Kokiya
Jaridar Kokiya jarida ce Mai yada labarai cikin harshen Hausa
domin Karin bayani +2348068171406
09/06/2026
SUBHANALLAHI: Daya daga cikin dattawan da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi, Malam Yahaya Billi, ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.
Ƙungiyar Izalah JIBWIS reshen Ƙaramar Hukumar Koko-Besse ta sanar da rasuwarsa, tare da bayyana cewa za a gudanar da Sallar Jana'izar Ga'ib da ƙarfe 4:30 na yammacin yau a ƙofar gidan Sarkin Koko.
09/06/2026
Tunda bayan da Tijjani Gandu yayi waƙar Hayaniyan bana, tiri tirin bana, Matsaltsalun bana, banda mu, Har yau Kwankwasawa cikin matsala suke.
Ba su sake samun zaman nitsuwa ta watanni Uku masu kyau a jam'iyya ɗaya ba.
NNPP - Matsaltsalun Bana
ADC - Tiri - Tirin Bana
NDC - Hayaniyar Bana
Yanzu kuma ana tunanin cewar za su abka cikin Cakwalkalin cakwakiyar bana.
Daga Haj Shehu
09/06/2026
Ɗan takarar sanatan Kano ta Tsakiya a jam'iyyar NDC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya ci gaba da gudanar da tattaunawa mai zurfi domin komawa jam’iyyar ADC, tare da neman tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.
Rahotanni daga jaridar Punch, sun nuna cewa tattaunawar sauya sheƙar na ci gaba da samun tagomashi, yayin da ake sa ran Gawuna zai shiga ADC domin fafatawa a zaɓen gwamnan Kano mai zuwa.
Wacce shawara za ku baiwa Gawuna?
08/06/2026
DA ƊUMI ƊUMI: Tsohuwar ministar jinkai Sadiya Farouq ta nemi kotu ta soke sammacin k**a ta
Tsohuwar ministar harkokin jin-ƙai, Sadiya Farouq, ta roƙi babbar kotun Abuja da ta soke sammacin k**a ta da aka bayar a kanta kan zargin da ake yi mata tare da wasu tsofaffin jami’an ma’aikatar.
Farouq ba ta halarci zaman kotun ranar Litinin ba, inda lauyanta ya bayyana cewa tana fama da matsalar lafiya. Sai dai lauyan EFCC ya ƙi amincewa da sauraron buƙatar, yana mai cewa ba za a iya yin hakan ba kafin a gurfanar da ita a hukumance.
Lauyan Farouq ya dage cewa buƙatar tasa ta dace a saurare ta, domin tana neman a soke sammacin k**a da kotu ta bayar a ranar 16 ga Afrilu.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ya ɗage shari’ar zuwa ranar 10 ga Yuni domin yanke hukunci kan buƙatar da Farouq ta gabatar.
08/06/2026
'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa da Dattawan Zamfara, 50 Bayan da Sukaje Neman Sulhu:
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dattawa 50 da daga kauyen Magamin Diddi da ke yankin Magami/Faru a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, yayin da s**aje yin sulhu da wani shugaban ‘yan bindiga da ake kira Jammo.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ‘yan bindigar ne ya nemi a yi sulhu, bayan wasu daga cikin mutanensa sun mutu a wani sumame da jami’an tsaro s**a kai.
Sai dai bayan da kwamitin mutum 50 da al’ummar yankin s**a tura ya isa wurin ganawar, sai ‘yan bindigar s**a yi garkuwa da su.
Shugaban karamar hukumar Maradun, Bello Dosara ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce dattawan sun shirya yin sulhun ne ba tare da amincewa ko sanin gwamnatin jihar ba.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar Zamfara ba ta goyon bayan yin sulhu da ‘yan bindiga.
08/06/2026
Iran ta harba "kusan mak**ai masu linzami 30" kan Isra'ila tun a daren Lahadin da ya gabata, in ji wani jami'in sojan Isra'ila da sanyin safiyar Litinin ɗin nan.
08/06/2026
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta karɓi wata ƙara da ke neman a soke rajistar Jam'iyyar NDC tare da cire ta daga cikin jerin jam'iyyun siyasa masu rajista a Najeriya.
Siyasarmu TV ta rawaito a rahoton Daily Trust cewa an shigar da ƙarar ne a ranar Talatar makon da ya gabata ƙarƙashin lamba FHC/ABJ/CS/1115/2026, kuma an miƙa shari'ar ga Mai Shari'a Mohammed Umar bayan Babban Alƙalin Kotun Tarayya, Mai Shari'a John Tsoho, ya yi rabon shari'ar.
