itz_alsheikh

itz_alsheikh

Share

We specialised in selling of all kinds of tricycle and motorcycle

05/04/2026

RANAR DA UBA DAN NIGERIA YA KIRA ‘YAN SANDA WA ‘YARSA A UK…

Yarinya ce 'yar shekara 14
Lokacin da suke Najeriya Lafiya lau ta ke Ga Da’a da Kuma Girmama iyaye just like every average Nigerian child.
Babu wata matsala ko kadan.

Da s**a koma UK ma, har yanzu haka take
kwatsam… wani abu ya canza.
“Shut up!” ta fada wa mahaifiyarta wata rana. 😳
Uwar ta tsaya cak.

Ta ce wata kila fushi ne kawai…
Inaaaa.....Abu sai kara gaba yake...

Idan mahaifinta ya yi magana?
Sai ta zo gabansa, ta tsaya kirji da kirji, idanu cikin idanu… k**ar tana kalubalantarsa.

Da farko s**a ce “teenage phase”
Wata rana, mahaifin ya ce ta yi abu mai sauki.
Ta ki.
Ta tsaya a gabansa, ta ce: “Ba zan yi ba.”

Sai ta tsaya… tana kallo… tana jiran ya dau mataki.
Kasan halin iyayen mu na nan Najeriya tuni zai tabbatar maka Shi Ne 'UBANKA"🤣

Amma uban nan ya yi abin da babu wanda ya zata.
📞 Ya dauki waya… ya kira ‘yan sanda.

Uwar ta firgita: “Da gaske kake?!”

Ya ce cikin nutsuwa: “Idan na taba ta, ni za su k**a.

Da ‘yan sanda s**a zo,yayi musu bayani yace Yana gani ta sami tabin hankali “kawai Ku tafi da ita.”

A UK, idan yaro ya fara irin wannan hali, sau da yawa suna zargin matsalar mental health.

Sai s**a ce za su kai ta a duba.
Da jin kalmar nan “mental health”…
karfin gwiwarta ya karye .
Nan take.
Ta fara kuka. “Please mummy… please daddy…” 😭
Amma uban? Ko motsi bai yi ba.

“Ku tafi da ita,” ya sake maimaitawa.
Kuma s**a tafi da ita.

Washegari, social services s**a zo.
S**a ce: “Ta kwana tana kuka. Tana son tai magana da shi.”
Uban ya ce: “Ba yanzu ba.”

Rana ta biyu: “Ba ta ci abinci ba. Tana roko.”
Daga baya ya amince ya ganta.
Da ta dawo gida…

Kai tsaye ta durkusa Tana Kuka.Roko.Neman gafara.

A nan ne gaskiya ta fito.
Abokanta a makaranta ne s**a koya mata.

“Ki tsokani iyayenki.
Ki sa su dake ki.
Ki kai kara.
Gwamnati za ta dauke ki, ta ba ki gida, kudi Mai yawa zaki samu freedom… 😅
A tunaninta?
Rayuwarta za tayi“upgrade”.
Ta zama chicks ga Soft life.

UBAN Nan Ya canza wasan gaba daya.
Script din da ta shirya…
ya juyo kanta.

True story......

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Kano