Hadejia Online News
We connect the people, promote unity, and give Hadejia a strong digital voice.
Hadejia Online is a community-based digital media platform committed to sharing accurate news, public announcements, events, and development stories from Hadejia and beyond.
24/06/2026
GIDAN SUGA NA HADEJIA: WATA BABBAR DAMA GA TATTALIN ARZIKIN JIGAWA
Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da J-INVEST, lokaci ne da ya dace a sake waiwayar aikin Gidan Suga na Hadejia, wanda ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan masana'antu da za su iya sauya fasalin tattalin arzikin Jihar Jigawa.
Gidan Suga na Hadejia ba kawai masana'anta ba ce, wata babbar dama ce ta samar da ayyukan yi, ƙarfafa noman rake, bunƙasa kasuwanci da ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnati da al'umma baki ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa idan aikin ya kammala tare da fara aiki gaba ɗaya, zai samar da ɗaruruwan ayyukan yi kai tsaye da kuma wasu da dama ba kai tsaye ba.
Haka kuma an tsara samar da s**ari, ethanol, abincin dabbobi da makamashi daga kayayyakin da ake samu daga rake.
A matsayinta na jiha mai albarkatun noma da ruwa, Jigawa na da damar zama ɗaya daga cikin cibiyoyin samar da s**ari a Najeriya idan aka bai wa irin waɗannan manyan ayyuka kulawar da s**a dace.
Yayin da masu zuba jari daga sassa daban-daban za su hallara a J-INVEST, ya kamata a ba da fifiko wajen tattaunawa kan hanyoyin kammala da farfaɗo da Gidan Suga na Hadejia, domin hakan zai ƙara jawo masu zuba jari, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin Hadejia da Jihar Jigawa baki ɗaya.
Tambayar ita ce: Shin lokaci bai yi da za a mayar da Gidan Suga na Hadejia ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan tattalin arzikin Jigawa ba?
~Abubakar Usman Turaki
~Hadejia Online News
Photo 📷:Sani Ubali Slacker
23/06/2026
Wata miyar..........
23/06/2026
Rahoto Kan Kasuwar Mallam Madori (Jihar Jigawa)
Kasuwar Malam Madori na daga cikin manyan kasuwannin yankin Hadejia da ke taka muhimmiyar rawa wajen harkokin kasuwanci da noma. Kasuwar tana gudana duk mako, kuma ranar Talata ce ranar babbar kasuwa inda manoma, 'yan kasuwa da masu kiwo daga sassa daban-daban ke taruwa domin gudanar da cinikayya.
Muhimman Kayayyakin da Ake Ciniki Da Su
-Gyada da man gyada
-Dawa da gero
-Wake da ridi
-Shanu, tumaki da awaki
-Kayan masarufi da kayan abinci
-Kayan sana'o'in gargajiya
Muhimmancin Kasuwar Ga Tattalin Arziki
Kasuwar Mallam Madori tana samar da hanyar samun kudin shiga ga dubban mazauna yankin, musamman manoma da masu kiwo. Haka kuma tana taimakawa wajen hada yankunan karkara da manyan cibiyoyin kasuwanci a Jigawa da jihohin makwabta. Tattalin arzikin yankin ya fi karkata ga noma da kasuwanci.
Tarihin Ci Gaban Kasuwar
Tarihin Mallam Madori ya nuna cewa gina layin dogo na Kano zuwa Nguru ya taimaka sosai wajen bunkasa kasuwanci a yankin. Hakan ya sa mutane daga garuruwa makwabta s**a rika zuwa domin ciniki, kuma garin ya zama daya daga cikin cibiyoyin kasuwanci masu muhimmanci a masarautar Hadejia.
Kalubale da Damar Ci Gaba
Duk da muhimmancin kasuwar, akwai bukatar ci gaba da inganta hanyoyin sufuri, wuraren ajiya da sauran kayayyakin more rayuwa domin kara habaka harkokin kasuwanci.
A shekarun baya-bayan nan, gwamnatin Jigawa ta fara manyan ayyukan hanyoyi a yankin Mallam Madori domin saukaka jigilar amfanin gona zuwa kasuwanni.
