Kwallon KAFA
Labarun Kwallan Kafa Da Zafi Zafin Su Akan Lokaci
05/10/2025
Sevilla sun tonawa Barcelona asiri da yammacin ranar yau...! ð±
Kwallon KAFA
29/09/2025
Hukumar Æwallon Æafa ta duniya FIFA ta Æwace makin Afirka ta Kudu bayan ta yi amfani da Éan wasan da aka dakatar, Teboho Mokoena a karawarsu da Lesotho a watan Maris.
Hukuncin ya ce an bai wa Lesotho maki uku a wasan da ci 3-0, sannnan an ci tarar Bafana Bafana kwatankwashin kusan naira miliyan 18.
11/08/2025
Manchester City ta shirya tsaf domin gabatar da tayin yuro miliyan 147 ga Chelsea kan Cole Palmer.
A cewar Fichajes, Chelsea za ta bukaci kusan fam miliyan 200 tare da fam miliyan 50 a matsayin kari. Don haka, Blues na neman kusan fan miliyan 250 kan Cole Palmer.
â Kwallon KAFA
17/03/2025
Sergio Ramos mai shekaru 38 ya karbi jan kati na farko a gasar La Liga MX.
Al'adarsa ta Æwallon Æafa tana cigaba da bin sa...
â Kwallon KAFA
16/02/2025
A cikin wasan da Real Madrid tasha kashi daci 5-0, a hannun Barçelona Cristiano Ronaldo ya ture Guardiola wanda hakan ya haifar fada.
Haka zalika Ronaldo ya ce wa Pedro: "Wane ne kai?"
Pedro ya amsa da cewa: "Ni zakaran gasar cin kofin Duniya ne. Kai kuma kai waye?"
04/01/2025
Ga cikakken bayani akan dokar 1:1!!!
Mutane da yawa suna tambayar menene dokar 1:1 wadda take addabar wasu kungiyoyi a manyan Lig-Lig daban-daban a fadin duniya musamman ma Barcelona a gasar La Liga.
Fagen Wasanni tayi muku bincike domin fitar daku daga duhu akan dokar 1:1 ta gasar La Liga!
Dokar 1:1 a gasar La Liga na nufin kayyade tattalin arziki wadda zata baiwa kungiya dama ta kashe adadin wasu kudade domin daukar sababbin yan wasa daidai da adadin kudin da ta samu wajen siyar da wasu yan wasan da kuma kudaden shigar ta.
Misali: Gaba daya asusun Bankin Barcelona 1000 ne a ciki, kuma wannan dubu dayar da ita suke baiwa yan wasa albashi da sauran dukkan wasu ayyukan kungiyar. Duk abun da Barcelona zata yi ba zai wuce na dubu daya ba. Kungiyar bazata iya kashe ko da Naira 100 ba akan dubu dayar nan domin ana so komai ya daidaita da abun da take samu da kuma abun da zata iya kashewa.
A lissafi idan kudin shigowar Barcelona dana siyar da yan wasanta 1000 ne to kungiyar bazata iya yin abun da ya wuce na 1000 ba domin a samu daidaito.
Kamar kan batun Dani Olmo da Pau Victor, an kayyadewa Barcelona iya adadin kudi da kuma abun da zata iya kashewa a kasuwa naira 1000 amma da kungiyar ta tashi sai ta kashe 1500, kuma gashi a bayyane kudinta 1000 ne, to a dokar La Liga dole sai ta san yadda akai ta samo cikon 500 din nan kafin a bata dama tayi Rijistar Olmo ko Pau Victor.
Hakanne yasa kungiyar ta saida kujerun VIP din ta domin ta daidaita kudadenta su koma 1500, Kuma kamar yadda rahotanni s**a bayyana sun samu damar yin hakan.
A takaice idan har aka ce kungiya ba ta kan dokar 1:1 to ana nufin basa kashe adadin kudin da suke samu, suna kashe fiye da abun da suke samu. Doka kuma tana so kungiya ta dinga kashe adadin kudin da take samu kar ta wuce sama da haka.
Idan baku manta ba a gasar Premier League an taba zarewa Everton maki saboda ana zarginsu da karya dokar kayyade tattalin arziki, FA na tuhumar Everton da kashe abun da yafi karfin tattalin arzikinsu hakanne y
03/01/2025
Halftime
Valencia 1:0 Real Madrid
03/01/2025
Hansi Flick akan Dani Olmo: "Maganar gaskiya ban ji dadin akan yanayin da ake ciki ba, suma kansu yan wasan mu haka - Amma haka lamarin yake. Dukkan mu mun san mai muke yi. Kuma muna da kwarin gwiwa. Kawai zamu jira lokaci.
"Ba aiki na bane batun Rijistar Olmo. Na yi magana da shugaba Laporta yau kuma ina da kwarin gwiwa akan kungiyar mu. Suna yin aikinsu, nima ina yin nawa."
Kwallon KAFA
03/01/2025
Bayan kammala tankade da rairaya
Wayannan sune jerin yan wasa 11 yan kasa da shekaru 21 mafi kyau a Duniya a 2024 na Foot Mercato.
Shin wane bai cancanta ba?
Kuma wane ya cancanta ba'a sa shi ba?
Kwallon KAFA
03/01/2025
Pep Guardiola akan batun kwantaragin De Bruyne: "Wannan ya rage na kungiyar. Ba aiki na bane, magana ce akan ya yanayin kokarinsa zai kasance har zuwa karshen kakar wasa, shekarun da yake da su da kuma sauran wasu abubuwan. Ina tunanin kungiyar zata yi duba akan hakan."
Kwallon KAFA
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Hadejia