Labaran Wasanni

Labaran  Wasanni

Share

Muna kawo muku labaran Wasanni zafafa a cikin harshen Hausa

10/09/2022

Matashin dan wasan tsakiyar Barçelona wato Gavi zai tsawaita kwantiragin da kungiyar Barçelona. Bayan dogon tat'taunawa da aka dauka anayi tsakanin dan wasan da kungiyar a karshe sanya hannu a sabon kwantaragin yazo karshe.

Duk da kasancewar akwai wasu rade redin cewa wasu kungiyoyi suna neman dan wasan, amma Barçelona nada kwarin guiwar dan yanzu lokaci ne kawai ya rage.

10/09/2022

Joe Felix ya shaidawa jaridar Marca akan alakantashi da Manchester United da akayi kafin a rufe kasuwar musanye yan wasa.

Felix yace shi baitaba jin labari cewa Manchester United suna nemansa ba, sabida hakan yana hannun shugaban kungiyar ne.

Basu taba kawo wani tayi a hukumance ba, kawai dae sun so sunemi dan wasanne, sai dai Athletico Madrid bazasu saida shi ba.

10/09/2022

Anya bata karewa Crisitiano Ronaldo ba kuwa?

10/09/2022

Hector Bellarin ya rage Albashin sa da kaso mai yawa dan yakoma Barçelona a ranar karshe da aka rufe kasuwar musanye yan wasa.

Dan wasan yayi watsi da tayin wasu kungiyoyi biyu daga kasar Italiya dan ya koma Barçelona.

A yau dan wasan zai fara taka leda a matsayin sabon dan wasan Barçelona.

Photos from Labaran  Wasanni's post 10/09/2022

MANYAN WASANNI YAU DA DAN KARAMIN SHARHI AKANSU!!

1. PSG VS Breast 4:00pm
2. Marseille vs Lille 8:00pm
3. Bayern Munich vs Stuggart 2:30pm
4. Leipzig vs Dourtmund 2:00pm
5. Napoli vs Spezia 2:00pm
6. Inter Milan vs Torino 5:00pm
7. Sampdoria vs Ac Milan 5:00pm
8. Cadiz vs Barcelona 5:30pm
Athletico Madrid vs Celta Vigo 8:00pm.

Bayan mutuwar Sarauniyar England Queen Elizabeth babu gasar Primier League a wanna makon. To amma zamu kalla sauran gasar.

Gasar Ligue 1.

Kwallon ƙafa a yanzu tana iya bada mamaki, amma duk da haka zamu iya cewa kwallaye nawa Psg zasu zuba? Zamu gani. Marsielle da Lille suna taka leda mai kyau a yanzu bari muga yadda wasan zai kasance.

Gasar Bundesliga!

Muna tsammanin sakamako mai girma daga Bayern Munich, haka zalika Dourtmund suna da katon aiki a gabansu.

Gasar Seria A

Napoli, Inter da Ac Milan duk zasu buga wasa a yau. Fafutukar neman zama a matsayi na daya a teburin gasar zaici gaba da wakana. Zamu iya cewa yanzu gasar Seria A shine gasa mafi wahala a duniya.

Gasar La Liga.

Muna fatan ganin karin kwallaye daga Lewandowski. Ga Athletico Madrid kuma muna fatan ganin Greizman a mintuna na 60 kamar yadda yayi a satin da ya gabata.

Ku kasance damu...

10/09/2022

Sarki da kuma tsohuwar sarauniya

Magoya bayan Arsenal ne kaɗai zasu fahimta

10/09/2022

Matashin dan wasan Napoli wato Giovanni Simeone yayi zanen tambarin Champions league a hannunsa tun yana dan shekara 14 a duniya.

A ranar laraba da ta gabata dan wasan yafara buga gasar Champions league a karo na farko a tarihin rayuwarsa a wasan da Napoli ta doke Liverpool daci 4-1.

Taban kwallo na farko da matashin dan wasan yayi sai a ragar Liverpool. Wannan dalilin yasa ya sumbaci zanen tambarin Champions league dake hannunsa sannan ya fashe da kuka domin mafarkinksa ya cika.

10/09/2022

Haryanzu Cristiano Ronaldo da Lionel Mess suke jan ragamar wadanda sukafi taimakawa aci kwallo a gasar nahiyar turai.

Ronaldo shine na daya a yawan taimakawa aci kwallo a gasar Champions league, Inda Messi yake biye masa a mataki na biyu.

Sai dai kasancewar Ronaldo baya buga Champions league a wannn shekarar ko Messi zai iya kamo Ronaldo?

Ga jerin masu yawan Asists a gasar Champions league.

1. C. Ronaldo 42
2. Lionel Messi 36
3. Angel Di Maria 35
4. Neymar 31
5. Ryan Giggs 31
6. Xavi Hernandez 30
7. Andres Iniesta 29
8. Karim Benzema 28
9. Thomas Muller 27
10. Cecs Fabregas

Photos from Labaran  Wasanni's post 09/09/2022

Hotunan atisayen yan wasan Barçelona a yau

09/09/2022

Haryanzu Crisitino Ronaldo baici kwallo ko yataimaka anci ba a wannan kakar wasan.

Ko dai takarewa Ronaldo ne?

09/09/2022

Bajintar sabon Kocin Chelsea.

Ya jagoranci wasanni 120.

Yayi nasara 34 aciki wasanni 120.

Yayi kunne doki sau 44 acikin wasanni 120..

Yayi rashin nasara sau 42 acikin wasanni 120.

Kuna ganin ya cancanci zama Kocin Chelsea?

09/09/2022

Wadannan sune yan wasan da Messi yayiwa Asist sukaci kwallo.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Plateau
Kaduna