Kano Progressive Media Network

Kano Progressive Media Network

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kano Progressive Media Network, Media/News Company, Kano.

Photos from Kano Progressive Media Network's post 27/05/2026

GUDUNMUWAR BARKA DA SALLAH:

ƘUNGIYOYIN SOCIAL MEDIA NA KANO TA AREWA DA JIHA SUN YABAWA SANATA BARAU I. JIBRIN

Ƙungiyoyin Social Media na Kano ta Arewa da Jihar Kano baki ɗaya sun miƙa saƙon godiya da jinjina ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Ƙasa, Sanata Barau I. Jibrin, bisa irin kulawa, goyon baya da gudunmawar alheri da yake ci gaba da bai wa matasa da ƙungiyoyin sadarwa na zamani a faɗin jihar.

Ƙungiyoyin sun bayyana cewa Sanata Barau jagora ne mai hangen nesa, wanda ya fahimci muhimmancin kafafen sada zumunta wajen wayar da kan al’umma, yaɗa ayyukan alheri da bunƙasa cigaban dimokuraɗiyya da zaman lafiya.

A cikin sanarwar da aka fitar ta hannun shugabannin ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagorancin DG Social Media na gidan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Hon. Basiru Yusuf Shuwaki (SLA), sun yaba da irin yadda Sanatan ke ƙarfafa matasa tare da ba su damar taka rawar gani wajen tallata ayyukan cigaba da manufofin gwamnati.

Ƙungiyoyin sun kuma tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da haskaka nasarori da ayyukan alherin da Sanata Barau I. Jibrin ke gudanarwa a Kano ta Arewa da Jihar Kano baki ɗaya, musamman waɗanda s**a shafi cigaban matasa, ilimi, zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziki.

Haka zalika, sun yi amfani da wannan dama wajen taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar Babbar Sallah, tare da addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya maimaita mana wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya, zaman lafiya da yalwar arziki.

A ƙarshe, ƙungiyoyin sun roƙi Allah Ya ƙara wa Sanata Barau I. Jibrin lafiya, hikima da ɗaukaka, Ya kuma ci gaba da ba shi ikon yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana.

DG Social Media Hon. Basiru Yusuf Shuwaki

— Sanarwa Daga:
Auwal Wadata Sansan
Shugaban Ƙungiyar Kapmen Yankin Kano ta Arewa

26/05/2026

Sanarwa ta musamman...
SOCIAL MEDIA...

Muna kira ga dukkanin Shugabannin Kwamittocin ƙananan hukumomin Kano ta Arewa na Social Media da Ƴan kwamitin Shiyyar Kano ta Kudu da Kano ta Tsakiya da Shugabannin Ƙungiyoyin da muke dasu, da suzo domin amsar kuɗaɗen hidimar Sallah kamar yacce Mai girma Mujaddadi Dsp. Dr. Barau I. Jibrin (Maliya), PhD. Cfr. Ya saba bayarwa aduk shekara

Rana: Yau, Talata 26/05/2026
Lokaci: 3:30pm
Wuri: Inda aka saba gudanar da taro

Sanarwa;
Basiru Yusuf Shuwaki
D.G Media na Dsp. Dr. Barau PhD.

Photos from Kano Progressive Media Network's post 26/05/2026

A jiya Litinin 25/05/2026; aka gudanar da taron manema labarai kan yadda rabon Takin Zamani na noma zai kasance, wanda mai girma mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya zaɓaɓɓen Sanatan Kano ta Arewa, kuma Ɗantakarar Sanata karo na huɗu a kakar zaɓe me zauwa ta 2027, Sanata Dakta Barau I. Jibrin PhD. Cfr. Zai rabawa Manoman yankin sa da yake wakilta na Kano ta Arewa kamar yadda ya saba a duk shekara. A wannan karon Mai girma Sanatan zai raba Tirela 88 ga Al'ummar yankin nasa wanda Mutane 53,040 zasu amfana da wannan Takin a faɗin ƙananan hukumomin Kano ta Arewa 13.

Hon. Prof. Muhammad Ibn Abdallah Shugaban ma'aikatan Ofishin Mai girma mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya tare da Hon. Sh*tu Madawaki Ghari Mai magana da yawun Sanatan sune s**a jagoranci zaman.

Taron yasamu halattar manya manyan jagorori daga dukkanin ɓangarorin Kano ta Arewa tare da ƴan jaridu da ƴan Social Media.

Basiru Yusuf Shuwaki
D.G Social Media na Dsp. Dr. Barau PhD.
26/05/2026

25/05/2026

SANATA BARAU I JIBRIN MALIYA ZAI RABAWA AL’UMMAR KANO TA AREWA NAIRA MILIYAN DARI DA TALATIN DA HUDU DA DUBU DARI TARA (1,34,90000) BARKA DA SALLAH

Al’umma maza da mata na yankin Kano Ta Arewa suna ci gaba da bayyana farin ciki da jin dadinsu bisa irin kulawa, tausayi da kuma jajircewar da Mai Girma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Barau I. Jibrin ke nunawa al’ummar da yake wakilta.

A wani babban mataki na kara kusantar al’umma da tallafawa rayuwarsu musamman a wannan lokaci na shagulgulan babbar Sallah, Mai Girma Sanata DSP BARAU I JIBRIN MALIYA zai gudanar da rabon sakon barka da sallah na kimanin Naira miliyan Dari da talatin da hudu da dubu dari tara ( #134,900,000) domin faranta ran al’ummar Kano Ta Arewa baki daya.

Wannan karamci da tallafi ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar musulmi ke shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah, lokaci wanda iyalai da dama ke bukatar taimako da kulawa domin gudanar da rayuwa cikin walwala da farin ciki.

Rabon tallafin zai hada da shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress na Kano Ta Arewa, shugabannin EXCO, wakilan mazabu guda 141, matasa maza da mata, kungiyoyin CRC LAFIYA JARI, kungiyar YAN TAURI, da kuma kungiyar Abba Gida Gida Organization tare da sauran al’umma masu bukata.

Hakika, wannan aiki babban shaida ne dake nuna cewa Sanata BARAU I JIBRIN ba kawai jagora bane, har ila yau uba ne mai tausayin talakawansa, wanda kullum burinsa shine ganin rayuwar al’umma ta inganta. A duk lokacin da bukatar jama’a ta taso, yana kasancewa a gaba wajen tallafawa da samar da mafita.

Ba a dade ba ma, cikin satin daya gabata, Mai Girma Sanatan ya kaddamar da rabon taki ga manoman Kano Ta Arewa, inda aka raba sama da buhunan taki dubu hamsin da uku domin bunkasa noma da karfafa tattalin arzikin manoma.

Wannan ya kara tabbatar da cewa jagorancinsa ya ta’allaka ne akan aiki tukuru, tausayi da cigaban al’umma.

A yau al’ummar Kano Ta Arewa na iya cewa cikin alfahari cewa sun samu shugaba mai hangen nesa, shugaba mai tausayi, kuma jagora wanda yake fifita bukatun jama’a fiye da komai.

Muna kara godewa Allah Madaukakin Sarki daya azurta mu da shugaba irin DSP BARAU I JIBRIN MALIYA. Muna rokon Allah Ubangiji Ya kara masa lafiya, hikima, daukaka da karin nasara a dukkan al’amuransa, Ya kuma ci gaba da amfani da shi wajen kawo ci gaba da walwalar al’umma.

Allah Ya kara daukaka Mai Girma Sanata DSP BARAU I JIBRIN MALIYA.
Allah Ya albarkaci Kano Ta Arewa.
Allah Ya sanya alheri cikin wannan Sallah.
Amin summa Amin.

Photos from Kano Progressive Media Network's post 25/05/2026

DSP. Dr. Barau I. Jibrin PhD. CFR. Ne GATAN ILMI kuma GARKUWAN ILMI a duk faɗin Arewacin Najeriya.