Masu shigar da ƙarar suna neman kotun ta binciki sahihancin rajistar jam'iyyar tare da ɗaukar matakin da ya dace kan ci gaba da kasancewarta a matsayin jam'iyyar siyasa mai rajista.
Sai dai wanda ya assasa jam'iyyar kuma jagoranta na ƙasa, Seriake Dickson, ya bayyana cewa babu wata ƙara ko ɗaukaka ƙara da ke gaban kotu da ke ƙalubalantar rajistar NDC, yana mai jaddada cewa jam'iyyar tana aiki bisa tanadin doka.
07/06/2026
Wike ya kare matakan sauye sauyen tattalin arziki da Tinubu ke aiwatar wa
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa jagoranci da jajircewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na taimakawa wajen rage gibin ababen more rayuwa a Najeriya.
Wike ya bayyana hakan ne yayin gabatar da lacca a bikin yaye dalibai karo na 36 na jami'ar Port Harcourt, inda ya ce ci gaban ababen more rayuwa na daga cikin muhimman alamomin ingantaccen shugabanci.
Ya yabawa gwamnatin Tinubu kan aiwatar da manyan ayyuka k**ar titunan Lagos-Calabar, Sokoto-Badagry, Abuja-Kaduna-Zaria-Kano, East-West Road da hanyoyin shiga gadar Niger ta biyu, tare da gyaran layin dogo na Port Harcourt zuwa Maiduguri.
Ministan ya kuma ce shirye-shiryen samar da wutar lantarki, gidaje, sadarwa, tsaro da ilimi, ciki har da asusun lamunin dalibai na NELFUND, na kara samar da damammaki ga ‘yan Najeriya.
Wike ya kare cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya samar wa gwamnatoci karin kudaden da za su zuba a ayyukan ci gaba da ababen more rayuwa, yana mai jaddada cewa shugabanci mai kawo sauyi na bukatar daukar matakai masu wahala domin samun dorewar ci gaba a nan gaba.
07/06/2026
'Yansanda cun ceto ƴar uwar tsohon ministan wutar lantarki da tagwayen ta da aka sace a Ibadan
Rundunar 'yansandan Najeriya ta tabbatar da ceto Misis Busayo Adelabu-John Paul da 'ya'yanta tagwaye masu shekara 12, Peter da Paul, bayan da wasu masu garkuwa da mutane s**a sace su a ranar 3 ga watan Yuni a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Mai magana da yawun rundunar, DCP Anthony Placid, ya bayyana a wata sanarwa ranar Lahadi cewa jami'an sashen tattara bayanan sirri na rundunar (FID-IRT) sun gudanar da wani samame na musamman a Ibadan da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Asabar, inda s**a yi nasarar kubutar da mutanen ba tare da sun ji rauni ba.
A cewarsa, nasarar ta samu ne bayan tattara bayanan sirri, sa ido da kuma dabarun aiki da s**a bai wa jami'an damar gano motsin masu garkuwar. Hakan ya kai ga artabu tsakanin jami'an tsaro da wadanda ake zargi.
Placid ya ce an harbe mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin har s**a mutu, yayin da aka kwato bindigogi biyu. Ya kara da cewa an kai wadanda aka ceto wurin da ya dace domin samun kulawar lafiya da sauran tallafi.
Babban Sufeton 'Yan Sandan Najeriya, Tunji Disu, ya yaba da jajircewa da kwarewar jami'an da s**a gudanar da aikin, yana mai cewa kokarinsu ne ya tabbatar da kubutar da mutanen cikin koshin lafiya.
Rundunar ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da farautar sauran mambobin kungiyar masu garkuwar da s**a tsere, inda bayanan farko s**a nuna cewa wasu daga cikinsu sun tsere da raunukan harbin bindiga.
An sace Misis Busayo Adelabu-John Paul, wadda ke kanwar tsohon Ministan Wutar Lantarki, tare da 'ya'yanta tagwaye a safiyar ranar 3 ga Yuni yayin da take kai su makaranta a yankin Elewura da ke Challenge a Ibadan. Lamarin ya jawo damuwa a tsakanin iyalanta da kuma al'ummar siyasar Jihar Oyo.
06/06/2026
Gwanin Burgewa: Yadda shugaban ƙaramar hukumar Mafara dake jihar Zamfara, Hon. Yahaya Yari, ya haye saman dutse a cikin daji inda 'yan bindiga ke yawo tare da bayyana cewa ya shirya mutuwa akan al'ummarsa da yake shugabanta,
Mezakuce?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano