Hadejia Emirate
Official Page of Hadejia Emirate
MOTTO: Majestic City of Stallion/Birnin doki
TWITTER @Hadejia_Emirate
INSTAGRAM @hadejia_emirate
16/09/2026
MARIGAYI MAIGIRMA SARKI FULANIN HADEJIA
Marigayi Sarkin Fulanin Hadejia Alhaji Abubakar Baffa Usman, daya daga cikin zuriyar gidan MAGARYA
Dan Sarkin Arewan Hadejia Usman ne, Jikan Sarkin Arewa Abubakar ne
Marigayi Sarkin Fulani Tsohon Ma'aikacin Karamar hukuma ne, yayi aiki a kananan hukumomi da dama, Ya bar aiki yana matsayin Ma'ajin karamar hukuma
A ranar 3-6-2001 Marigayi Maimartaba Sarkin Hadejia Alhaji Abubakar Maje Haruna
Ya nada Marigayin Sarauta a Matsayin Ajiyan Hadejia na farko Hakimin Gundumar Diginsa
Daga bisani aka samu sauye sauye Gundumomin, a inda hakimi ya rike Gundumomin har guda hudu 4
Yayi Hakimin Gundumar Diginsa
Yayi Hakimin Gundumar Garun Gabas
Yayi Hakimin Gundumar Jabo
Yayi Hakimin Gundumar Yalo
A ranar 14-9-2024 Maimartaba Sarkin Hadejia Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje CON, ya daga Darajar Sarautar sa daga Ajiyan Hadejia zuwa Sarkin Fulanin Hadejia Dan Majalissar Sarki
Nayi aiki tare dashi a lokacin yana hakimin gundumar Yalo, ina matsayin makaddas din sa
Mutumin kirki ne matuka, masanin makamar mulki, Mutum ne mai son talakawan sa, mai kokarin yaga ya kawo cigaba gundumar sa
Daga karshe muna miki sakon Ta'aziyyar mu ga Maimartaba Sarkin Hadejia tare da dukkanin hakiman sa
Muna mika sakon Ta'aziyyar mu zuwa zuriyar gidan Magarya a karkashin Sarkin Arewan Hadejia
Muna adu'ar Allah yaji kan sa da rahama, Allah yasa jinya ta zamemasa Kaffara, Allah yasa Aljanna fiddausi ce makoma a gare shi
Allah yaji kan magabatan mu, idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da imani
15/09/2026
Allah Ya yiwa Sarkin Fulanin Hadejia Alh. Abubakar Baffa Usman Rasuwa
Za'ayi Jana'iza Yau Da Misalin Karfe 5 NaYamma Kofar Sarkin Arewan Hadejia Dake Unguwar Bayi.
Allah Yajikansa Ya Gafarta Masa Tare Sauran Musulmi Baki Daya
Ran Sarki Ya Dade ✊
14/09/2026
Allah Ya Jazamanin Sarki✊🙏
14/09/2026
CIKA SHEKARU 24 A KARAGAR MULKIN HADEJIA
A yau, 14 ga Satumba, 2026, ya yi daidai da ranar 14 ga Satumba, 2002, ranar da Mai Martaba Sarkin Hadejia ya hau karagar mulkin Masarautar Hadejia.
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alh. (Dr.) Adamu Abubakar Maje, CON, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa, ya cika shekaru 24 a kan karagar mulkin Masarautar Hadejia.
Muna taya Mai Martaba murnar wannan gagarumin tarihi, tare da addu'ar Allah Ya ƙara masa lafiya, imani, hikima da basira. Allah Ya ƙara masa tsawon rai mai albarka, Ya ba shi ikon ci gaba da gudanar da adalci da jagoranci nagari a tsakanin al'ummar Masarautar Hadejia.
Allah Ya ƙara wa Mai Martaba lafiya da nisan kwana cikin albarka. Amin. 🤲
12/09/2026
TARIHIN MARIGAYI SARKIN HADEJIA ABUBAKAR MAJE HARUNA.....
Bayan rasuwar Sarkin Haɗejiya Alhaji Haruna sai aka naɗa Ɗansa Alhaji Abubakar Maje Haruna a matsayin Sarkin Haɗejiya na goma sha biyar (15), A jerin sarakunan Fulani, an naɗashi ranar Juma'a 31st/august/1984. Sai akayi Sarki mai farin jini da hakuri da son mutane, a wajen kyauta kuwa ya kasance mai Alheri tun yana ƙaraminsa. Sarkin Haɗejiya Abubakar kafin zamansa sarki yayi Ayyuka da dama, sannan ya kasance Ɗan kasuwa.
A zamaninsa an samu sauye sauye da dama a ƙasar Haɗejiya, musamman Ɓangaren Ilmin Addini dana zamani Kasuwanci da siyasa. Sarkin Haɗejiya Abubakar Maje ya halarci makarantu da dama inda ya fara halartar makarantar Elementary dake Unguwar Dallah a shekarar 1945, sannan ya tafi makarantar Middle School dake Unguwar fantai a shekarar 1949 zuwa 1952. Haɗejia A yau. Ismaila A Sabo
Sarkin Haɗejiya Abubakar ya tafi makarantar T.T.C. Maru dake a Lardin Sokoto a wancan lokacin, ya fara a cikin shekarar 1953 zuwa 1956. Sarkin Haɗejia Abubakar ya koma makarantar horar da ma’aikata dake Potiskum ta jihar Borno, wadda yanzu take a jihar Yobe. Kuma ya fara aikin gwamnati a matsayin Malamin Hakimi a Gundumar Bulangu, sannan ya riƙe muƙamin Magatakarda a majalissar Sarki. Saboda iya mu’amala da son jama’a sai yazama duk inda ka ganshi bazaka ganshi shi kaɗai ba sai da jama’a, hakan ya bashi nasarar gogewa wajen tafiyar da shugabancin jama’a. Haɗejia A yau.
https://isabohadejia.blogspot.com/2016/08/15-sarkin-haejia-abubakar-maje-haruna.html?m=1
12/09/2026
Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, ya karɓi bakuncin tawagar jami’an Gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, tare da Kwamandan Bataliyar Sojojin Jihar Jigawa, Brig. Gen. O. I. Odigie, a Fadar Mai Martaba.
Ziyarar ta gudana ne a ranar Juma’a, 11 ga Satumba, 2026, tare da halartar wakilan Karamar Hukumar Hadejia, domin tattauna da tabbatar da samar da Barikin Sojoji na 263 Tank Battalion, Hadejia, a Karamar Hukumar Hadejia.
Mai Martaba ya bayyana jin daɗinsa da wannan muhimmin shiri, wanda zai ƙara ƙarfafa tsaro da zaman lafiya a Hadejia da ma sauran sassan Jihar Jigawa.
SHATA WAKAR SA TA "Zaki Sarkin Hadejia Maje"
11/09/2026
Ko Kai/Ke ma ka taba zuwa karbar sadar KWANDALA da Sarki Maje keyi a duk safiyar Duniya? 😅
Jawabin Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje, CON, a yayin ziyarar da Mai Martaba Sarkin Gumel, Alh. Dr. Lawal Ahmad Sani, ya kawo masa a fadarsa.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Address
Emir's Palace Road
Hadejia
171101