GSN Hausa

GSN Hausa

Share

Ziyarci GSN Hausa don labarai ingantattu daga Najeriya, Nijar, Kamaru da Ghana, tare da sauran duniya baki daya. Kada ka manta da LIKE da FOLLOW. Mungode!

04/04/2026

Kukan zuci…

Shafuka a kafafan sada zumunta na ta ƙara yawa ma su kira izuwa ‘Hausa zalla’ da wai ‘Bahaushe ya mulki kansa’. Ba hakan ba ne matsala. Da man kowacce ƙabila a Najeriya ta na da na ta ƙungiyoyin irin haka. Matsalar ita ce wasunsu na ta yaɗa gaba da tunzuri tsakanin Hausawa da Fulani. Ko jiya sai da lamarin nan ya hana ni bacci. Amman fa duk lokacin da lamarin ya dame ni, sai kuma na tuna cewa duk waɗannan matsalolin rashin tsaro ya haifar da su. Kuma da man ai a kan tafe kan taras…

Tabbas ba ƙaramar illa a ka yi ma na ba da a ka kasa shawo kan banditry. Waɗanda ya dace su yi abin da ya dace a lokacin da ya dace ba su yi ba. Matsalar babba ce, amman ba ta fi ƙarfin hukomomin tsaron Najeriya musamman idan su ka haɗa kai da jihohi cikin ikhlasi. Sai dai kash…

Bandits har TikTok live su ke yi, kuma da yawan su za su faɗa ma ka cewa su Bahaushe maƙiyinsu ne, ga kuma Hausa villages da su ke raiding. Sun sha su yi video su na lalatawa Hausawa amfanin gona su na dariya. Unfortunately matsala ta ƙi tafiya, har kuma wasu Hausawa su ka fara tunanin matsalar ƙabilanci ce. Yo ko akwai wanda ya taɓa ganin bandits sun yi raiding ruga? Abun babu daɗi. Da gwamnati ta yi abun da ya dace a kan lokaci da ba mu kai ga haka ba. Yanzu ga shi mun zo lokacin da matsalar tsaro da wawayen cikinmu su ka haddasa na neman assasa gaba tsakanin ma su hankalinmu daga Hausawa da Fulani.

Abubuwa ne fa su kai ta faruwa na dabbanci tsawon shekaru kusan goma. Bandits ɗin nan dai ‘yan ƙabilar Fulani ne yawancinsu, su kuma victims yawanci Hausawa. Ƙiri-ƙiri a ka ciwa Sarkin Gobir mutunci kuma a ka kashe shi. Sarki guda fa. Har kuma wai sulhu a ke da bandits a basu kuɗi, su kuma victims ɗin an ƙyale su. Da yawa victims na ganin ƙabilanci ne kawai. Akwai Lokacin da a ka fara maganar yaƙar bandits, har former ES na NHIS ya fito ya yi magana a matsayinsa na Fulani wai ba sa goyon bayan hakan. Hakan ya ƙara ingiza ma su rajin Hausa zalla. Maimakon a samu daidaito da maslaha, sai kuma a ke neman nuna cewa su reactionists ɗin Hausawa su ne wai za su tada fitina. Ga kuma ci mu su mutunci da a ke a na kiransu da maguzawa. Wai har wani na cewa “Mu na zaman lafiyarmu za’a tada ma na rikici”…

To ai shi ya sa victims ɗin ke ganin saboda mu na cikin gata shi ya sa mu ke ganin matsalarsu ba wata matsala ba ce. Da yawanmu za ka ji mun ce mu na tsoron ka da abunda ya afku a Rwanda ya afku, amman fa da yawan ƙauyukan Hausawa a SOKEZA, su sun ga Rwanda tun tuni - an yiwa ‘ya’yansu fya*ɗe a gabansu, an kashe mu su iyaye a gabansu, an kore su daga ƙauye an banka ma sa wuta, an same su a masallaci su na sallah duk an yayyankasu, duk sati ko wata wasunsu sai sun baiwa ‘yan ta’adda haraji. To kuma me ya rage?

Ma su hankali dai sun san cewa abinda ke faruwa da man zai faru. A duk lokacin da wasu mutane daga wata ƙabila su ka fitini wasu mutane daga ƙabila mabambanciya, to fitinar ta kan zama biyu - ga rashin aminci ga kuma hassada gaba tsakanin ƙabilun. Mafitar a ko yaushe ɗaya ce - a tabbatar da tsaro ga kowa da kowa.

Marzuq Ungogo

Photos from GSN Hausa's post 11/02/2026

Me ya ja hankalina game da FasCoin Network?

Ba wai dan mining ne da ake samun kuɗi masu yawa ba… A’a!
Ba kuma saboda an ƙera app ɗin da kyau ba… A’a!

Abin da ya fi ɗaukar hankalina shi ne:

FasCoin ba kawai app na kuɗi ba ne — app ne da aka gina domin al’umma su taimaki juna da yaƙi da zalunci a duniya.