Daga karshe
Kasuwar Mallam Madori na daga cikin ginshikan tattalin arzikin yankin arewa maso gabashin Jigawa. Tana tallafawa noma, kiwo da kasuwanci, tare da samar da hanyoyin samun kudin shiga ga al'umma da dama.
~Abubakar Usman Turaki
Photo 📷: Abubakar B Danladi
~Hadejia Online News>
23/06/2026
Assalamu Alaikum,
Allah ya yiwa Mairama Rakiya Alh Haruna (Goggo Inkama) Rasuwa, Yar Sarkin Hadejia Alh Haruna Abdulkadir, Matar Marigayi Galadiman Hadejia Habibu Adamu kuma Mahaifiya ga Mai girma Dan Galadiman Hadejia alh Ilyasu Habibu Adamu, Mustapha Habibu Adamu, Usman Habibu Adamu da Sadiya Habibu Adamu.
Za ayi Jana'iza da karfe 1:30 na rana , a Kofar Fada.
muna addu'a Allah Ubangiji yayi mata rahama yasa Aljannah firdausi makomar ta Amin.
Hadejia Emirate
23/06/2026
DASA BISHIYU A GEFEN TITIN HADEJIA ZUWA GARIN GABAS: ALHAKIN AL’UMMA NE
Jiya na ga wani rubutu da Sawaba FM 104.9 Hadejia s**a wallafa tare da hotunan t**in Garin Gabas da aka gyara, da kuma wasu sassan NTA Quarters. Daga yadda aka ɗauki hotunan, da alama an yi amfani da na’urar drone.
Babu shakka, gwamnati ta yi ƙoƙari matuƙa wajen gyaran wannan t**i. Sai dai yanzu akwai wani muhimmin aiki da ya rataya a wuyan mazauna yankunan da t**in ya ratsa. Wannan aiki shi ne dasa bishiyu a gefen t**in a wannan damina, domin a halin yanzu babu ko bishiya ɗaya a gefensa.
Wannan aiki ya fi dacewa ƙungiyoyin unguwanni da mazauna yankin su jagoranta, ba wai gwamnati kaɗai ba. Hakan kuwa saboda renon bishiya ya fi dasa ta wahala, kuma al’umma su ne s**a fi kusa da kula da ita.
Idan t**i ya koma na kwalta (asphalt), yana ƙara zafi a muhalli domin yana tara zafin rana da rana, sannan da daddare yake sakin wannan zafi. Haka kuma gine-gine da kwalta suna taimakawa wajen riƙe zafin rana, wanda ke sa wasu lokuta ko sanyin asuba ya ragu.
Dasa bishiyu a gefen t**i ba wai rage zafi kaɗai zai yi ba. Haka kuma zai taimaka wajen rage zaizayar ƙasa a gefen t**i, ya taimaka wajen tsawaita rayuwar t**in, ya samar da inuwa ga masu amfani da hanya, ya ƙara wa muhalli kyau, kuma ya kare gidaje da unguwanni daga iska mai ƙarfi.
Yawancin titunanmu ba su cika samun masu tafiya a lokacin zafi ba saboda tsananin rana. Bishiyu ne mafita ga wannan matsala. Baya ga haka, masu dasa su za su samu lada, domin shuka bishiya na daga cikin ayyukan alheri kuma sadaka ce mai gudana.
Saboda haka, muna kira ga ƙungiyoyin unguwanni da dukkan mazauna yankunan da ke gefen t**in Hadejia zuwa Garin Gabas da su tashi tsaye wajen tabbatar da wannan aiki.
Gwamnati ta yi nata ƙoƙarin wajen gyara hanya, amma kiyaye ta da inganta muhallin da ke kewaye da ita yana hannun al’umma.
©️ Nuraini Abba Muhammad
23rd June, 2026.
22/06/2026
Hadejia LGA Shortlisted Candidates for UNICEF EYEPINN Programme Learning Facilitators Recruitment
Interview Date: 23rd June 2026
Venue: Abdulkadir Special Primary School
Congratulations to all shortlisted candidates. We wish you the very best in the interview and success throughout the selection process.
