R.T.D YOUTH Development

R.T.D YOUTH Development

Share

Wannan feji na Aikin yada bayanan cigaban wannan kungiya

02/05/2025

Award da akabawa shugaban matasa na R.T.D youth development (Alh. Mudassir Adam Dan Shayi)/ (Sahibul Hubbi)

Photos from R.T.D YOUTH Development's post 04/04/2025

4/4/2025

Gina Matasa Shine Burin Da Muka Sanya Gaba.

Shugaban Kungiyar Cigaban Matasan Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa, Alhaji Mudassir Adam Danshayi, ya gudanar da zama na musamman da wakilan Kungiyar Daliban Fannin Shari’ah daga Kwalejin Koyon Addinin Musulunci da Shari’a ta Malam Aminu Kano a ofishinsa.

A yayin taron, Alhaji Mudassir ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki tare da yabawa irin hangen nesa da ƙoƙarin daliban wajen ganin cigaban al'umma.

Ya kuma tabbatar musu da cikakken goyon bayansa kan manufofin su na cigaba da alkhairi.

Ya ja hankalin su da su kasance masu haƙuri da jajircewa, tare da janyo hankalin sauran mambobin da s**a kasance a gefe domin su ma su bayar da gudunmawa ga cigaban Kungiyar.

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Daliban Shari’ah, Abdullahi Mudassir Salisu, ya bayyana manufar zuwansu da cewa sun zo ne domin tattauna muhimman batutuwa tare da neman haɗin kai da goyon bayan Alhaji Mudassir Adam Danshayi, wanda kuma shi ne Shugaban Gidauniyar Sahibul Hubbi, bisa irin rawar da yake takawa wajen cigaban matasa.

Ya kuma gode masa bisa karɓar su da kuma tabbatar da goyon bayansa.

Sa hannu:
Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Shugaban Kungiyar Cigaban Matasan Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa
Karkashin Gidauniyar Sahibul Hubbi

Photos from R.T.D YOUTH Development's post 21/01/2025

Press Release

Al'ummar Garin Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta sun yabawa Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Rimin Gado Tofa Dawakin Tofa Alhaji Mudassir Adam Danshayi kuma Shugaban Gidauniyar Sahibul Hubbi abisa rawar da yake takawa wajen samar da cigaban yankin Karamar Hukumar Rimin Gado.

Malam Abdu Isa Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta ne ya bayyyana hakan a lokacin da s**a ziyarci Shugaban o ofishinsa.

Sun kuma jaddadada goyon bayansu ga manufofi da Tsare-Tsaren Shugaban.

Da yake nasa Jawabin, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya tabbatarwa da al'ummar Garin Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta cewa zai cigaba da bada fifiko wajen ganin sun samu yanayi mai kyau na cigaban yankin.

Ya Kuma gode musu abisa ziyarar tare da basu goyon baya domin cimma abinda aka sanya a gaba.

Zai Kuma dauki duba lafiyar idanun daya daga cikin mutanen Unguwar Mahauta abisa yanar Ido dake damunsa.

Haka zalika, Shugaban ya karbi bakuncin matasa daga Mazabar Yalwan Danzial a ofishinsa, da yake Jawabinsa na maraba agare su, Shugaban yaja hankalin su wajen dogaro da kai da barin kazamar Siyasa da banbadanci.

Ya kuma yaba musu tare da kara rokon su wajen haduwa guri guda domin kawowa yankin cigaba.

Da suke Jawabansu matasan sun yabawa Shugaban abisa kulawar sa da mutuntasu da yayi wajen basu lokaci domin tattaunawa da shi.

Sun kuma jaddadada goyon bayansu agare shi da kuma bukatar ganin an farfado da ayyukan da Kungiyar take aiwatarwa zuwa wasu fannoni masu mahimmanci.

Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Chairman Rimin Gado Tofa Dawakin Tofa Youth Development founder na Sahibul Hubbi Foundation.

Photos from R.T.D YOUTH Development's post 08/12/2024

08/12/2024

_Burina Shine Al'umma su samu Cigaba domin dorewar zaman lafiya._

Al’ummar Jujin Gobirawa Unguwar Mahauta da ke karamar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano, sun nuna jin dadinsu ga Alhaji Mudassir Adam Danshayi, Shugaban Kungiyar Cigaban Matasan Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa, bisa sadaukarwar da yake yi na ci gaban al’ummarsu.

A ganawar da s**a yi da Shugaban kungiyar, karkashin jagorancin Malam Audu na Babale, al’ummar sun bukaci Shugaban Kungiyar Daya shige musu gaba izuwa Gwamnatin Jiha da Karamar Hukumar Rimin Gado wajen a tallafa musu wajen magance rushewar gidajensu a lokacin damina, da gina musu guraben ajujuwa na makarantun firamare da Islamiyya, da kuma kaura daga mahallin da suke ciki.

Sun yi nuni da cewa al’ummar yankin sun kai dubu daya, inda suke da gidaje kusan dari da hamsin.

