa yana iya ba da alamar amincewa da batancinsa ko kuma ilimin da ya yi ikirari da shi, wanda taron wawaye s**a jingina masa ta hanyar ƙarya, tare da ƙara zurfafa cikin rashin kunya da ɓata.
Haka kuma, sun ƙi zama da wannan baƙo mai katsalandan ne domin aiki da koyarwar Mazhabar Imam Malik (Rahimahullah), wadda dukkan musulmin wannan ƙasa suke bi. Shi kuwa Imam Malik (Rahimahullah) yana hana zurfafa bincike a kan ayoyi masu rikitarwa (Al-Mutashabihat) a gaban ammawa.
Kamar yadda Al-Hafiz Ibn Hajar Al-Asqalani (Rahimahullah) ya ambata a cikin littafin Fathul Bari, yayin da yake bayani a kan babin: "Wanda ya keɓe wani sashe na ilimi ga wasu mutane ba tare da wasu ba, saboda tsoron kada su fahimce shi ba daidai ba," a matsayin tsokaci ga maganar Imam Ali (Karamallahu Wajhah).
Idan da kuskuren fassara a gyara mun
Mujaheed M Muh'd
2022 KHATAMAN FASSARAN DIWANI
WANDA KHALIFA IBRAHIM SHEIKH ABAGONI
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kano
3735