Rabiatu Muhammad
Welcome to Sirrin Yayan Itatuwa – a page for stories, advice, entertainment & more. Wannan shafi ne na dariya, ilimi,
shawarwari, da kuma Sirrin Yayan Itatuwa.
Ku biyo mu!
Tips for growing your page
゚viralシfypシ゚ Rabiatu Muhammad
02/06/2026
Wani abin tausayi da tunani shi ne yadda yaran marayu da marasa gata suke samun kulawa da soyayya daga wasu bayin Allah masu zuciya ta alheri. Wallahi irin wannan alkhairi ba abu ne mai sauƙin mantawa ba. Ko kai ba maraya ba ne, idan wani ya taba yi maka irin wannan gata, tabbas zuciyarka ba za ta manta ba.😭🤲
A ci da su abinci mai kyau,
a sha da su abin sha mai kyau,
a samar musu da wajen kwana mai tsafta,
a tufatar da su cikin mutunci,
a yi musu magana mai dadi da kulawa,
a saka musu farin ciki a rayuwa,
har ma a ba su ilimi mai inganci kamar sauran yaran masu gata.
A cikin yaran akwai marayu, akwai marasa hali, akwai wadanda aka yar da su tun suna kanana, akwai masu iyaye amma babu abin ci ko sha. Haka kuma akwai wasu yaran da suke yawo a t**i ba tare da kulawa ba, idan aka gan su sai a taimaka musu da iya hali.
Wasu daga cikin yaran nan ma ba su san iyayensu ba, amma suna samun tarbiyya da kulawa kamar ‘ya’ya na gaskiya. Wasu sun girma sun zama samari da ‘yan mata, wasu kuma har yanzu suna tasowa cikin kulawa da kauna. Wannan babban aikin alheri ne da ya cancanci yabo da addu’a. Allah Ya saka da alkhairi ga duk masu taimakon marayu da marasa gata.🤲❤️
Rabiatu Muhammad
Malam a tashi a nemi nakai talauci wlh ba Sunnah bane.
゚viralシfypシ゚ Rabiatu Muhammad
Ku fa bar ganina haka Nima inada buri
゚viralシfypシ゚ Rabiatu Muhammad
01/06/2026
Aunty Rabi Dan Allah kiyi min posting Yan uwa su fadamin abinda xe kwantarmin da hankali na hakura mijinane watanmu biyu da aure kawata tazomin wuni se ruwan sama yasa tayi dare shine ya kaita gida da motansa daganan s**a dinke yace itama ze aurota.
Nice matarsa ta biyu dukanmu talakawa ne Kuma masu talle Amma kafin ya auremu seda ya wadata iyayenmu da komai na kayan more rayuwa mu dasu ba abinda muka rasa ko Baki nayi inde kinsame shi agida seya baki abinda ze isheki jari babu abinda muka rasa nida iyayena da Yan uwana a wjenshi ahaka nan ya shigo da lamarin ze auri kawata Kuma kawar tawa ta amince shine gaba daya hankalina ya kasa kwanciya kullum tunani bana cikin nutsuwa.
Nide da farko cemata nayi kinci gidanku da neman shawarin kafin namata nasiha ko kunga lefina,amma duk da haka nace zanyi posting dan kukara mata da naku,nifa inkamin haka to wlh kowa ma ka ga dama ka aura kowa fa Kuma da gidanta
Allah ya sa mu dace Yaba kowa zaman lafiya agidan aurensa.
Plx kukara samin ita a hanya Dan Allah.
゚viralシfypシ゚
01/06/2026
🌸 SHAWARA GA MATA 🌸
Ya mace mai daraja…
Ki sani cewa kyawunki ba wai a fuska kawai yake ba, har da halayyarki, mutuncinki da yadda k**e mu’amala da mutane.
✔️ Ki kasance mai hakuri a gida.
✔️ Ki rika girmama mijinki da iyayenki.
✔️ Ki kula da tsafta da kamshinki.
✔️ Ki rika magana cikin nutsuwa da hikima.
✔️ Ki dage da addu’a da neman ilimi.
Mace ta gari tana gina gidanta ne da soyayya, hakuri da fahimta. 💕
Kada ki bari fushi ya rushe abin da hakuri zai iya gyarawa.
Allah sarki tuwo da fa ka zagu amma yanxu har masu kudi zakaji suna tuwo yafi komai dadi
Dan Allah kuyi following dina kuyi liking kuyi share inshaAllah yanxu abubuwana ze koma videos da iKon Allah Dan mutane Sufi fahimtanmu wannan gwajine kawai
Allah yasa mu dace
゚viralシ
31/05/2026
“Wasu mata suna ganin girki aikin wahala ne, amma ki tuna cewa abinci ba wai cika ciki kawai yake yi ba… yana kara soyayya da kulawa a tsakanin ma’aurata. ❤️
Namiji idan ya dawo gida cikin gajiya sannan ya samu kulawa da abinci mai dadi daga matarsa, zuciyarsa tana kara natsuwa da farin ciki.
Ba dole sai kin iya manyan girke-girke ba. Ko simple food da aka yi da soyayya yana da muhimmanci sosai a aure.
Mata ku rage yawan cewa:
‘Ka siyo a waje.’
‘Ban da lokacin girki.’
‘Ka dafa da kanka.’
Aure yana bukatar kokari daga bangarorin biyu. 🙏
Ke fa, mene ne ra’ayinki? Shin mace tana da muhimmiyar rawa wajen girkin gida?”
31/05/2026
AMFANIN SHAN RUWAN DUMI DA SAFE 🌿
Shan ruwan dumi da safe kafin cin abinci na iya taimakawa wajen:
✅ Taimakawa narkewar abinci
✅ Rage kumburin ciki
✅ Tsaftace jiki
✅ Kara kuzari da walwala
Wasu ma suna hada shi da zuma ko lemon tsami domin karin anfani. Amma a kiyaye yawan amfani idan akwai wata matsalar lafiya. 👍
Lafiya ita ce babban arziki. Allah ya ba mu lafiya mai anfani. 🤲
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Atta Ikpehe Street Gwagwalada Abuja
Gwagwalada
902101