Hakazalika sun kara da cewa irin wadannan kungiyoyi sune wadanda Gwamnati ya kamata ta hada hannu dasu ba.

Da yake mayar da martani, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya jajanta musu halin da suke ciki tare da tabbatar musu da aniyarsa ta warware matsalolin da kuma shige musu gaba wajen cimma abinda aka sanya a gaba.

Ya yi alkawarin bayar da shawarwari ga gwamnati da kuma neman tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu don rage matsalolin da al'umma ke fuskanta.

Shugaban kungiyar Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya kuma bukaci al’umma da su cigaba da yiwa shugabanin kasa, jaha, da kananan hukumomi addu’a domin samun dorewar zaman lafiya da cigaban yankin.

Ya Kuma bukace su dasu kasance masu hakuri da juriya a duk halin da s**a tsinci kansu.

Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Chairman Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa Youth Development.

Photos from R.T.D YOUTH Development's post 18/11/2024

Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa Ya Yaba da Shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na Gina Ajujuwa na Sikandire a Garin Danshayi.

Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa, Alhaji Mudassir Adam Danshayi, ya bayyana godiyarsa mai zurfi ga Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa umarninsa na gina wani block ɗin ajujuwa a garin Danshayi,mazabar Karofin Yashi, karamar hukumar Rimin Gado.

Da yake bayyana wannan mataki a matsayin babbar hanya ta inganta ilimi da kuma kawo cigaban da zai dore a yankin, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya yaba da jajircewar Gwamna wajen inganta rayuwar al’ummar yankin.

Haka kuma, Shugaban ya miƙa godiyarsa ga gidan Rediyon Premier bisa rahoton da s**a bayar kan kokarin wata mace mai kishin ilimi da ta shafe sama da shekaru ashirin tana koyar da mata da marasa galihu a garin Danshayi domin Cigaban al’umma.

A cikin jawabinsa, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Rimin Gado da su goyi bayan wannan baiwar Allah domin cimma burinta.

Ya kuma tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da tallafa mata da sauran mutane domin cigaba da wannan aikin alheri na koyar da mata da waɗanda ba za su iya biyan kuɗin makaranta ba.

Alhaji Mudassir Adam Danshayi
Shugaba
Kungiyar Raya Matasa na Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa

Photos from R.T.D YOUTH Development's post 11/11/2024

Assalamu alaikum.

A yau ne Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Kananan Hukumomin Rimin Gado/Tofa/ Dawakin Tofa,Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya gana da Kansilolin Mazabun Gulu, Karofin Yashi, da Dawakin Gulu duk cikin ayyukan cigaba da Kungiyar ke gabatarwa wajen Bunkasar tattalin arzikin yankin.

Hakazalika, Alhaji Mudassir Adam Danshayi yaja hankalin su wajen jin tsoron ALLAH a lokacin gudanar da ayyukan su, tare kira agare su dasu tabbata sun kawo cigaban yankunan su.

Daga bisani ya jaddada kudirinsa na ganin samar da tsare-tsare na cigaban Kananan Hukumomin.

Ya kara da yin addu'ar fatan alkhairi ga Shugabanni da jagororin Kananan Hukumomin na ganin samun nasara da dorewar zaman lafiya a yankin da samun bunkasar tattalin arziki. ALLAH ya bamu zama lafiya da cigaban yankunan mu,Amin.

Shugaban Kungiyar Cigaban Matasa na Kananan Hukumomin Rimin Gado/Tofa/Dawakin Tofa.
Alhaji Mudassir Adam Danshayi

Photos from R.T.D YOUTH Development's post 31/07/2024

R.T.D YOUTH DEVELOPMENT (31-07-2024)


Assalamu alaikum.
A madadina shugaban kungiyar cigaban matasa RTD,Alhaji Mudassir Adam Danshayi ina mika godiya ga Kungiyar Red Cross RiminGado,Tofa,da Dawakin Tofa Detachments abisa ziyara domin tattauna muhimman al'amuran cigaba da s**a shafi yankunan mu.

Haka zalika ina kira ga matasa dasu zama masu dogaro da kansu tare da kaucewa duk wani yanayi dazai kaisu yin dana sani a rayuwar su.

Ina fatan sun koma gida lafiya. Nagode.

Musa K Musa
Media aide
to the chairman

Photos from R.T.D YOUTH Development's post 28/07/2024

R.T.D YOUTH DEVELOPMENT (28-07-2024)

Assalamu Alaikum. A madadin shugaban kungiyar cigaban matasan RTD,Alhaji Mudassir Adam Danshayi, na mika godiyarsa ga matasa Yan gwagwar maya masu son cigaban matasa na wadannan yankunan abisa ziyarar da su kawo Domin Tattauna batutuwan Cigaban matasa.

Mai Girma chairman na kira ga matasan dasu jajirce wajen tabbatar da cigaban yankin su.

Daga karshe Yana fatan alkhairi Agare su da Fatan sun Koma gida lafiya.

Musa K Musa
Media aide
to the chairman

13/06/2024

FINA-FINAN BATSA (BLUE FILMS).

Idan ka Karanta ka Turawa Sauran Ƴan Uwa Domin Su Amfana.