1. Ya Kawo Federal Polytechnic Kabo
2. Ya Kawo Open University 13 L.G
3. Ya kawo Study Centres reshen FUDMA
4. Ya kawo Resunan FCET Bichi a L.G 5
5. Ya biya Scholarship ga Ɗaliban gaba da sakandire na Kano ta arewa
6. Ya rabawa Ƙungiyar Dalibai na manyan Makarantu Motoci
7. Ya Dalibai na gaba da Sakandire Mashina
8. Ya Rabawa Daliban gaba da sakandire Kekuna
9. Ya rabawa Daliban gaba da sakandire Kwamfutoci
10. Ya Rabawa Daliban gaba da sakandire Wayoyi
11. Ya kawo Police College
13. Ya gina Blocks masu yawa a makarantun Kano ta arewa
14. Ya raba kujeru a dukkanin makarantun kano ta arewa
15. Yana biyawa Daliban Sakandire Ƙuɗin Jarabawar NECO ga waɗanda s**a faɗi Jarabawar Qualifying duk shekara.
16. Tura Ɗalibai Ƙasashen Waje Domin Yin Degree na II

Basiru Yusuf Shuwaki DG media

Photos from Kano Progressive Media Network's post 21/05/2026

Muna zargin Baffa Babba Ɗan'agundu da yiwa Jam'iyyar APC zagon ƙasa.

Babu ko shakka maganganun da Baffa Babba yakeyi a wannan gaɓar zagon ƙasa ne da neman rarraba kawunan ƴaƴan jam'iyyar APCn Jihar Kano musamman Shiyyar Kano ta Arewa wacce itace GOLDEN ZONE a gurin dukkanin wani ɗan tsohuwar jam'iyyar APC, Shiyyar da ita kaɗai ce Jam'iyyar APC taci Sanata da Ƴan Majalissu ta kawowa shugaban ƙasa kuri'a tare da ɗan takarar gwamna na wancan lokacin, duk wani me kishin jam'iyyar APC da son tayi nasara a jihar Kano bazai rinƙa yin kalamai na tunzuri da rarraba kawunan ƴaƴan jam'iyyar ta APC ba, musamman ya rinƙa ƙara rura wutar fitina tsakanin Sanata Barau da ATM Gwarzo wanda sun riga sun haɗe zasu yiwa APC aiki tun daga sama har ƙasa, a wannan gaɓar da tafi kowacce gaɓa haɗari, gaɓar da ake taka tsantsan da gudun faɗawa cikin rarrabuwar kawunan ƴaƴan jam'iyya a gaɓar shi Baffa Babba Ɗan'agundu zai fito yana iƙirarin babu sulhu a siyasar wani yanki daba nasa ba.

Duk wani ɗan Jam'iyyar APC dama wanda ba ɗan Jam'iyyar ba idan ka tambaye shi wanne zone ne ko kokwanto basayi zone ɗin Jam'iyyar APC ne kuma ko tantama ba'ayi akan Nasarar jam'iyyar APC a yankin da ɗan Jam'iyyar APC dama wanda ba ɗan Jam'iyyar ba zai ce maka Shiyyar Kano ta Arewa, Shiyyar da kowa yake da tabbaci a kanta, Shiyyar da a 2023 ita kaɗai ce Jam'iyyar APC tai Nasara amma Baffa Babba ya fito yake ƙoƙarin raba kawunan Mutane a Shiyyar, yankin da ba nasa ba.

Baffa Babba Ɗan'agundu Maimakon Kalaman tunzuri da katsalandan a cikin siyasar wani yanki daba naka ba zaifi kyau ka koma ka gyara siyasar yankin ka, tun daga matakin akwatu zuwa mazaɓa har zuwa ƙaramar hukumar ka, ina ganin wannan aiki shine yafi maka ba fitowa kana rura wuta a wani yanki daba naka ba, Jam'iyyar APC a Shiyyar Kano ta Arewa zaune take lafiya kuma muna da tabbacin ruɓanya ƙoƙarin ƴaƴan jam'iyyar ta APC akan samun nasarar cin zaɓe a 2027 tun daga sama har ƙasa.

