SHUNI
Ingantattun labarai masu ɗaukar hankali—ilimantarwa, faɗakarwa, da nishadantarwa.
09/06/2026
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa fushin da ‘yan Najeriya ke yi kan matsin rayuwa da wahalhalun tattalin arziki na ƙaruwa, inda ya gargadi jam’iyyar APC da Shugaba Bola Tinubu cewa ba za su raina ƙarfin hamayya ba yayin shirin zaɓen 2027.
A lokaci guda, Ndume ya roki gwamnatin Amurka da ta kafa sansanin soja a Dutsen Mandara na Jihar Borno domin murkushe ragowar mayakan Boko Haram, yana mai jaddada bukatar haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya da Najeriya wajen yaki da ta’addanci.
Sanata Ndume ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓen 2027, inda ya nuna damuwarsa kan yadda rikicin tattalin arziki da tsaro ke shafar al’umma.
09/06/2026
Rahotanni daga fagen siyasar Kano na nuni da cewa jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, na ci gaba da zawarcin tsohon ɗan takarar gwamnan Kano na APC a 2023, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, domin ya koma jam’iyyar ya tsaya takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Bincike ya nuna cewa ana tattaunawa da wasu na kusa da Gawuna, inda aka ce ADC ta yi masa tayin tikitin gwamna da goyon bayan kamfen. Sai dai har yanzu babu wata sanarwa kai tsaye daga Gawuna ko shugabannin ADC da ta tabbatar da sauya sheƙar, lamarin da ya sa batun ke ci gaba da kasancewa a matakin rade-radi da tattaunawar siyasa.
Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa a baya an ayyana Gawuna a matsayin ɗan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin NDC, yayin da Aminu Abdussalam Gwarzo ya fito a matsayin ɗan takarar gwamna. Idan tattaunawar ADC ta tabbata, ana ganin hakan ka iya sake sauya taswirar siyasar Kano gabanin 2027.
09/06/2026
Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, NDC, reshen Jihar Kano, ta sauya wasu ‘yan takara da aka ce suna da alaƙa da tafiyar Kwankwasiyya, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a siyasar jihar gabanin zaɓen 2027.
Rahotanni sun nuna cewa kujerun da batun ya shafa sun haɗa da wasu na Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma na Majalisar Dokokin Jihar Kano. A cewar bayanan da s**a fito, jam’iyyar ta ce matakin na da alaƙa da tsarin raba mukamai na 60/40 tsakanin tsohuwar tsarin NDC da ɓangaren Kwankwasiyya, amma ɓangaren Kwankwasiyya na nuna rashin jin daɗinsa kan sauye-sauyen.
Wannan rikici na zuwa ne a daidai lokacin da Kano ke ci gaba da zama ɗaya daga cikin jihohin da ake sa ido a kai a siyasar 2027. Masu lura da al’amuran siyasa na ganin idan ba a sasanta ba, saɓanin ka iya shafar ƙarfin haɗin kan NDC da tafiyar Kwankwasiyya a jihar.
09/06/2026
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa a shirye yake ya sasanta da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, duk da saɓanin siyasar da ya shiga tsakaninsu.
A cewar rahoton Punch, Kwankwaso ya ce har yanzu ƙaunar da yake yi wa Abba ba ta ragu ba, yana mai cewa ba shi ne ya yi watsi da gwamnan ba, illa dai Abba ne ya fice daga tafiyarsu ta siyasa. Ya ƙara da cewa idan duk wanda ya fice ya dawo, ba zai zama mai riƙon ƙiyayya ba.
Batun na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Kano ke ci gaba da ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027, musamman bayan sauya sheƙar Gwamna Abba daga NNPP zuwa APC. Masu lura da siyasa na ganin yiwuwar sulhun zai iya tasiri sosai kan makomar siyasar Kano da tafiyar Kwankwasiyya.
09/06/2026
INEC TA ƊAUKAKA ƘARA KAN HUKUNCE-HUKUNCEN KOTU DA S**A SHAFI JADAWALIN ZAƁEN 2027
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar wasu hukuncen Kotun Tarayya da s**a shafi ikon hukumar na tsara jadawalin ayyukan babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC, Prof. Joash O. Amupitan, SAN, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron tattaunawa na biyu na shekara da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar da ke Abuja. Ya ce hukuncen kotunan sun haifar da ruɗani kan wasu muhimman matakai na shirye-shiryen zaɓe, musamman batutuwan jadawalin fidda ‘yan takara da sauran ayyukan jam’iyyu.