BLue FiLms Fina-finai ne da Wasu Tsageru Daga Cikin Yahudawa Suke Shiryarwa Wanda Yana da ILLa Sosai.

Domin Yanzu Anyi IttiQakin Cewa Ba Abin da Yake Saurin Rufta Mutum Zuwa Zinace-zinace Kamar Shi KaLLon BLue FiLms Ɗin Wanda Zamani Yazo da shi, Ba Ga Namiji ba, Ba Kuma Ga Mace ba.

Babban Abin Takaici Yanzu Yan Mata Sunfi Kowa Qwarewa Wajen Iya KaLLon Wnnn LaLaci na BLue FiLms.

HUKUNCIN SA:

KaLLon Tsaraici Haramun Neh a Shari'ar MusuLunci in Banda Na Matarka Ko Na Mijin ki, BaLLantana Kuma KaLLon Saduwa Tsakanin Mazinata, Wnnn Abune Mai MatuQar Muni Sosai.

Allah Yana Cewa:

"Ka Gayawa Muminai Maza su Rintse Idanuwansu Daga KaLLon Haram Kuma Su Kiyaye Daga Yin Zina".

'Yan Uwa Mu Kiyaye, Duk Wanda Yake KaLLon Irin Waɗannan Abubuwan to LaLLai Yayiwa ALLAH Tawaye.

A Wani Gurin ALLAH Yana Cewa:

"Kada Ku Kusanci Zina hakika ita Zina ALfasha Ce Kuma Mummunar Hanya ce".

Kunga Saboda HaLakan da Take Cikin Zina, Sai ALLAH Yace Kada Mu Kusanceta, shi Kuwa Irin Wnnn KaLLon Yakan Sanya Masu Yinsa su Afka Cikin Zina Kai Tsaye.

Manzon Allah (S.A.W) Yana Cewa:

" ALLAH ka Tsinewa Mai kallon Tsaraici da Kuma Wanda Ake KaLLon Tsaraicin nasa".

Daga Qarshe Ina Qara Jawo HankaLin Masu Yi su Tuba su Daina.....!!!

Sannan KaLLon Fina-finan Batsa Yana Kai Mutum Zuwa ga Aikata Mummunar Ɗabi'ar Nan ta Istim'na'i Wacce Itama Tana da iLLoLi Ga Lafiya.

Ya ALLAH Ka Tsarkake Mana Zukatan Mu, Ka Kare Zuri'ar Mu Daga Afkawa Cikin Mummunar BaLa'in Dake Tattare Da KaLLon BLue FiLms.🙏🙏🙏

ALLAH Ya Qara Shiryar da Mu da ƴan Uwan mu Masu Aikatawa.

Gaskiya dayaa

26/03/2024

R.T.D YOUTH DEVELOPMENT (26-09-2024)


A yau ne abisa jagorancin Shugaban kungiyar cigaban matasan Rimin gado, Tofa da Dawakin Tofa, Alhaji Mudassir Adam Danshayi ya kai ziyarar gabatar da kungiya da kuma kudire-kudiren da zasu taimaka wajen tafikar da cigaban al'umma dama yan kunan baki daya.

Taron ya gudana a ofishin shugaban Karamar Hukumar, Hon. Zangina Galadima Zango dake sakatariyar karamar hukumar ta Rimin gado.

Mai girma shugaban karamar hukumar Hon. Zangina Galadima ya karbi shugabancin kungiyar ta hannun jagoranta Alh. Mudassir Adam (Dan-shayi) dama sauran mambobin kungiyar.

A karshe shugaban kungiyar ya taya mai girma shugaban Karamar Hukumar murnar nada shi da akai matsayin riko, kuma ya jajanta masa bisa nauyin da Allah ya dora masa.

Ya kuma yi masa fatan alheri da addu’ar nasara.

Musa K Musa
Media aide
to the chairman

21/03/2024

R.T.D YOUTH DEVELOPMENT / KANO NORTH YOUTH DEVELOPMENT ASSOCIATION (K.N.Y.D.A)

21/03/2024

Bayan Kammala liyafar shan ruwa da shugabancin kungiyoyin cigaban matasan Rimin gado, Tofa da Dawakin tofa karkashin jagorancin Alh. Mudassir Adam (Dan-shayi), shugaban ya kai ziyarar gaisuwar dattawa da marasa lafiya cikin kwaryar garin Rimin gado.

An yi liyafar shan ruwan ne a bakin babban ofishin kungiyar dake karamar hukumar rimin gado. Inda ya'yan kungiyar dama jama'ar gari s**a halarta.
An gudanar da addu'o'i da al'ummar yankunan dama jama'ar jihar Kano baki daya.

Daga karshe a madadin kungiyar shugaban Alh. Mudassir Adam ya amshi sakunan fatan alheri dama addu'o'in jama'ar da s**a hilarci wannan taron.

Media aide
To the chairman

(Musa k musa)

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano

Opening Hours

Saturday 09:00 - 12:00
Sunday 09:00 - 12:00