21/06/2026
Tsokaci Kan Railway Station na Mallam Madori,
Jihar Jigawa
Railway Station na Mallam Madori wani muhimmin tarihi ne da ya taka rawa wajen bunƙasa tattalin arziki da kasuwancin yankin tun shekaru da dama da s**a gabata.
Tarihi ya nuna cewa zuwan layin dogo da gina tashar jirgin ƙasa a Mallam Madori ya jawo ƙaurar 'yan kasuwa da manoma daga garuruwa da dama zuwa yankin, wanda hakan ya mayar da Mallam Madori cibiyar kasuwanci a masarautar Hadejia.
A yau, al'ummar Mallam Madori da ma Jigawa baki ɗaya suna da buƙatar a farfaɗo da harkokin sufurin jirgin ƙasa domin sauƙaƙa zirga-zirga, rage tsadar jigilar kayayyaki, da samar da sabbin damar kasuwanci ga matasa da manoma.
Jirgin ƙasa na daga cikin hanyoyin sufuri mafi araha da aminci, kuma sake inganta tashar Mallam Madori zai taimaka wajen haɗa yankin da manyan cibiyoyin kasuwanci na ƙasa.
Ra'ayi:
"Railway Station na Mallam Madori ba kawai tarihi ba ne, alama ce ta ci gaba da bunƙasar tattalin arzikin al'umma.
Ya kamata gwamnati da masu ruwa da tsaki su mayar da hankali wajen farfaɗo da harkokin layin dogo domin samar da ayyukan yi, ƙarfafa kasuwanci, da bunƙasa harkokin noma a yankin.
Duk yankin da jirgin ƙasa ya isa, ci gaba kan biyo baya."
✍️ Daga Desk na Hadejia Online News
Railway Station na Mallam Madori wata muhimmiyar gada ce ta tarihi da ci gaban tattalin arzikin yankin Hadejia da Jigawa baki ɗaya.
Al'umma na fatan hukumomi za su sake farfaɗo da harkokin layin dogo domin bunƙasa kasuwanci, noma da samar da ayyukan yi ga matasa.
Hadejia da Mallam Madori suna daga cikin yankunan da s**a amfana da layin dogo a tarihi, kuma sake inganta shi zai ƙara haɗa yankin da manyan cibiyoyin kasuwanci na ƙasa.
~Abubakar Usman Turaki
Hadejia Online News
Photo 📷: Abubakar B Danladi
21/06/2026
SANARWA A HUKUNCE
DAGA OFISHIN MAI GIRMA KAMISHINAN MA'AIKATAR HARKOKIN JINƘAI DA AYYUKA NA MUSAMMAN, JIHAR JIGAWA
SABUN BAYANI KAN RABA KATIN SHIRIN TALLAFIN KUƊI NA SHARAƊI (NSIPA CCT) NA GWAMNATIN TARAYYA A ƘANANAN HUKUMOMI 27 NA JIHAR JIGAWA.
A matsayin wani ɓangare na jajircewar Gwamnatin Jihar Jigawa wajen bunƙasa rayuwar al'umma, rage talauci da ƙarfafa tattalin arzikin iyalai masu ƙaramin ƙarfi, ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi, FCA, Ma'aikatar Harkokin Jinƙai da Ayyuka na Musamman tare da haɗin gwiwar Hukumar Shirye-shiryen Tallafin Jama'a ta Ƙasa (NSIPA) na sanar da al'umma sabon bayani kan ci gaba da rabon katunan Shirin Tallafin Kuɗi na Sharaɗi (Conditional Cash Transfer – CCT).
Ta wannan muhimmin shiri, kowane wanda aka tantance kuma ya cancanta zai karɓi jimillar Naira 75,000 kacal (₦75,000). Wannan tallafi na da nufin rage wahalhalun tattalin arziki da tallafa wa waɗanda s**a fi buƙatar taimako.
An tsara rabon katunan zuwa matakai daban-daban domin tabbatar da tsari da gudanar da aiki cikin nasara a dukkan Ƙananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa.
1. JADAWALIN RABON KATUNA NA YAU
Yau Lahadi, 21 ga Yuni, 2026, ana gudanar da rabon katuna a waɗannan ƙananan hukumomi:
Babura: Masu cin gajiya 913 (Sabbi 448, Cikawa 465).
Garki: Masu cin gajiya 770 (Sabbi 70, Cikawa 700).
2. ƘANANAN HUKUMOMIN DA AKA KAMMALA RABON KATUNA
An kammala rabon katuna cikin nasara a waɗannan ƙananan hukumomi:
Gwaram – 3,422 (13–14 Yuni)
Birnin Kudu – 1,052 (15 Yuni)
Buji – 696 (15 Yuni)
Dutse – 1,384 (16 Yuni)
Kiyawa – 1,351 (16 Yuni)
Jahun – 1,545 (17 Yuni)
Miga – 947 (17 Yuni)
Kazaure – 1,060 (18 Yuni)
Roni – 542 (18 Yuni)
Gwiwa – 1,296 (19 Yuni)
Yankwashi – 1,004 (19 Yuni)
Ringim – 859 (20 Yuni)
Taura – 1,250 (20 Yuni)
3. JADAWALIN RABON KATUNA MAI ZUWA
Litinin, 22 ga Yuni, 2026
Gagarawa – 603 (Sabbi 242, Cikawa 361)
Gumel – 1,071 (Sabbi 120, Cikawa 951)
Talata, 23 ga Yuni, 2026
Maigatari – 1,426 (Sabbi 387, Cikawa 1,039)
Sule Tankarkar – 1,335 (Sabbi 370, Cikawa 965)
Laraba, 24 ga Yuni, 2026
Biriniwa – 860 (Sabbi 224, Cikawa 636)
Guri – 1,361 (Sabbi 291, Cikawa 1,070)
Alhamis, 25 ga Yuni, 2026
Kiri Kasamma – 2,100 (Sabbi 263, Cikawa 1,837)
Jumma'a, 26 ga Yuni, 2026
Kaugama – 1,080 (Sabbi 123, Cikawa 957)
Malam Madori – 1,780 (Sabbi 327, Cikawa 1,453)
Asabar, 27 ga Yuni, 2026
Auyo – 1,787 (Sabbi 968, Cikawa 819)
Lahadi, 28 ga Yuni, 2026
Kafin Hausa – 2,090 (Sabbi 209, Cikawa 1,881)
Litinin da Talata, 29–30 ga Yuni, 2026
Hadejia – 2,174 (Sabbi 253, Cikawa 1,921)
A wannan zagaye na shirin, za a tallafa wa jimillar masu cin gajiya 35,758 a dukkan Ƙananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa, waɗanda s**a haɗa da 8,021 sabbin masu cin gajiya da 27,737 na cikawa (Mop-up).
MUHIMMAN UMARNI GA MASU CIN GAJIYA
Ku kasance masu bin doka da oda: Ku ba jami'an tsaro, jami'an NSIPA da masu kula da shirin haɗin kai domin gudanar da aikin cikin lumana.
Ku zo da takardun da ake buƙata: Ku tabbatar kun zo da ingantacciyar shaidar zama ɗan ƙasa da sauran takardun tantancewa da aka ba ku.
Ba a biyan kuɗi: Raba katunan da kuma biyan tallafin ₦75,000 kyauta ne. Kada ku bai wa kowa kuɗi da sunan zai taimaka muku. Ku kai rahoton duk wanda ya nemi cin hanci ga jami'an ma'aikatar nan take.
Gwamnatin Jihar Jigawa na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa wannan tallafi ya isa ga waɗanda s**a cancanta cikin gaskiya, adalci da cikakken tsari.
An Sanya Hannu:
Hon. Auwal D. Sankara (F**A)
Kwamishinan Ma'aikatar Harkokin Jinƙai da Ayyuka na Musamman,
Jihar Jigawa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Hadejia