INEC ta yi gargaɗin cewa idan ba a samu fayyacewar shari’a cikin lokaci ba, hakan ka iya kawo cikas ga shirye-shiryen zaɓen 2027. Hukumar ta bukaci jam’iyyun siyasa su ci gaba da bin ƙa’idojin zaɓe, yayin da ake jiran hukuncin manyan kotuna kan batun.
09/06/2026
Zulum ya bayyana hakan ne yayin ganawa da wata tawaga daga ƙaramar hukumar Gubio, inda ya ce farkon mulkinsa ya zo da manyan ƙalubale, musamman batutuwan ‘yan gudun hijira, hare-haren ‘yan ta’adda, da bukatar kai ɗauki ga al’ummomin da rikici ya shafa. A cewarsa, shekaru huɗu na farko sun kasance masu matuƙar wahala, amma an fara samun sauyi da taimakon Allah.
Wannan furuci ya sake jawo hankali kan irin sadaukarwar da ake buƙata wajen jagorantar jiha mai fama da matsalar tsaro kamar Borno. Masu sharhi na ganin kalaman na Zulum sun nuna nauyin da shugabanci ke ɗauka, musamman a yankunan da ke buƙatar kulawa ta musamman daga gwamnati da hukumomin tsaro.
09/06/2026
GWAMNA FINTIRI YA NAƊA DR. SUMAYYA SABO A MATSAYIN JAGORAR ADAMAWA DIGITAL ACADEMY
Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, CON, ya amince da naɗin Dr. Sumayya Babangida Sabo a matsayin Programme Coordinator na Adamawa Digital Academy, a wani mataki na ƙara ƙarfafa shirin sauya fasalin jihar ta hanyar ilimin zamani da fasahar dijital.
A cewar sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamna, Humwashi Wonosikou, ya fitar a ranar 9 ga Yuni, 2026, Dr. Sabo ƙwararriya ce a fannin Information Systems, gudanar da ilimi, shirye-shiryen ƙere-ƙere, da kula da harkokin fasahar sadarwa. A halin yanzu tana aiki a matsayin Tutor da IT Coordinator a American University of Nigeria, AUN, da ke Yola.
Sabon aikin nata zai haɗa da kula da shirye-shiryen Academy ɗin, karɓar sabbin ɗalibai, hulɗa da masu ruwa da tsaki, gudanar da harkokin ilimi, da aiwatar da haɗin gwiwar dabaru. Gwamnatin Adamawa ta ce shirin na daga cikin Adamawa 2.0 Digital Transformation Agenda, wanda ke da burin horar da matasa da ma’aikatan gwamnati sama da 100,000 kan fasahohin dijital da sabbin dabarun zamani.
09/06/2026
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya yi kakkausar s**a ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, inda ya zarge shi da amfani da matsalolin tsaro da hare-haren ‘yan bindiga a Najeriya domin neman farin jini gabanin zaɓukan da ke tafe.
09/06/2026
Shin Ko Kun San?
Octopus, wata halittar teku ce mai hannaye takwas, da ke da zukata uku. Biyu daga cikin zukatan suna aika jini zuwa inda take shaƙar ruwa, ɗaya kuma yana aika jini zuwa sauran sassan jikinta. Abin mamaki kuma shi ne, jininta shuɗi (blue) ne, ba ja ba, saboda wani sinadari da ke taimaka mata rayuwa a cikin sanyi da zurfin teku.
08/06/2026
Shin Ko Kun San ?
A wasu yankuna na ƙasar Norway, musamman wuraren da suke kusa da Arctic Circle, rana kan ci gaba da haskawa har cikin dare a wasu watannin shekara. Ana kiran wannan da Midnight Sun. Wannan na faruwa ne saboda yadda duniya take karkata yayin da take zagaya rana. Saboda haka, akwai lokutan da mutane ke rayuwa ba tare da cikakken dare ba na tsawon kwanaki ko makonni.
Darasi: Duniya tana da wurare da yanayi masu ban al’ajabi fiye da yadda muke zato.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Jimeta
640101