Muna kira ga uwar Jam'iyyar APC ta Jihar Kano da mai girma Gwamna da dukkanin jagororin Jam'iyyar APC na jiha dama ƙasa dasu tsawatarwa da Baffa Babba Ɗan'agundu kan zagon ƙasa da kalaman tunzuri da yakeyi kan siyasar Shiyyar Kano ta Arewa zone ɗin da duk ɗan Jam'iyyar APC yake kiran sa da (GOLDEN ZONE). Sannan su bashi assignment da yakoma yankinsa musamman ma akwatinsa da ƙaramar hukumar sa kada wannan lokacin ma yabamu kunya ya kasa ciwo mana zaɓen su.

Nasarar APC itace a gaban mu.

Hon. Abdullahi Abubakar
Ɗan kishin jam'iyyar APC

Photos from Kano Progressive Media Network's post 20/05/2026

SAMAR DA MOTOCIN SUFURI DA SANATA DAKTA BARAU YAYI YA TAIMAKA WAJEN FITAR DUBUNNAN MUTANE DAGA ƘANGIN TALAUCI.

Sanata Barau I. Jibrin ne kaɗai a duk faɗin Najeriya ya fito da irin wannan tsarin na Taimakon Direbobi da Motocin Sufuri domin su samu hanyar dogaro da kansu.

Abin birgewa an fito da tsarin biyan kaso 40% cikin 100% kowanne dire Sanata Dakta Barau ya biya masa 60% shi kuma direban shine ya biya 40% kuma cikin sauƙi a tsawon shekaru biyu, samar da wannan tsarin ya taimakawa dubunnan Mutane fita daga ƙangin Talauci, ya cire Dubunnan Mutane daga wahalar rayuwa, ya saka Dubunnan iyalai cikin nutsuwa ya cire su daga fargabar rayuwa.

Sanata Barau ne ya cancanci cigaba da tuƙa ragamar Siyasar Kano ta Arewa domin cigaba da kawo mana ayyukan alheri a yankunan mu.

Photos from Kano Progressive Media Network's post 16/05/2026

Bari in tunatar muku!!!

~~Daga Basiru Yusuf Shuwaki

Ko kun san bayan kawo Manyan Jiragen ruwa guda Biyu da Sanata Barau yayi Dam ɗin Bagwai, an kuma yi gine-ginen na ban sha'awa wanda duk wani me zuwa yawon buɗe ido nan gaba kaɗan zai iya zuwa Dam ɗin Ɓagwai domin bawa idonsa abinci, ta yadda ko ƙasar waje kaje kafita wuraren da suke da Manyan Dam da ake shagulgula da shaƙatawa zaka iya zuwa Ɓagwai domin buɗe idon ka.

Ba wannan ne kawai abin jindaɗi da godewa Allah da shi kansa Dsp Barau I. Jibrin ɗin ba, idan kuka tuna a wannan Dam na Ɓagwai a shekarun baya kafin Sanata Barau ya kawowa Al'ummar wannan yanki waɗancan jirage duk kusan shekara Mutane da damane suke rasa ran su ta dalilin yin haɗari ta hanyar faɗawa cikin wannan ruwa musamman hawa ƙananan kwale-kwale da ake amfani dasu wajen sufuri tsakanin garuruwan da s**a shafi sai an haye wannan ruwa kafin aje inda suke.

Cikin bada kariya ta Ubangiji Allahu kamar yadda yace "tashi in taimake ka" DSP. Dakta Barau ya tashi a madadin Al'ummar wannan yanki ya kawo musu waɗannan jirage, tun shekarar da Sanata ya kawo wannan jiragen ruwa ba'a ƙara samun haɗarin jirgin ruwa a wannan yanki ba.

Da wannan dole mu godewa Sanata Barau ta yadda ya taimaki Al'ummar wannan yanki shima Allah ya taimake shi, muna addu'ar Allah ya bashi dama wacce tafi wannan da yake kai domin cigaba da kawowa Al'ummar yankinsa na Kano ta arewa, Kano dama ƙasa baki ɗaya cigaba me ɗorewa.

Al'ummar Kano ta Arewa ayi Dakta Barau da alkairi.

Basiru Yusuf Shuwaki D.G Media

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano