General BMB
General BMB
Film Director | African Actor | Influencer My name is Bello Mohammad Bello (General BMB)
20/05/2026
Ni ba ina yin kamfe din Dr. Jamil Gwamna don wata akida ta Izalah ne ko dan Darika ba. Na tsaya tare da shi ne saboda kwakkwarar shaidar da na samu daga bakin al'ummar Jihar Gombe na dattakonsa, sanin ya kamata, da kuma tsantsar taimakon talakawa da matasa.
Mun yi alkawari za mu tsaya kai da fata har sai nasara ta tabbata insha Allah.
20/05/2026
Muna taya babban mutum mai kishin kasa da al'umma, Dr. Jamil Gwamna (Sardaunan Gombe), murnar sake tabbatar da shi a matsayin dan takarar Gwamna a jam'iyyar APC.
Wannan tabbaci ya nuna cewa al'ummar Gombe a shirye suke su kara bude sabon shafi na cigaba da adalci, wanda zai cigaba da taimakawa rayuwar kowane matashi a jihar Gombe.
Muna tare da kai ɗari bisa ɗari a wannan tafiya ta alkhairi.
Allah Ya ba mu nasara.
WANE HALI KUKA FI SO BABBAN JARUMIN FIM ƊIN YA FITO DA SHI?
1. Jarumin da ke amfani da dabarun sirri wajen kare al'umma?
KO KUMA...
2. Tsohon dan ta'adda da ya tuba yake yakar na daji?
20/05/2026
Makiyin cikin gida shi ne silar kowace barna
Nuna wulakancin karshensu shi ne tushen fim ɗin, kuma kofa a bude take domin mu hada karfi da karfe da ire iren ku don kawo mafita.
20/05/2026
Wannan shi ne jigon rikicin nuna yadda aka assasa rashin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya aka mayar da shi ta'addanci. Za mu fito da wannan rarrabuwar domin a gane gaskiyar lamarin.
20/05/2026
Daina biyan fansa shi ne matakin farko na dakile ta'addancin. Jajircewa da sadaukarwa sune ainihin makamanmu, kuma za mu fito da wannan darasin a fili.
20/05/2026
Manufar fim din ita ce bude idon talaka wajen fahimtar dabaru da danyen aikin ’yan ta’addan, amma ba za mu fallasa sirrin tsaron al'umma ba. Za a yi aiki da taka tsantsan.
20/05/2026
Wannan shi ne jigon wayewar kai. Nuna musu cewa jahilci ne ke mayar da mutum kayan aikin wani, yayin da ilimi kuma ke ba da asalin 'yanci. Shawararka ta shiga kundin tsarinmu.
19/05/2026
You subject people to hunger,
You deny people peace,
You set people against one another in conflict and hatred,
Then in the end, you arrive with food relief and security after the fire of division has already been ignited.
The gullible among us may see you as heroes,
But the enlightened among us see you as zeros.
Stop the premature celebration.
Allah awaits you at the point of reckoning.
NA TSAYA GA ANNABI MUHAMMADU 💚
19/05/2026
Na ga wannan comment din daga daya daga cikin mabiya wannan shafi, kuma gaskiya shawara ce mai amfani da tunatarwa ga al’umma. Matsalar tsaro ba ta shafi mutum iya daya bane kawai, tana shafar kowa da kowa ne.
A matsayinmu na masu shirya fina-finai (Directors/Producers), akwai nauyin da ke kanmu na isar da sakonnin da za su ilmantar, su fadakar, tare da karfafa hadin kai tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.
Ina matukar jin dadin irin wadannan shawarwari masu ma’ana.
Idan za mu shirya fim a kan wannan muhimmin batu na tsaron rayuka da zaman lafiyar al’umma, wane irin sako ko darasi kuke so a fito da shi a ciki?
Ra’ayoyinku suna da matukar muhimmanci a gare ni, domin nasarar wannan aiki tana bukatar shawarwari da gudummawar ku.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Plateau
Jos
930001