Anne Jason
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Anne Jason, Journalist, tudun wada, Gusau.
Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC ranar Litinin
Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa jam’iyyar ADC a ranar Litinin mai zuwa.
Majiyoyi sun shaida cewa wannan sauyin sheƙa ya biyo bayan makonni na shawarwari tsakanin Kwankwaso, ƙungiyarsa ta Kwankwasiyya da shugabannin jam’iyyar ADC.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi jerin ganawa da manyan jiga-jigan ADC da sauran ‘yan adawa a ‘yan makonnin nan.
A makon da ya gabata, ya gana da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a Kano a matsayin wani ɓangare na ci gaba da tattaunawa.
Haka kuma, ya tattauna da wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da Sakataren Ƙasa na ADC, Rauf Aregbesola; ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi; gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde; da Sanatan Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson.
Rahotanni sun ce wannan mataki na daga cikin yunƙurin sake fasalin haɗin gwiwar ‘yan adawa gabanin babban zaɓen 2027, domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da aka samu rabuwar alaka tsakanin Kwankwaso da tsohon yaronsa a siyasa kuma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Yusuf, wanda ake kallonsa a matsayin ɗan siyasar da Kwankwaso ya raina da ƙungiyar Kwankwasiyya, ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC tare da wasu ‘yan majalisa da masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Sai dai Kwankwaso ya nuna rashin amincewa da wannan mataki, inda ya nisanta kansa da shi tare da bayyana hakan a matsayin cin amana.
28/03/2026
Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gana da Sheikh Sani Khaleefa Zaria a wajen da hukumomi ke tsare da shi.
Me za ku ce?
Kai tsaye: yadda ake gudanar da bikin ƙaddamar da shugabannin matasa na ƙungiyar Sokeza APC Youth Movement na matakin jiha da ƙananan hukumomi. A jihar Zamfara
Wuri: Taula Arena, Gusau, Jihar Zamfara
25/03/2026
DSS sun kubutar da sakataren ƙaramar hukumar Kibiya tare da k**a waɗanda su ka yi garkuwa da shi
Jami’an hukumar tsaron farin kaya na DSS sun k**a wadanda s**a yi garkuwa da Sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya a Kano Hon. Hamza Musa Durba inda s**a kuɓutar da shi k**ar yadda jaridar Arewa Updates ta rawaito.
Bayanan da Arewa Updates ta samu sun nuna cewa jami’an sun kubutar da sakataren ne a wani daji da ke Kibiya bayan da aka soma tattaunawa da wadanda s**a yi garkuwa da shi ta waya.
Jamiʼan sun k**a 2 daga cikin inda aka same su da bindiga ƙirar Ak47.
Ana ci gaba da bincike kan lamarin.
Kadan daga cikin tawagar jagoran dirkar siyasar gidan turakin zamfara hon yusuf MD Gusau digital coordinator
Inda ake dakon jiran minister of defense Dr Bello Matawalle tare da MD C.E.O yazeed Shehu Danfulani.
A yaune za a karbi gwamna jahar zamfara dauda lawal zuwa jam'iyar APCn kasar. Wanda mataimakin shugaban kasar Najeriya kashin shatima zai karbi sauyin shekara gwamna jahar. Tare da shugaban jam'iyar APC da gwamanoni da man yan kasar
Kai tsaye: yadda al'ummar ke ciki gaba da mika gaisuwar ban girma ga Dr Sani Abdullahi Shinkafi Wamban Shinkafi kan hanyarsa daga Fadar gwamnatin Zamfara bayan da magoya bayansa s**a raka rufa masa baya, a cikin da shirye-shiryen bikin karɓar Gwamna Dauda Lawal zuwa APC
Kai tsaye: yadda al'ummar ke ciki gaba da mika gaisuwar ban girma ga Dr Sani Abdullahi Shinkafi Wamban Shinkafi kan hanyarsa daga Fadar gwamnatin Zamfara bayan da magoya bayansa s**a raka rufa masa baya, a cikin da shirye-shiryen bikin karɓar Gwamna Dauda Lawal zuwa APC
Zamfara ta kafa tarihi bayan jirgin sama ya fara sauka a filin jirgi na Gusau
Ya zama wajibi mugodema Dr Bello Matawallen Maradun Ministan Tsaron Najeriya, Domin Shine Ya Samar da wannan wuri a lokacin da Yana Gwamnan Jahar Zamfara.
