Mus'abmk

Mus'abmk

Share

Change de Chang 2023

Photos 09/02/2017

Ya Allah, Ya Rahman,Ya Aziz, Ya Kayum Ya Zuljalali Wal Ikram Ya Allah Kabawa Wanann Bawa Naka Lafiya Tareda Nisan Kwana Karabashi Daga Sharin Makiya Da Duk Wani Sihiri Da Wasu Suke Yi Don Suga Bayan Wanann Bawa Naka Ya Allah Karka Basu Iko Ya Allah Kasa Yafi Karfin Su Ako Inna Alla Ka Kara Kare Mana Baba Buhari

Photos 24/01/2017

Allah Yaja Kwana Baba

Photos 02/01/2017

Babu Wani Mara Gaskiyar da Zan 'Dagawa 'Kafa Cewar Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta sassautawa duk wanda aka k**a da cin hanci da rashawa ba domin tana nan daram kan 'kudurinta na kawar da almundahana a Najeriya.

Buhari wanda ya ke jawabi a sa'kon taya murnar sabuwar shekara ga 'yan Najeriya ya ce za a binciki duk wad'anda ake zargi da rashin gaskiya da karkatar da abinci da kud'ade'n da aka ware don taimaka wa 'yan gudun hijira da inganta sansanoninsu.

Buhari wanda ya ce makomar 'kasarnan ta dogara kan gwargwadon nasarar da ta samu wajen ya'kar rashawa, ya kuma jaddada aniyarsu ta bin doka da oda wajen yin wannan ya'ki.

Kwanakin baya ne dai sanatoci s**a zargi Sakataren Gwamnatin Buharin da sab'a doka wajen bai wa kamfaninsa kwangila da kuma amfani da ofishinsa wajen ware ma'kudan miliyoyin nairori don sare ciyayi a sansanonin gudun hijira.

Photos 01/01/2017

Yadda zamu inganta Nigeria a 2017 -inji Buhari

A sakonsa ga al'ummar Nijeriya na sabuwar shekarar 2017, Shugaba Muhammad Buhari ya sake jinjinawa sojojin Nigeria bisa kwato dajin Sambisa.

Buhari wanda ya kalubalanci 'Yan Shi'a da kungiyoyin tsageru kan Zaman Lafiya, ya nemi su shiga taitayinsu.

Ko da yake dai mista Buhari ya nemi kungiyar Shi'ar da tsagerun Niger Delta kan su rungumi zaman lafiya tare da bin dokokin kasar a yayin da aka shiga sabuwar shekara amma yace ba za'a lamunci tsageranci ba.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bin hanyoyin yin sulhu da wadannan kungiyoyin inda ya sake rokon mayakan Niger Delta kan su daina fasa bututun mai, su zo a zauna kan teburin zaman lafiya. Sannan sai ya nemi jami'an tsaro su rika mutunta wadannan kungiyoyi a duk lokacin da wata rigima ta hada su.

Haka nan kuma Shugaba Buhari ya jaddada cewa dole 'yan Nigeria su zauna da junansu cikin mutunci da girmamawa yana mai cewa wadannan rukunai biyu ne kadai za su tabbatar da ci gaba da zaman kasar a matsayin dunkulalliyar kasa mai yanci.

Shugaban kasar ya kuma tabbatar da kurakruran da gwamnatinsa ta yi wajen kula da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya rutsa da su inda ya ce za'a gyra a sabuwar shekara.

Ya ce nasarar da aka samu wajen fatattakar mayakan Boko Haram daga hedkwatarsu da ke cikin Dajin Sambisa ya bude sabon faifai a tarihin tsaron lafiya a Nigeria inda ya nemi 'yan Nijeriya kan su sanya ido kan bakin fuska da s**a gani a cikinsu tare da kai rahoto kan duk wani abu da basu gamsu dashi ba ga jami'an tsaro.

