Hausa Motivation
Shafin da ke kawo maku saƙonnin ƙarfafa gwiwa, hikimomi da tarihin malaman falsafa da kuma darussa akan rayuwa.
Ku kasance tare da mu domin inganta rayuwarku a kullum.
24/12/2025
Kuma ka sani: duk dariya ɗaya da ka yi, akwai wasu dubban a can suna kuka a cikin rayuwa.
Amma hukuncin Ubangiji dukkaninsa adalci ne da hikima, babu zalunci ko rashin daidai a cikin sa.
22/12/2025
Ya Ubangiji! Ka nuna mana gaskiya gaskiya ce kuma ka ba mu ikon bin ta.
Sannan ka nuna mana ƙarya ƙarya ce kuma ka ba mu ikon guje mata.
20/12/2025
Rayuwa tana da matuƙar sauƙi.
Amma ga mutumin da ya fahimta.
19/12/2025
Babban haɗarin tsoro shi ne ba ya taɓa gangan jiki amma yana ɗaure zuciya. Shi matsoraci ya kan sha ƙasa ne tun faɗan ma bai fara ba.
Ba'a san maza da ja da baya ba. Don haka ka yi iya bakin yin ka ɗan uwa, abin da ya fi ƙarfinka ka zuba wa sarautar Allah ido.
Kuma ka tuna cewa matsoraci ba ya zama gwani.
18/12/2025
Wa ya ba ka tabbacin gobe?
Idan yau kana da lafiya, wa ya gaya maka gobe kana da lafiya?
Idan yau kana da lokaci wa ya gaya maka a gobe zaka samu lokaci?
Duk abin da ya cancanta ka aikata kawai ka fara aikata shi nan take, kada ka jira wani lokaci na musamman.
Idan damar nan ta kuɓuce maka ba lallai ka sake samun irin ta a nan gaba.
18/12/2025
Idan ka dogara ga uzuri ba zaka taɓa samun abin da kake so ba a rayuwa.
Mutane na fara kasuwanci babu jari, gajiyayyu na koyon sana'a, makafi na haddace Kur'ani, matasa na ɗaukar nauyin karatunsu na jami'a.
Almajirai suna neman ilimi cikin fatara da talauci, marayu na samun ɗaukaka, kuma masu laifi suna tuba Allah Ya karɓe su.
Don haka ba ka da kowane uzuri. Idan da gaske kake zaka doge akan manufarka komai wahala.
Uzuri da kalubale ba sa kan hana nasara kamar yadda rashin ƙudiri, jajircewa da rashin haƙuri suke hanawa.
Rayuwa ta gwada ni ta hanyar da ba zan iya kaucewa ba. Wata shida baya zuwa yanzu, an ɗora mun wani babban nauyi a wurin aiki da ya mamaye lokacina gaba-ɗaya.
Don haka na ɗauki hutu daga wallafa saƙonnin faɗakarwa a wannan shafin. Ina miƙa godiya ta ga waɗanda s**a aiko saƙonnin bibiya, da addu'a da fatan alkairi.
Allah Ya saka da alkairi, Allah Ya bar zumunci. Ba zan iya amsa duka saƙƙoninku amma na ji daɗi sosai kuma ina matuƙar godiya.
Zamu ɗora daga inda muka kwana In Allah Ya so. Ku cigaba da kasancewa tare da mu domin inganta rayuwarku a kullum.
Fatan alkairi gare ku!
04/07/2025
Kowane mutum za iya canza rayuwarsa idan ya iya canza mahangarsa game da rayuwa.
03/07/2025
Sarewa zaɓi ne kamar yadda shima dagewa zaɓi ne. Duk yadda zaka wahala wurin neman abin da kake so kada ka taɓa hakura.
Babu wani abu mai daraja da ya ke samuwa da sauki. Ka yi haƙuri ka cije domin tabbas watarana sai labari!
02/07/2025
Kowace gazawa tana ƙara kusantar da kai ne ga nasara. Ka cigaba da gwadawa domin duk wanda bai yi rarrafe ba ba ya taɓa koyon tafiya.
01/07/2025
Komai a rayuwa akwai lokacinsa kuma akwai bigirensa. Don haka kada ka ruɗu da gaggawa.
Ka bi rayuwa a sannu sannan ka yi abin da ya dace a lokacin da ya dace.
30/06/2025
Gani ga wani ya ishi wani tsoron Allah domin duniya makaranta ce, kuma ko ba magana a zura ido ya ishi mai hankali.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano