Sharp Reporters Hausa

Sharp Reporters Hausa

Share

Sharp Reporters Hausa sabuwar kafar watsa labaru ce ta hanyar kafafen sadarwar zamani wanda ta kudur

17/03/2023

Hello

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 20/09/2022

Hotuna surukar shugaban ƙasa, ɗiyar Sarkin Bichi, jikar marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, Zahra Nasiru Ado Bayero, yayin da ta kammala digiri a wata jami'a dake ƙasar Birtaniya

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 19/09/2022

Waɗannan hotunan suna nuna yadda gidan Turji ya koma bayan Sojoji sun ƙaddamar masa da hari. Babu labari game da takamaimen halin da yake ciki zuwa yanzu.

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 19/09/2022

Anan, ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji ne yake shawagi a harabar gidansa dake ƙauyen Fakai, jihar Zamfara, kafin Sojoji su ƙaddamar da hari a gidan.

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 13/09/2022

Kalli halin da Sojojin Najeriya s**a tarar da wasu mutane a sansanin ƴan bindiga bayan ƴan bindigan sun yi garkuwa dasu a jihar Kaduna.

Mutanen sun haɗa da:
- Surajo Aliyu
- Ayuba Yakubu
- Ibrahim Abdulrasheed
- Aliyu Mohammed
- Magaji Tasiu
- Nasiru Ahmed
- Mohammadu lbrahim
- Ayuba Abdulsalam
- Kelvin Musa
- Paul Patrick

Amma tuni Sojojin s**a kuɓutar dasu bayan sun karkashe ƴan ta'addan.

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 12/09/2022

(TALLA)

Allah Ya kawo mu sabon mako, a yau ma na zo muku da wanda ni Petra Akinti Onyebule na ƙirƙireshi domin sanar daku al'amuran da s**a shafi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC tare da abokin takararsa, a kowanne mako, a duk ranar Lahadi.

Kamar yadda kuka sani, maƙasudin shi ne kawar da duk wasu gutsuri tsoma da ƙarairayi game shige da ficen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da tabbatar da bamu baiwa duk wasu masu nufinsa da sharri daman kitsawa da yaɗa ƙarairayi akansa ba.

A ranar Lahadi, 4 ga watan Satumbar 2022, ɗan takarar jam'iyyar APC a matakin shugabancin ƙasa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya tarbi manyan baƙi a gidansa dake Asokoro, Abuja, da s**a haɗa da tsofaffin gwamnonin jihohin Yobe da Abia, watau Sanata Ibrahim Gaidam da Sanata Orji Uzor Kalu.

Sai kuma ranar Litinin, 5 ga watan Satumbar 2022, inda jakadiyar haɗaɗɗiyar daular Birtaniya a Najeriya, Catorina Lian tare da ƴan rakiyarta s**a ziyarce shi a ofishin yaƙin neman zaɓensa dake Abuja. Catorina ta kai masa wannan ziyara ne domin tattauna manufofin ƙasar Birtaniya ga Najeriya bayan zaɓen 2023.

A ranar Talata, 6 ga watan Satumbar 2022 kuwa, Tinubun ne tare da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima da shugaban yaƙin neman zaɓensa, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar ne s**a gana da shuwbagabannin jam'iyyar APC a sakatariyar jam'iyyar dake Abuja. A yayin ganawar, cikin ƙuzari da ƙwarewa wajen salon magana da nuna sanin makaman aiki, Tinubu ya bayyana manufofinsa tare nanata yaƙininsa na APC za ta lashe zaɓukan 2023.

Har wa yau, a ranar Talatan, ɗan takarar shugabancin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu rakiyar abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima, shugaban yaƙin neman zaɓensa, Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu, shugabar mata ta jam'iyyar, Dakta Betta Edu, Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa, mataimakinsa, Umar Namadi Danmodi, mataimakin shugaban APC na ƙasa shiyyar kudu, Emma Nnekwu da tsohon shugaban EFCC, Malam Nuhu Ribaɗu sun kai ziyarar jajantawa jihar Jigawa bisa ambaliyan ruwa da aka samu wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 51 tare da lalata kadarori da dama.

Sai kuma ranar Juma'a, 9 ga watan Satumbar 2022 inda Asiwaju Tinubu tare da abokin takararsa Kashim Shettima, da Kaakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da wasu jagororin yaƙin neman zaɓensa s**a gudanar da sallar Juma'a a masallacin Sanusi Ɗantata dake Abuja.

Bugu da ƙari, Tinubu da Shettima sun karɓi baƙoncin ƙungiyar manoma masu goyon bayan Asiwaju daga shiyyoyi shidda na Najeriya a ofishin yaƙin neman zaɓensa dake Abuja. A jawabinsa yayin ganawar, Tinubu ya yi alƙawarin kashe maƙudan kuɗaɗe a harkar noma tare da sarrafa amfanin gona domin tabbatar da samun ƙarin isashshen abinci a Najeriya.

Kamar yadda na saba, ba zan ƙarƙare ba sai na nanata muhimmancin kyakkyawar alaƙa da fahimtar juna dake tsakanin BAT da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima. Su kaɗai ne a yanzu za a iya cewa tabbas abokan takara ne, kuma hakan abin a yaba ne.

Ku kasance tare da ni a mako mai zuwa don cigaban . Na barku lafiya.

12/09/2022

Haɗuwar marigayi Shehu Shagari da marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth

Shehu Shagari ya ce "yayin da mu ka hau keken doki tare da sarauniyar Ingila, an taru ana ta mana tafi, sai kawai na ji an kwala min kira, ana cewa "Malam Shehu! Malam Shehu!!

Da na duba sai na ga ashe wani Bature ne, tsohon D.O da ya taɓa aiki a Sakkwato, na tuna na taɓa rokarsa aron keke, ya hana ni ƙememe!

A zuciya ta na ce "da ka hana ni keke, ai yau ga shi na hau keken uwarka" 🤣🤣

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 12/09/2022

Yadda aka gudanar da kasafin kudin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayar a jihar Kano Naira Million 10 ga ƴan kasuwan da ibtila'in ambiyan ruwa ya faɗa mawa a kasuwar Beirut road.

10/07/2022

Ƙarshen tika tika tik!

Ɗan takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya zaɓi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 09/07/2022

Babbar Sallah

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli kenan tare da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da Sanata Uba Sani yayin sallar Idi a Zaria.

Barkanmu da Sallah
Da fatan Allah Ya karba mana.

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 09/07/2022

Babbar Sallah

Mai Martaba Muhammadu Sanusi II ya halarci sallar Idi a Masallacin Portsmouth Jami mosque and Islamic centre dake kasar Ingila.

Barkanmu da Sallah
Da fatan Allah Ya maimaita mana

Photos from Sharp Reporters Hausa's post 09/07/2022

Babbar Sallah

Sallar Idi kenan kamar yadda ya gudana a Masallacin Annabi dake Madina. Wanda Sheikh Thubaity ya jagoranta.

Barkanmu da Sallah
Da fatan Allah Ya karɓa mana.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Kaduna