A cikin FasCoin Network, mutum zai iya:
✅ Kai rahoton zalunci a garinsa ko ƙasarsa
✅ Bayar da labarin cin hanci, damfara, fyade, wariyar launin fata, ko cin zarafi
✅ Rahoton zai kasance a bayyane ga jama’a amma ba wanda zai san wanda ya shigar da shi
✅ Ana iya rubuta rahoto da kowane yare — muddin rahoton na gaskiya ne.

Misali: idan an damfare ka, za ka iya shigar da rahoto domin jama’a su yi hattara, sannan kuma FasCoin Network zasu taimaka ma wajen neman maka haƙƙinka.

👉 Duk rahoton da ka shigar, za a baka 50 FasCoin.

Ba Iya haka kaɗai ba — idan kana son samun kudi masu yawa:

⛏️ Claiming 5 FasCoin duk awa 6

📺 Tasks na kallon ads:
• Duk minti 20 = 5 FasCoin
• Duk awa 1 = 8 FasCoin

Wannan app an gina shi ne domin inganta al’umma da dawo da gaskiya a duniya.

👉 Idan kana son buɗe account: duba link ɗin da ke comment section ko ku mana magana ta private
👉 Kar ka manta amfani da referral code ɗinmu:

gsnhausa

Tabbas — Gaskiya tana da daraja!

04/02/2026

Wani Dan Gwagwarmayar Siyasa Kenan Da Yace Ya Kashewa Gomna Abba Kudi Ba Adadi Amma Ya Juya Musu Baya Ya Koma APC.

Photos from GSN Hausa's post 04/02/2026

Labari mai ɗaukar hankali!

Farfesa Isa Ali Pantami, CON, ya sabunta rajistar kasancewarsa memba na jam’iyyar APC a yanzu, inda ya sake jaddada biyayyarsa da ci gaba da jajircewarsa ga hangen nesan jam’iyyar, tare da yin alƙawarin cikakken goyon baya ga gwamnatin APC da ƙoƙarinta na bunƙasa ƙasa, haɗin kai, da shugabanci na ci gaba a Nijeriya.

02/02/2026

RAYUWA KENAN! Innalillahi wa Inna ilaihi raaji'un!

Allah Ya yi wa shahararren malamin addinin Muslunci, Sheikh Usman Kusfa Zariya, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi, rasuwa a daren ranar Lahadi 1 ga Fuburairun 2026, kamar yadda majiyoyi na kusa da ahalin s**a tabbatar.

Sheikh Usman Kusfa, wanda ya shahara a kafafen sada zumunta saboda salon wa’azinsa, ana sa ran za a gudanar da jana’izarsa a yau Litinin, a gidansa da ke Zariya.

Photos from GSN Hausa's post 26/01/2026

Har Yanzu Ana Ta Shirin Tarbar Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf zuwa Jam'iyyar APC inda Aka Haka Ganduje Ya Sauka A Jirgi Domin Halartar Wannan Taro.

25/01/2026

Kurunkus! Gwamna Abba Kabir Yusuf zai shiga APC gobe Litinin, 26/01/2026 — in ji Sunusi Bature Dawakin Tofa.

An tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai sauya sheka zuwa jam’iyyar APC gobe Litinin, 26 ga Janairu, 2026.

Wannan bayani ya fito ne daga Babban Daraktan Yada Labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya bayyana cewa dukkan shirye-shiryen sauyin jam’iyyar sun kammala.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na Gwamna Abba na iya sauya yanayin siyasar Kano, tare da haifar da sabbin sauye-sauye a tafiyar jam’iyyun siyasa a jihar da ma kasa baki ɗaya.

Ana sa ran manyan jiga-jigan APC da sauran masu ruwa da tsaki za su halarci taron karɓar Gwamnan a hukumance.

25/01/2026

Me Kuka Fahimta A Wannan Bidiyon?

24/01/2026

An tsinci jariri sabuwar haihuwa a Tudun Murtala, Kano — lamarin ya tayar da hankalin jama’a.

An tsinci jariri sabuwar haihuwa a safiyar yau a yankin Tudun Murtala, kusa da makabarta da ke cikin birnin Kano.

Wata mazauniyar yankin, Ummulkhair Ayuba Musa, ta shaida wa Freedom Radio Nigeria cewa sun wayi gari da ganin wani abu a nannade cikin leda a gefen makabartar. Bayan an duba abin, sai aka gano jariri ne mace, sabuwar haihuwa.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a yi mata cikakken kulawar haihuwa ba, lamarin da ya nuna jaririyar ta zo duniya ne a cikin yanayi mai tayar da hankali.

A halin yanzu, ana sa ran za a yi mata sallah a binne ta kamar yadda addini ya tanada.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Tudun Wada, Nassarawa
Kano
700282