CCN Hausa

CCN Hausa

Share

CCN Hausa – Creative Communication Network Hausa– Za ta dinga kawo muku labarai ingantattu masu kayatarwa.

Muna karbar tallan kasuwanci ko na siyasa. 08035996090 Whatsapp kaɗai, idan har ka san ba talla za ka ba mu ba, don Allah kar ka yi mana magana 🙏

31/05/2026

KA JI RABO: Matashiyar ’yar Najeriya, Hafiza Sumayya, takammala haddace Alƙur’ani mai girma da dukkan riwayoyinsa, tare da manyan littattafan Ilimin Qira’ah kamar Ash-Shatibiyyah, Ad-Durrah da At-Tayyibah.

An yaba da kwarewarta wajen karatu da sauyawa tsakanin qira’o’i daban-daban cikin fasaha da kiyaye ka’idojin tajwidi, lamarin da ya sa mutane da dama ke kallonta a matsayin abin koyi ga masu neman ilimin Alƙur’ani.

Wane irin fata za ku yi musu?

31/05/2026

HOTO: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris (na 2 daga dama a sahu na biyu), yana halartar liyafar shekara-shekara da Yarima Mai Jiran Gado kuma Firayim Ministan ƙasar Saudiyya, Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, ya shirya a madadin Mai Kula da Masallatan Harami Biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, domin tawagogin gwamnatoci da sauran manyan baƙi na musamman da ke gudanar da aikin Hajji na bana.

30/05/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN: Allah ya yi wa wannan bawan mutumin rasuwa bayan hatsarin mota a hanyar Jega zuwa Argungu, Jihar Kebbi. An kai shi Asibitin Tarayya (FMC) Birnin Kebbi domin ceto rayuwarsa, amma ya rasu bayan isa asibitin.

Kafin rasuwarsa ya bayyana cewa shi ɗan Argungu ne, amma ba a samu wata takarda ko lambar waya da za ta taimaka wajen gano iyalansa ba.

Ku tayw mu yaɗa wannan labarin ko za a samu wanda ya san ƴan'uwansa.

Allah ya jikansa ya gafarta masa

30/05/2026

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris (a hagu), tare da Magajin Garin Landan na ƙasar Birtaniya, Sadiq Khan, a cikin wani hoto mai tarihi a Fadar Sarauta da ke Mina, kusa da Makka a ƙasar Saudiyya, a matsayin baƙi na musamman na Yarima mai jiran gado kuma Firayim Ministan Masarautar Saudiyya, Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Rahman Al Saud, bayan kammala aikin Hajjin bana.

29/05/2026

YANZU-YANZU: Wata matashiya mai suna Abigail ta karɓi addinin Musulunci, inda ta sauya sunanta zuwa Khadijatu.

Rahotanni sun ce kafin Musuluntarta, ta kasance mamba a cocin ECWA da ke garinsu. An yi mata addu’ar Allah Ya tabbatar da ita a kan Musulunci tare da ƙara mata imani da shiriya.

Photos from CCN Hausa's post 29/05/2026

DA ƊUMI-ƊUMINSA: 1ran ta kakkaɓo wani jirgin leƙen asiri na Am0rka nau’in MQ-9, tare da harba makaman kariya (interceptor missiles) zuwa wani jirgin yaƙi na F-35 da kuma jirgin leƙen asiri na RQ-4.

Sojojin rundunar juyin juya halin 1ran sun zargi ƙasar Am0rka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tsakanin ɓangarorin biyu, inda s**a yi gargadin cewa duk wata karya yarjejeniyar da Am0rka za ta yi za ta fuskanci martani mai tsauri daga 1ran.

Rahotanni na nuna cewa tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya na ci gaba da ƙaruwa yayin da kowanne ɓangare ke zargin ɗaya da karya yarjejeniyar tsagaita wutar.

Photos from CCN Hausa's post 28/05/2026

NAHCON Ta Shirya Addu’o’i Na Musamman Ga Najeriya A Filin Arafa

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta shirya addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Najeriya a ranar Arafa yayin gudanar da Hajjin 2026.

Shugaban hukumar, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa an shirya addu’ar ne saboda kalubalen tattalin arziki da zamantakewar da kasar ke fuskanta, yana mai kira ga maniyyata su rika sanya Najeriya cikin addu’o’insu.

Addu’ar ta samu halartar malamai, jami’an hukumar, ‘yan majalisa da maniyyata daga Najeriya, inda aka gudanar da ita cikin harsuna daban-daban da s**a hada da Hausa, Turanci da Larabci.

Hukumar ta kuma ce tana ci gaba da kokarin inganta ayyukan Hajji tare da tabbatar da dawowar maniyyata gida cikin tsaro bayan kammala ibadunsu.

Photos from CCN Hausa's post 28/05/2026

ALLAHU AKBAR: Shugaban Ƙasar Côte d’Ivoire, Alassane Ouattara Ya Kwana A Muzdalifah Tare Da Miliyoyin Alhazai A Yayin Gudanar Da Ibadar Aikin Hajji

An hangi Shugaban Ƙasar Côte d’Ivoire, Alassane Ouattara, yana kwana a Muzdalifah tare da miliyoyin Alhazai daga sassa daban-daban na duniya domin cika ɗaya daga cikin muhimman ibadun aikin Hajji.

Lamarin ya sake nuna yadda addinin Musulunci ke tabbatar da daidaito tsakanin mutane, inda mai mulki da talaka ke tsayuwa a matsayi guda wajen bautar Allah Maɗaukakin Sarki.

Alhazai sun gudanar da ibadu cikin tawali’u, addu’o’i da neman rahama da gafarar Allah Ta’alaa a ƙarƙashin sararin samaniya.

27/05/2026

Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai ga Shugaba Tinubu, Abdulaziz Abdulaziz na taya Al'ummar Musulmi Barka da Bikin Babbar Sallah.

Photos from CCN Hausa's post 27/05/2026

GWANIN BURGEWA: Magajin garin New York ta ƙasar Amurka wanda shi ne musulmi na farko da ya taɓa rike muƙamin ya gudanar da idin Salla babba a yau Laraba, inda ya halarci filin sallar yana sanye da wata doguwar rigar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal.

Wane irin fata za ku yi masa?

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


B. U. K Road
Kano
700301