Buhari ya kuma bayyana cewa shirinsa na ganin Nigeria na ciyar da kanta, ya fara tasiri musamman yadda a wannan shekarar manoma s**a sami amfanin Gona mai yawan gaske sannan kuma wasu jihohi sun shiga cikin wasu yarjejeniyoyi da bankuna don samar wa manoman jihohinsu rancen noma mai saukin biya.

A karshe, Shugaba Buhari ya sha alwashin kyautata jin dadin yan Nigeria domin cin gajiyar cenjin da s**a zaba. Sannan ya kara da taya Al'ummar Nigeria fatan Alheri na shiga sabuwar shekara ta 2017.

Allah Ya Taimaki Shugaba Muhammadu Buhari
Allah Ya Taimaki Al,ummar Najeriya
Allah Ya Bamu Zaman Lafiya A Kasarmu Najeriya.......Ameen

Photos from Mus'abmk's post 31/12/2016

An Mika Wa Buhari Tutar Shekau Da Al-Qur'ani Da Aka Gano A Dajin Sambisa

Shugaban rundunar Soja na 'Zaman Lafiya Dole', Manjo Janar Lurky Irabor ya mika wa Shugaba Muhammad Buhari ainihin Al-Qurani da tutar da Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ke amfani da su wadda aka gano a Dajin Sambisa bayan fatattakan mayakan kungiyar da sojoji s**a yi.

Sai dai, a yayin karbar tutar wanda aka gudanar a wurin liyafar da rundunar tsaron Fadar Shugaban kasa ta shirya a Abuja, Shugaba Buhari bai ce Uffan ba game da ikirarin Shekau na cewa har yanzu kungiyar na da tasiri a dajin Sambisa.

Photos 29/12/2016

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada hakuri kan rashin Zuwan sa jihar Bauchi
-----------------------------------------------------------------------

A wani sakon waya da kafar LDB ta samu wanda shugaba muhammad Buharin ya kira Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar Esq

Shugaban kasar ya bada hakuri ga Gwamnatin jihar Bauchi da Al'umman jihar Bauchi Kan rashin Zuwan sa a yau 29/12/2016 Sak**akon yanayin sararin samaniya ,

Shugaba Buhari ya ce Kullum kana nakane Ubangiji yana nasa lallai na shirya tsaf Domin ziyaran jihar masoyana Bauchi,

Domin Bude asibiti na san-sanin Sojojin sama da aka Gina tare kuma da kaddamar da wasu Ayyuka da Gwamnan jihar Bauchi yayi,

Amma Sak**akon yanayin Hazo
( weather Report) jami'an mu sun tabbatar jirgi Bazai iya sauka ba Sabila da haka, ina mai Bada hakuri ma Dinbin masoyana na jihar Bauchi tare da Gwamtin jihar Bauchi,

Insha Allah Za'a sanya wani lokaci Domin wan nan ziyaran inzo muga juna
SHUGABAN KASA MUHAMMAD BUHARI

Ga Audio

https://www.facebook.com/groups/1163452897063872/permalink/1239468176129010/

Photos 28/12/2016

Mun sami Nasarori a har kar Noma, an bankado sunayen boge sama da 50,000 sannan gwamnati za ta dauki nauyin katatun 'yan matan Chibok har zuwa Jami'a - BUHARI
-------------------------------

Babban mai taimaka wa shugaban kasa MUHAMMADU BUHARI akan harkar watsa labarai Garba Shehu yace a wannan shekaran gwamnati ta rage asaran da take yi na biyan albashi a kowani wata ga ma'aikatan boge.

Garba Shehu yayi bayanin hakanne a wata ganawa da yayi da 'yan jarida a Abuja.

Yace gwamnati na biyan kudin da ya kai biliyan 200 a kowani wata amma bayan ta gama binciken sahihan ma'aikatan gwamnatin tarayyan sai ta gano cewa sama da ma'aikata 50,000 na boge ne wanda wadansu ne ke amfani da sunayensu domin wawushe kudaden gwamnati sannan gwamnati ta k**a wadansu manyan ma'aikatan ta guda 11 da suke da hannu akan hakan kuma ta mika su ga hukumar EFCC domin a bincikesu.

