Haske Support Foundation

Haske Support Foundation

Share

The Organization was founded by our able mother, mother of motherless, a Uwar Marayu Haj. Maryam

Photos from Haske Support Foundation's post 18/06/2026

HASKE SUPPORT FOUNDATION CONDUCTS AWARENESS AND EMPOWERMENT OUTREACH IN YAKANAJI COMMUNITY, JOS

As part of its continued commitment to community development and humanitarian service, Haske Support Foundation, under the leadership of Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu), carried out an awareness and empowerment outreach program in Yakanaji Community, Jos.

The outreach brought together mothers and adolescent girls for an interactive session focused on personal hygiene, menstrual health management, and the importance of self-care. The program aimed to equip participants with practical knowledge and guidance that would enable them to maintain healthy lifestyles and make informed decisions regarding their well-being.

Mothers were educated on the vital role they play in nurturing children with strong moral values, discipline, and good character. Young girls were also sensitized on menstrual hygiene, body care, self-respect, and the importance of protecting their dignity and future aspirations.

As part of the support provided, sanitary pads were distributed to young girls to promote proper menstrual hygiene and help them manage their monthly cycles with confidence and dignity. In addition, selected mothers received food items to support their households and encourage resilience in the face of economic challenges.

This outreach further demonstrates the unwavering dedication of Haske Support Foundation to improving the lives of women, children, orphans, widows, and vulnerable members of society. The Foundation remains actively engaged in various humanitarian initiatives, including educational support, payment of school fees for orphans and underprivileged children, distribution of learning materials, and community empowerment programs.

We pray that Almighty Allah continues to bless Haske Support Foundation and its leadership with wisdom, strength, good health, and the resources required to sustain these impactful humanitarian efforts for the benefit of humanity.

Signed:
Haske Support Foundation
17th June, 2026

Photos from Haske Support Foundation's post 17/06/2026

Gidauniyar Haske Support Foundation ƙarƙashin jagorancin Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu) ta kai ziyarar wayar da kai zuwa ƙauyen Yakanaji da ke cikin garin Jos, inda ta gudanar da wani muhimmin taro na musamman ga iyaye mata da ‘yan mata domin ilmantar da su kan yadda za su kula da kansu, musamman a lokacin al’ada.

Taron ya mayar da hankali ne kan wayar da kan iyaye mata game da muhimmancin tarbiyyar yara cikin nagarta da kyawawan ɗabi’u, tare da ilmantar da ‘yan mata masu tasowa kan tsaftar jiki, kula da lafiyar al’ada, da kuma hanyoyin kare mutunci da martabarsu a cikin al’umma.

A yayin taron, gidauniyar Haske ta jaddada muhimmancin rayuwa mai tsafta, tarbiyya nagari, da gina al’umma da kwanciyar hankali. Mahalarta taron sun samu shawarwari da nasihohi masu amfani da za su taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da ta iyalansu.

A wani ɓangare na tallafin da gidauniyar ta rabawa ‘yan mata audugar tsaftar al’ada (pads) domin tallafa musu wajen kula da lafiyarsu da tsaftar jikinsu. Haka kuma, an bai wa wasu daga cikin iyaye mata kayan abinci a matsayin tallafi da ƙarfafa gwiwa.

Wannan shiri ya sake nuna irin jajircewar Haske Support Foundation wajen inganta rayuwar al’umma, musamman mata, yara, marayu, da marasa galihu. Gidauniyar na ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi ta hanyar bayar da tallafin karatu, biyan kuɗaɗen makaranta ga marayu da marasa ƙarfi, da kuma rabon kayan karatu ga ɗalibai masu buƙata.

Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya albarkaci gidauniyar Haske Support Foundation da shugabanninta, Ya ƙara musu lafiya, hikima, da ikon ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi domin amfanin al’ummah








Signed:
Haske Support Foundation
17th May, 2026

Photos from Haske Support Foundation's post 16/06/2026

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI 1448 HIJIRA: SHEKARA MAI CIKIN FATAN ALHERI, ZAMAN LAFIYA DA RAHAMAR ALLAH

Hajiya Maryam Shehu Nabage, wacce aka fi sani da Uwar Marayu, cikin farin ciki tana miƙa gaisuwa ta musamman ga dukkan al’ummar Musulmi a wannan albarkatacciyar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1448 Hijira.

Wannan sabuwar shekarar Hijira ta 1448 tana ɗauke da wata babbar dama ta tunani, sabunta imani, da ƙara jajircewa wajen bin tafarkin gaskiya. Tana kara tunatar da mu tarihin hijirar Annabi Muhammad (SAW), wadda ke nuni da sadaukarwa, haƙuri, jarunta, da dogaro da rahamar Allah Madaukaki (SWT).

Ta yi addu’ar Allah yasa wannan sabuwar shekara ta ta kawo ƙarshen ta’addanci a Najeriya, ta zama shekarar zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaba mai ɗorewa ga iyalanmu, al’ummominmu, da ƙasa baki ɗaya. Allah (SWT) Ya kawar da dukkan wahalhalu da matsalolin tsaro, Ya ƙarfafa haɗin kanmu, Ya kuma azurta mu da fahimta, tausayi, da zaman lafiya a tsakanin dukkan mutane ba tare da la’akari da addini, kabila ko yanki ba. Ya Allah Ka sanya ƙasarmu ta zauna lafiya cikin aminci da albarka.

Uwar Marayu ta ƙara ƙarfafa mutane da su ci gaba da tallafa wa ayyukan jinƙai, musamman kulawa da marayu, zawarawa, da marasa ƙarfi. Ta jaddada cewa ayyukan alkhairi da sadaka suna da matuƙar muhimmanci wajen inganta al’umma da kuma samun ladar Allah.

Ta hanyar gidauniyar ta Haske Support Foundation, ta sake jaddada cikakkiyar ƙudirinta wajen hidimar jinƙai, ƙarfafa al’umma, da tallafa wa iyalai marasa ƙarfi domin su samu dogaro da kai da mutunci.

Allah Ya sa wannan Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1448 Hijrah ta buɗe ƙofofin albarka, gafara, shiriya, da zaman lafiya mai ɗorewa ga kowa.

Barka da Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1448 Hijrah.

Signed:
Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu)
CEO/Founder, Haske Support Foundation

16/06/2026

WELCOME TO ISLAMIC NEW YEAR 1448 HIJRAH: A YEAR OF HOPE, PEACE, AND DIVINE MERCY

Hajiya Maryam Shehu Nabage, popularly known as Uwar Marayu, Joyfully extends her heartfelt greetings to the entire Muslim Ummah on the blessed occasion of the Islamic New Year 1448 Hijrah.

This new Hijrah year 1448 marks another divine opportunity for reflection, renewal of faith, and recommitment to righteousness. It reminds us of the historic migration of Prophet Muhammad (SAW), which symbolizes sacrifice, patience, courage, and total reliance on the mercy of Almighty Allah (SWT).

She prays that this new year brings peace, stability, and progress to our families, communities, and the nation at large. May Allah (SWT) remove hardship, strengthen our unity, and bless us with understanding, compassion, and harmony among all people regardless of religion or ethnicity.

Uwar Marayu further encourages everyone to continue supporting humanitarian causes, especially the care of orphans, widows, and the less privileged. She emphasizes that acts of kindness and charity remain a powerful means of transforming society and earning Allah’s reward.

Through her foundation, Haske Support Foundation, she reaffirms her unwavering commitment to humanitarian service, empowerment, and uplifting vulnerable families toward self-reliance and dignity.

May this Islamic New Year 1448H open doors of blessings, forgiveness, guidance, and lasting peace for all.

Happy Islamic New Year 1448 HIJRAH

Signed:
Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu)
CEO/Founder, Haske Support Foundation

13/06/2026

KIRA NA MUSAMMAN DAGA UWAR MARAYU, SHUGABAR HASKE SUPPORT FOUNDATION (PART 2)

A madadin Gidauniyar Haske Support Foundation da al’ummar unguwarmu baki ɗaya, ni Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu) ina kira ga Gwamnatin Jihar Plateau, Sanatan da ke wakiltar Plateau ta Arewa, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bassa/Jos North, Shugaban Karamar Hukumar Jos North, Dan Majalisar Jihar Plateau mai wakiltar Jos North, Kwamishinan Ayyuka da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar mataki kan mummunar lalacewar hanyar Tudun O.C. da ke cikin garin Jos.

Wannan hanya ta lalace matuƙa, lamarin da ke jawo hatsarori, cunkoso da kuma asarar rayuka da dukiyoyi akai-akai. Mazauna yankin, masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar na fuskantar matsaloli masu yawa a kullum sakamakon wannan lalacewa.

12/06/2026

BARKA DA RANAR DIMOKIRADIYYA 🇳🇬

A yau muna murnar Ranar Dimokiradiyya a Najeriya, Ina taya daukacin ‘yan kasa murna da fatan alheri. Wannan rana tana tunatar da mu muhimmancin ‘yanci, hadin kai, da kuma dimokiradiyya mai dorewa wadda ke ginuwa kan gaskiya da adalci.

A lokaci guda, muna tuna da ‘yan uwanmu da s**a rasa rayukansu sakamakon tashin hankali, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro da ke addabar kasarmu. Muna rokon Allah Ya ji kan wadanda s**a rasu, Ya kuma bai wa iyalansu hakuri da juriya.

Ina kira ga shugabanni da su kara himma wajen inganta tsaro, walwala, da jin dadin al’umma domin dimokiradiyya ta yi amfani ga kowa.

Allah Ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a Najeriya, Ya kuma kara mana hadin kai da cigaba.

Signed:
Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu)
Shugabar Haske Support Foundation

12/06/2026

HAPPY DEMOCRACY DAY 🇳🇬

As we celebrate Democracy Day, I extend my warm greetings to all Nigerians. let us remember the victims of killings, banditry, kidnapping, and other challenges facing our nation. True democracy can only thrive where there is peace, security, and justice for all.

I pray for a safer, united, and more prosperous Nigeria, and I call on our leaders to prioritize the welfare and protection of the people.

May Almighty Allah grant peace to our land and bless the Federal Republic of Nigeria.

Signed:
Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu)
CEO/Founder Haske Support Foundation

11/06/2026

KIRA NA MUSAMMAN DAGA UWAR MARAYU, SHUGABAR HASKE SUPPORT FOUNDATION PART 1

A madadin Gidauniyar Haske Support Foundation da Al'ummar Unguwa ta, ni Hajiya Maryam Shehu Nabage ina kira ga Gwamnatin Jihar Plateau, Sanatan da ke wakiltar Plateau ta Arewa, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bassa/Jos North, Shugaban Karamar Hukumar Jos North, Dan Majalisar Jihar Plateau mai wakiltar Jos North, Kwamishinan Ayyuka da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar mataki kan mummunar lalacewar hanyar Tudun O.C. dake cikin garin Jos.

Wannan hanya ta lalace matuƙa kuma tana jawo hatsarori da asarar rayuka da dukiyoyi akai-akai. Duk da yawan koke-koke daga al’umma, har yanzu ba a dauki matakin da ya dace ba.

Abin da ke kara ci wa jama’a tuwo a kwarya shi ne yadda lokacin yakin neman zabe ake yawan zuwa neman kuri’u da alkawura masu yawa, amma bayan an samu nasara, al’umma s**an ji kamar an manta da su da matsalolinsu.

A matsayina na mai rajin jin kai kuma mai kula da walwalar al’umma, ina ganin lokaci ya yi da za a fifita rayukan jama’a fiye da komai. Mutanen Tudun O.C da sauran masu amfani da wannan hanya suna da hakkin samun ingantacciyar hanya kamar sauran ‘yan kasa.

Muna tunatar da shugabanni cewa rayukan jama’a sun fi komai muhimmanci, kuma ya kamata a fifita gyaran wannan hanya cikin gaggawa domin kare rayuka da sauƙaƙa wahala.

Muna kira da a daina mantawa da al’umma bayan lokacin neman kuri’a, a maida hankali kan cika alkawura.

Allah Ya shiryar da shugabanni Ya ba su ikon yin adalci.

Signed:
Hajiya Maryam Shehu Nabage (Uwar Marayu)
Shugabar Gidauniyar Haske Support Foundation
11th June, 2026

Photos from Haske Support Foundation's post 08/06/2026

Hajiya Maryam Shehu Nabage, shugabar gidauniyar Haske Support Foundation, fitacciyar jaruma ce a fagen ayyukan jin ƙai da taimakon al'umma. Ta sadaukar da rayuwarta wajen tallafawa marasa galihu, marayu, zawarawa da masu buƙata ta musamman, tare da samar da hanyoyin inganta rayuwarsu.

Ta hanyar gidauniyar ta mai suna Haske, ta gudanar da shirye-shiryen tallafi a fannoni daban-daban da s**a haɗa da ilimi, kiwon lafiya, ƙarfafa mata da matasa, da kuma taimakon gaggawa ga mabukata. Saboda irin ƙauna, tausayi da kulawar da take nunawa ga marayu da marasa galihu, mutane da dama suna kiranta da lakabin "Uwar Marayu."

Gudummawar da take bayarwa ta zama haske ga dubban iyalai, tare da zama abin koyi ga mata da matasa a Arewacin Najeriya da ma ƙasa baki ɗaya. Ayyukanta suna ƙarfafa taimakon juna, zaman lafiya da ci gaban al'umma.

Allah Ya ƙara mata lafiya, albarka, hikima da nisan kwana, Ya ci gaba da ba ta ikon yi wa al'umma hidima, Ya kuma saka mata da mafificin alkhairi da gidan Aljannatul Firdausi🙏🏻

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Jos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Tudun O. C. Rikkos, Jos North
Jos