Bashir BARAU

Bashir BARAU

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bashir BARAU, Health/Beauty, Gwale ward, Kano.

15/10/2022

KURA DA SHAN BUGU GARDI DA....
Iyaye su suke shan wahalar haihuwa da reno da dawainiya da kuma tarbiyyar 'ya'yansu, amma da sun data rana a tsaka sai wani yazo ya fizgesu ya mallake zuciyoyinsu dama gabobinsu kai har ma da rayuwarsu gaba daya. Ba ina nufin masu satar mutane ba a'a ina magane kan masu juya rayuwar yara yadda suke so fiye da iyayensu kuma ta hanyar ma da bata dace ba wato da sunan 'YAN SIYASA KO MALAMAI KO 'YAN SHARHOLIYAR GARI, zakaji yaro yana cewa ko ubana bai isa yahanani ra'ayin dan siyasa wane ba ko ubana bai isa ya hanani bin malami wane ba ko ubana bai isa ya hanani yin rayuwata yadda nakeso ba.
To shine nake cewa bai kamata iyaye su zura ido wasu suna sarrafa rayuwar 'ya'yansu don biyan bukatun kansu ba, a wasu lokutan ma suna karkatar da rayuwar yaran izuwa halaka kuma iyaye suna kallo. Allah SWT yana fada mana a Alkur'ani cewa 'Ku tseratar da kawunanku da iyalanku daga shiga wuta... '
Don haka dai yakamata kowa ya ja 'ya'yansa a jiki, akai akai yasan halin da suke ciki dangane da rayuwarsu ta yau da kullum, da irin abokansu da irin akidarsu ta addini wannan yana da muhimmanci, kai da ma ra'ayin siyasa. Iyaye musamman uba yakamata ya zama kan tafarki nagari kuma ya tabbatar 'ya'yansa suma suna kan wannan tafarkin, idan kuwa baka bawa danka aikinyi ba to fa shedan yana da abin da zai bashi, ma'ana idan baka da lokacin sanya yaronka a hanya mai kyau to akwai wadanda suke da lokacin sanya shi a mummunar hanya. Allah ya sawwake. Allah ya shirya mana yaranmu.

16/09/2022

KANMU A WAYE YAKE AMMA FA 'YAN UWA MU KARA HATTARA:
1. A kokarin makiya musulunci na dagula lamuran musulmin arewacin najeriya ta hanyar amfani da kafafen sa da zumunta, da farko suna amfani da banbance banbancen dake tsakanin musulmi suna yin kutse suyi zagi da aibata wani bangare a matsayin su musulmi ne 'yan wani bangare, kuma da daga nan sai su goce su kyale wawaye suyi ta s**a da aibata juna.
2. A yanzu kuma ganin hakansu yaki cimma ruwa shine s**a fito da wata dabara amma a irin nasu tunanin, wato ta amfani da arna a matsayin su Hausawa ne ko ma musulmai da kuma wawaye 'yan babu ruwansu da addini,, suna amfani da yanayin da ake ciki na rashin tsaro suna yada maganganun raba kan Hausawa da Fulani har ta kai suna zagin Shehu Usmanu dan Fodio wai ya zalunci Hausawa. To yanzu kuma kiyayyar tasu da arnancin nasu sun gagara boyewa, sun fara fito da manufarsu ta dirarwa addinin musulunci kai tsaye, yanzu suna fassara wasu shibhohi wato labaran karya da aka rubuta da harshen turanci don bata musulunci a idon arna, suna yadawa kan wai Larabawa sun bautar da 'yan Afrika, sun tursasasu yin musulunci ta dole, daga nan zakuji sunyi gaba in sun sami hali.
Abin tsokaci anan shine yakamata musan cewa mu al'ummar musulmi hausa/fulani kanmu a waye yake wajen gane irin wadannan shegantakun, amma kuma dole ne muyi hattara da sanya ido tare da taka tsantsan dangane da bibiyar irin wadannan rubuce rubuce, musamman ga masu zafin akida. Allah ya kara kare musulunci da al'ummar musulmi daga sharrin makiya, Allah ya karawa Annabi daraja.

31/08/2022

KIRA GA 'YAN UWA TALAKAWA:
1. Tabbas talaka ya wahala a hannun shugabanni ' Yan siyasa.
2. To yanzu ga lokacin sake zaban shugabanni ya karato kada mu yarda mu dawwamar da kanmu cikin wahala, mu tsaya muyi tunani a karan kanmu kada mu dogara da tunanin wasu kawai.
3. Bai kamata mu ci gaba da zaben shugabanni da zasu rika wahalar damu ba.
4. Kada a yaudaremu da abin da bazai raba mu da talauci ba wajen yin zabe.
5. Kada soyayyar jam'iyya ko wani dan siyasa ya sanya mu yin zabe da ka.
6. Ya kamata musan farashinmu mu talakawa, ma'ana abubuwan da muke da bukata, su kuma 'yan siyasa muji irin tayinsu garemu, ma'ana me zasu iya yi mana daga bukatunmu, amma kada kawai muce sai wane sai wane saboda kawai dan jam'iyya kaza ne ba tare da yarjejeniya da alkawarin abin da zai yiwa talakawa ba. Mun dai san abin da ya faru jiya. Allah yasa mu fahimta

26/08/2022

NAJERIYA-DUNIYAR GIZO:
Kasarmu Najeriya kasa ce da Allah yayi mata baiwar jama'a da arziki. Gata da shuawagabanni masu kishi masu jajircewa, ga dattawa masu dattaku, ga matasa masu kishi da hamasa, ga kuma talakawa masu biyayya wannan yasa aka samu zaman lafiya da karuwar arziki da jin dadi amma fa a da.
Yanzu da ake cewa anci gaba, takardun shedar karatuttuka sun Karu, daktoci da farfesoshi da 'yan yangu yangu masana sun karu sai kuma shiririta ta Karu. Yanzu kusan komai a Najeriya ya koma labarin Gizo da Koki ko ince Tatsuniya.
Shuganni na gizo, Talakawan gizo, Dimokadiyyar gizo, 'yan siyasar gizo, Masana 'Yan bokon gizo, Malaman gizo, Dattawan gizo, Matasan gizo, ci gaban gizo, bunkasar tattalin arzikin gizo, tsaron gizo, 'Yacin dan Adam din gizo...... . Kai komai ya zama rayuwar gizo a Najeriya, Allah ya kawo mana mafita.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Gwale Ward
Kano