Hadisai zallah

Hadisai zallah

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hadisai zallah, Health/Beauty, Sharada, Kano.

26/01/2022

11-Annabi (s) yana cewa:”Abubuwa biyu sun halakar da mutane,tsoron talauci,da neman suna”.

12-Annabi (s) ya ce: “Abubuwa biyu basa haduwa a musulmi, rowa da mummunan hali”.

13-Annabi (s) ya ce: “Bai yi imani ba,mutumin da ya kasance yana da rowa,ko hassada,ko ragwanci,mumini bai kasance wa mai ragontaka,ko kwadayi,ko kwauro”.

14-Annabi (s) ya ce:”abubuwa 3 darajoji ne,3 kaffarori ne,3 masu halakarwa ne,3 masu tseratarwa ne.

Darajojin su ne:yada sallama,ciyar da abinci,sAllah da dare lokacin da mutane ke bacci.

Kaffarorin su ne:kyautata alwala lokacin sanyi,tafiya dare da rana zuwa masallatai da kiyaye jam’o’i.

Amma 3 masu halakarwa:kwauro abin bi,bin son zuciya,da tinkahon mutum ga kan sa.

Masu tseratarwa kuma:tsoron Allah a asirce da fili,da tsakaitawa a halin yalwa da talauci,da kalmar gaskiya a halin yarda ko fushi”.

15-Annabi (s) ya ce:”abubuwa 3,duk wanda s**a kasance a cikin sa Allah zai aura masa Hurul ini yanda ya so:Hadiye fushi,dauriya kan Takubba saboda Allah da mutumin da ya sami iko kan dukiyar haram sai ya barta saboda Allah”.

26/01/2022

Wadannan wadansu Hadisai ne da muka fitar da su daga littafai mabambanta, domin amfanuwar al’umma. Allah ya amfanar da mu.

1-Manzon Allah (s) ya ce: “yana daga son mutum ga addinin sa, ya so yan uwan sa (na addini)”.

2-Manzon Allah (s) ya ce: “babu abinda za a hada mafi alkairi kamar a hada ilmi da hakuri”.

3-Manzon Allah (s) ya ce: “Hawariyawa sun ce da Annabi Isah (as) :ya mai sanar da alkairi, sanar da mu wane abu ne yafi komai tsanani, sai ya ce :”fushin Allah”, sai s**a ce to dame ake nisantar fushin Allah? sai ya ce :”kar ku yi fushi”, sai s**a ce: to menene tushen fushi ?”sai ya ce:”girman kai,jiji da kai da rena mutane”.

4-An tambayi Manzon Allah (s) me ke tabbatar da imani ga bawa ?”sai ya ce:”abinda ke tabbatar da shi tsantseni,abinda ke fitar da shi kwadayi”.

5-Manzon Allah ya ce:”Babu abinda yafi cancanta a da dadewa a kurkuku kamar harshe”.

6-Annabi (s) ya ce:”babu abinda ke rusa imani kamar kwauro (tsananin rowa)”.

7-Annabi (s) ya ce:”madalla da kyauta kafin bukata, kuma ya ce, ku yi kyauta domin ta na kawar da kullace kullacen zuci”.

8-Annabi (s) ya ce: “wanda ya taimaki fakiri, ya zauna da mutane lafiya, to wannan mumini ne na gaskiya”.

9-Annabi (s) ya ce, abubuwa 2,wanda s**a kasance a cikin sa,in kuwa ba haka ba to tir da su! Yin Sallah a kan lokacin ta da kiyaye ta,da taimako”.

10-Annabi (saww) :”ka so abinda ke wajen Allah, Allah zai so ka,ka ki abinda ke hannun mutane mutane za su so ka”.

Hadisai zallah

26/01/2022

*ISLAMIYA* *DADI* ☪️❤️.
▪️Koka san wanda ya fara harba kibiya a tafarkin Allah shine *Sa'ad* *bin* *abi* *Waqqas* 🏹

▪️Amintaccen Al'ummar Annabi (SAW) shine *Abu* *Ubaidatu* *bn* *Jarrah* 🤝🏼

▪️Annabi (SAW) yace wanda yake so yaga dan aljannah yana yawo a bayan kasa ya kalli *Dalha* *bn* *Ubaidullah* ❤️❤️

▪️Wanda yafi kowa tausayi a alummar Annabi (SAW) shine *Sayyadina* *Abubakar*
😭😭

▪️Wanda yafi kowa tsananin kishin addinin musulinci shine *Sayyadina* *Umar*
😳😳

▪️Wanda yafi kowa tsananin kunya a alummar Annabi (SAW) shine *Sayyadina* *Usman*
🤦🏻‍♂️🤦🏻‍♂️

▪️Wanda yafi kowa sanin hukunci a alummar Annabi (SAW) shine *Sayyadina* *Aliyu*
🙇🏻‍♂️🙇🏻‍♂️

▪️Wanda yafi kowa sanin halal da haram shine *Mu'azu* *bn* *Jabal*
🙇🏻‍♂️🙇🏻‍♂️

▪️Wanda yafi kowa iya karatun Qur'ani shine *Ubayyu* bn *Ka'ab*
👨🏼‍🎓👨🏼‍🎓

▪️Wanda yafi kowa sanin ilimin rabon gado shine *Zaidu* *bn* *Thabit*
👨🏻‍💻👨🏻‍💻

▪️wanda yafi kowa sanin ma'anar ALQUR'ANI shine: *ABDULLAHI BN ABBAS*
📖📖
In kaji dadi tura wa wasu suma suji dadi sukuma qaru

Ya Allah Kayi tsira da rahama ga Annabinmu Muhammad, da iyalansa, da sahabansa, da duk wanda yayi aiki da saqonsa har ya zuwa ranar tashin qiyama AMEEN🤲🏿

HADISAI ZALLAH.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Culinary Team

Attire

Telephone

Website

Address


Sharada
Kano
1111