22/03/2026
WAMBAN SHINKAFI POLITICAL FRONT
PRESS RELEASE
WAMBAN SHINKAFI TO ATTEND RECEPTION CEREMONY FOR GOVERNOR DAUDA LAWAL’S DEFECTON TO APC
As preparations intensify by the All Progressives Congress (APC) for the anticipated defection of the Governor of Zamfara State, Dauda Lawal, from the Peoples Democratic Party (PDP) to the APC, a prominent APC chieftain in the state, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi (Wamban Shinkafi), has confirmed his participation in the reception ceremony alongside his supporters.
In line with the ongoing arrangements, Dr. Shinkafi has directed the leader of Wamban Shinkafi political front Yushau Abdullahi Mada to coordinate logistics for the mobilization of supporters across all the fourteen (14) Local Government Areas of Zamfara State. This includes the provision of transportation to ensure the smooth conveyance of party loyalists to the event venue.
The reception is scheduled to take place on Tuesday, March 24, 2026, at the Trade Fair Complex in Gusau. The event is expected to attract high-profile dignitaries, including the Vice President of the Federal Republic of Nigeria, state governors, and other top government officials.
Dr. Shinkafi has called on all his supporters to remain calm, disciplined, and law-abiding throughout the event. He emphasized the importance of maintaining peace and strictly avoiding any form of violence or possession of weapons during the gathering.
He further congratulated Governor Dauda Lawal on his decision to join the APC, describing the move as a significant step toward strengthening the party and fostering unity, progress, and an end to internal political disputes within the party in the state.
Dr. Shinkafi concluded by praying for a peaceful and successful event and for the safe return of all attendees to their respective homes.
Signed:
Nasiru Musa Adabka
March 22, 2026
22/03/2026
Fiye da ‘yanbindiga 150 sun nutse bayan kwale-kwale ya kife a Sokoto
Rahotanni sun bayyana cewa akalla ‘yanbindiga sama da 150 sun mutu sak**akon nutsewa bayan wani kwale-kwale da ke dauke da su ya kife a yankin Sabon Gida da ke Jihar Sokoto, k**ar yadda Zagazola Mak**ai ya rawaito.
Majiyoyin yankin sun shaida wa Zagazola Mak**ai cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar, lokacin da jirgin ruwan da ke dauke da dimbin ‘yanbindiga dauke da mak**ai ya kife yayin da suke kokarin tsallaka wani tafki a yankin.
A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar na tafiya ne a cikin yawa kafin kwale-kwalen ya kife ba zato ba tsammani, lamarin da ya jefa dukkan fasinjojin cikin ruwa.
“Bayanan farko sun nuna cewa da dama daga cikinsu ba su iya iyo ba, wanda ya haddasa yawan mace-mace,” wata majiya ta bayyana.
Rahotannin farko sun nuna cewa babu wanda ya tsira daga cikin fasinjojin, sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaro zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Idan aka tabbatar da faruwar lamarin, ana sa ran hakan zai yi matukar tasiri ga kungiyoyin masu aikata laifuka da ke aiki a wasu sassan yankin Arewa maso Yamma.
16/03/2026
Tinubu ya zaɓi Gwamna Lawal na Zamfara cikin tawogar da za su raka shi ziyara zuwa Burtaniya
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaiyaci Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal domin ya taka shi zuwa Burtaniya, inda zai yi wata gagarumar ziyara zuwa ƙasar.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Suleiman Bala Idris ya aike wa Daily Nigerian Hausa, gwamna Lawal zai bi ayarin shugaban kasa da me dakin da Remi Tinubu da sauran yan tawoga.
Ya ce Sarki Charles ne zai yi wa shugaban kasar tarbar girma a ziyarar ta kwanaki biyu, 18 zuwa 19 ga watan Maris.
Idris ya ce a gobe Talata ake sa ran shugaban ƙasa Tinubu da tawogar ta sa, ciki har da Gwamna Lawal,.za su tashi daga Abuja zuwa Burtaniya.
A cewar Idris, tafiyar za ta taimakawa Gwamna Lawal ya samu damar kulla alaka da masu.zuba jari da ka iya zuwa jihar Zamfara su zuba hannun jari don cigaban jihar.
16/03/2026
Kai Tsaye Daga Garin Shinkafi,Inda Sani Abdullahi Wamban Shinkafi Phd (Lamidon Zurmi Kuma Majidadin Salatin Annabi Muhammad S A W).
Dan Takara Gwamna Jihar Zamfara A Jam'iyar APC 2027.
Ya Sabunta Katin Jam'iyar Sa Ta APC A Mazabarsa Dake Garin Shinkafi.
Wace Fata Zakuyi Masa???
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Culinary Team
Attire
Telephone
Website
Address
Tudun Wada
Gusau