Unity Media
Unity Media | Home of Unity Radio 93.3 FM, Unity TV, Unity eHub, Unity Media Academy & Unity Futsal. Voice of Reason - Promoting peace and unity.
05/06/2026
Sarkin Argungu, Alhaji Muhammad Samaila Mera, ya buƙaci al’ummomin masarautarsa da su mallaki makamai bisa ka’ida domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da ke addabar yankin.
Sarkin ya kuma yi kira ga al’ummomin masarautar da su kasance cikin shiri tare da ɗaukar matakan kariya daga ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka da ke kai hare-hare a yankunansu.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da hakimai, masu unguwanni da shugabannin gundumomi da aka gudanar a fadarsa da ke Argungu, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Alhaji Samaila Mera ya ce ya kamata al’umma su haɗa kai wajen tara kuɗaɗe domin sayen makaman da doka ta amince da su domin kare kansu.
A cewarsa, “Idan kuka mallaki irin waɗannan makamai bisa doka, ’yan bindiga zasu san cewa al’ummarku na da damar kare kanta. Wannan kaɗai na iya hana su kusantar yankin.”
05/06/2026
Allah ya yi wa Malam Sadik Pharmacy Gombe rasuwa, bayan fama da jinya da ya yi.
Al'ummar Musulmi, musamman daga Arewacin Najeriya, sun shiga alhini bayan samun labarin rasuwar marigayin, wanda ya kasance matashin malamin addinin Musulunci, tare da kwarewa a fannin magungunan Musulunci da kuma bayar da shawarwari kan gyaran zamantakewar iyali.
Ubangiji, Allah Ya gafarta mi shi.
05/06/2026
🎙️ UNITY MUSIC RADAR PREMIERES THIS SATURDAY ON UNITY RADIO 93.3 FM! 🎶
Unity Radio 93.3 FM – The Voice of Reason proudly brings you the debut edition of Unity Music Radar.
Join us as we welcome our first-ever guest artist, SnowFlexxy, for an exclusive interview and music showcase.
🎤 Hosted by King DJ Mask DJ MASK
📅 Saturday
⏰ 5:30 PM – 6:30 PM
📻 Live on Unity Radio 93.3 FM
Unity Music Radar
Tracking Talent. Spotting Trends.
🎵 Discover Talent. Follow Trends. Celebrate Music.
04/06/2026
Senate commences constitutional process for the establishment of state policing in the Country
The Senate has commenced the constitutional process for the establishment of state police as part of efforts to tackle rising insecurity across the country.
Chairman of the Senate Committee on Media and Public Affairs, Yemi Adaramodu, said lawmakers are ready to fast-track the necessary legislation to support President Bola Tinubu’s security agenda and strengthen the nation’s security architecture.
The move follows renewed concerns over banditry and kidnappings, including the recent abduction of pupils and teachers in Oyo State, which has intensified calls for decentralised policing.
04/06/2026
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani mutum mai shekaru 38, Nsikak Kingsley, bisa zargin dukan mahaifinsa har lahira a yankin Oda da ke karamar hukumar Akure ta kudu a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abayomi Jimoh ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne bayan wata gardama tsakanin wanda ake zargin da mahaifinsa, Adone Peter mai shekaru 65, wacce ta rikiɗe zuwa fada.
Binciken farko ya nuna cewa a ranar 28 ga watan Mayun 2026, Kingsley ya kai wa mahaifinsa hari tare da yi masa munanan raunuka, musamman a kai.
Daga bisani an garzaya da wanda abin ya shafa asibiti domin samun kulawar likitoci. Sai dai duk da kokarin ceto rayuwarsa da ma’aikatan lafiya s**a yi, likita ya tabbatar da mutuwar tsohon yayin da ake masa magani.
SHIRIN MURYAR JAMA'A KASHI NA BIYU 👇👇👇👇👇
https://youtu.be/X7kUzQLOh6E?si=K1dW0EaNwbAKOg_x
04/06/2026
CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA!
Ana cikiyar wannan baiwar Allah mai suna FATIMA IBRAHIM wacce ake kira da UMMI, wacce ta ɓata tun kwanaki 2 da s**a gabata.
Fatima dai ƴar kimanin shekaru 10 ce, sannan ta fita ne daga gidan su dake Anguwan Rogo bayan jeji a nan Jos sanye da doguwar rigar less mai launin “golden”.
Mai ɗan matsakaicin tsayi da jiki ce.
Idan Allah Ya sa wani ya ganta ko ya ji labarin inda FATIMA ta ke, a dubi girman Allah a tuntuɓi wannan lambar: 07015898279.
A taya mu da tura wannan saƙo har ko da Allah zai sa saƙon ya isa inda Fatima ta ke.
Mun gode.
04/06/2026
News for Thursday 4th June, 2026. (18th Zul Hijjah, 1447AH)
04/06/2026
Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai shida na Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda a Jihar Zamfara, bayan sun kai hari gidan da ɗaliban ke zaune a wajen harabar makarantar da sanyin safiyar Laraba.
Rahotanni sun nuna cewa mutum bakwai ne aka fara sacewa, amma ɗaya daga cikinsu ya tsere, lamarin da ya bar maza uku da mata uku a hannun masu garkuwar.
Rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami'an tsaro tare da dakarun Operation Fansan Yamma sun fara aikin ceto wadanda aka sace, a cewar Trust .
YAYA KU KE GANIN MAKOMAR KARATUN ƊALIBAI, MUSAMMAN WANDA SUKE MAKARANTUN KWANA?
04/06/2026
Aƙalla ɗalibai da malamai 603 ne aka yi garkuwa da su a hare-hare bakwai da aka kai wa makarantu a jihohi daban-daban na Najeriya tsakanin watan Maris na shekarar 2024 zuwa Mayun 2026.
CIKIN SHEKARU BIYU: ƊALIBAI DA MALAMAI SAMA DA 600 AKA SACE DUK DA SHIRIN TSARON MAKARANTU NA NAIRA BILIYAN 145 Rahotanni sun nuna cewa aƙalla ɗalibai da malamai 603 ne aka yi garkuwa da su a hare-hare bakwai da aka kai wa makarantu a jihohi daban-daban na Najeriya tsakanin watan Maris na shekarar 2024 zuwa Mayun 2026. Wannan na zuwa ne duk da aiwatar da shirin “Safe Schools Initiative” na gwamnatin tar...
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the business
Telephone
Website
Address
No 62, Zinaria Hill Layout Jos, Plateau State
Jos