Garba Shehu ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta zake da sai ta kawar da duk wani irin cin hanci da rashawa a kasar domin kuwa zata cigaba da tantance ma'aikatan ta domin tabbatar da ta gano masu shirya irin wannan aiki da karerayi.

Da yake magana akan ‘yan matan Chibok wanda aka ceto su daga hannun Boko Haram Ya ce gwamnati ta dauki nauyin kula da ‘yan matan amma a yanzu haka mutane da kungiyoyi dayawa da ke kasar nan da wadansu daga kasashen waje sun nuna suna son su dauki nauyin ‘yan matan musammman akan abinda ya shafi karatunsu k**ar wani hanshakin mai kudi mai suna Robert Smith kuma mazaunin kasar Amurka da ya dauki alkawarin biyan kudin makarantar ‘yan matan guda 21 da kuma sauran da sojoji za su ceto har zuwa jami’a, da kuma gidauniyar Murtala Muhammed da ta yi irin wannan tayin.

Duk da haka wasu iyayen ‘yan matan sun koka da yadda ‘yan sandan farar hula ba su bar ‘yan matan sun je gidajen iyayen su ba domin su yi bukin krismati duk da cewa suna cikin garin Chibok.

Shugaban ‘yan sandan farar hulan wato SSS yace dalilin yin haka shine domin sun sami ‘yan matsaloli ne kan tsaron yan matan.

NOMA

Garba Shehu yayi bayanin cewa ganin yadda shugaban kasa ya ke da muradin ganin cewa aikin gona ya dawo da martabarsa a kasa Najeriya a wannan shekaran gwamnati ta taimakawa manoma sannan a na sa ran za'a samu kayan gona wadatacce domin ci da siyarwa a kasa Najeriya da kasashen waje kuma hakan ya farantawa manoma rai domin a yanzu haka sababbin tsaruka da shirye shirye ne gwamnati ta fara domin samun ire-iren wadannan nasarori a damiman badi.

Wani abin da ya farantawa manoma ciki shine yadda gwamnati ta hana shigowa da kayan abinci musamman shinkafa kuma ta shawarci manyan kamfanoni k**ar su Nestle, Unilever da sauran su da su duba su gani ko akwai abin da za su iya amfani da shi wanda kasar ke nomawa a maimakon su siyo a kasashen waje.

Me za kuce akan hakan?

www.premiumtimesng.com

Photos 28/12/2016

Burinsa kenan ganin fuskokin da s**a dade cikin damuwa da tashin hankali sun samu fara,a da murmusi a cikknsu...

Tun bayan da aka samu nasarar kawar da kungiyar Boko Haram daga cikin dajin sambisa fuskar Shugaba Muhammadu Buhari take cikin farin ciki da annushuwa, ba saboda siyasa yake wannan murnar ba, sanin cewa yanzu miliyoyin fuskoki ne s**a kasance cikin murna da wannan labarin, hakan ne ya sanya shima tasa fuskar take cikin farin ciki da annushuwa....

Nan gaba zai kara kasancewa cikin wata murnar da annushuwa lokacin da al,umma s**a samu kansa cikin rayuwa mai nutsuwa kuma mai sauki, shinkafa ta dena tayar da hankalin al,umma, kayan masarufi su dena takurawa mutane da tsadar ba gaira ba dalili, nan gaba idan Dollar ta dena tashin gwauron zabin da takeyi, hakan zai kara sanyawa fuskar baba ta kasance cikin Annushuwa.....

Baba zaiyi nasara In sha Allah.....

Photos 27/12/2016

Obasanjo, Yar Adua Da Jonathan Sun Girgiza Buhari...

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya girgiza matukar gaske sak**akon gano yadda tun daga shekarar 1999 zuwa 2014 tsoffin shugabannin Najeriya
Obasanjo,

Yar Adua da Jonathan gaba daya kudin shigar da aka samu daga man fetur a abinci s**a tafi.

Want your establishment to be the top-listed Bar/pub in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe