Bitkova Digital Hub
Waye Mu?
Bitkova dandamali ne na ilimiwanda aka kirkira don taimakawa daidaikun mutane wajen koyan ilimin fasahar zamani kamar daura talla akan kafafen sada zumunta, kasuwancin Crypto currency ko forex, gina manhajoji akan kafar Blockchain Bitkova dandamali ne na ilimi wanda aka kirkira don taimakawa daidaikun mutane wajen koyan ilimin fasahar zamani kamar daura talla akan kafafen sada zumunta, kasuwancin
20/03/2026
Sunnonin Sallar Eidul Fitr da Yakamata mu sani.
Yakai ɗan uwa mai albarka kayi ƙoƙarin domin dacewa da sunnar fiyayyen halitta Annabi Muhammad ﷺ gobe ranar Eidin Sallar Azumi ka lizimci waɗannan abubuwan domin samun ladar koyi da Annabi Muhammad ﷺ, gasu kamar hakan:
1⃣Wanka Domin Sallar Eid
(الموطأ للإمام مالک 432)
2⃣ Sanya turare, Sanya Tufafi masu kyau.
(المطالب العالیة 1:85)
3⃣Cin Abinci kafin Zuwa Sallar Eidi (Eidil Fitr)
( صحیح البخاری 953)
4⃣Tafiya Kasa Zuwa Eidi
(530 سنن الترمذی)
5⃣ Sauraron Khudubah bayan gama Sallar Eidi
( صحیح سنن ابن ماجه1073 )
6⃣Chanza Hanya yayin dawowa daga Sallar Eidi
(صحیح البخاری 986)
7⃣ Addu'o'in yayin Haduwa da mutane
" تقبل الله منا و منکم"
(مسند الإمام أحمد)
8⃣ Nuna farin ciki da Nishadi
(صحیح مسلم)
Domin samun lada daga Allah kuyi sharing ɗinsa domin ƴan uwa su amfana. Allah ya karɓa mana.
Rubutawa da gabatarwa
©️ Engr Aliyu Almustapha
19/03/2026
Registration na 2026A Cohort yana ci gaba da wakana
Yanzu haka ana kan Registration na ajin 2026 har zuwa ranar
Asabar, 28th March daga nan za a rufe domin shirye shiryen fara karatu
Ranar fara karatu zai kasan ce Asabar, 4th April Insha Allah
Idan kana son koyon Crypto Trading da yaren Hausa cikin sauki kuma yanda zaka fahimta, wannan babbar damace gare ka
Karku bari lokaci ya wuce muku
Domin yin register garzaya shafin mu
www.bitkova.com
Ko kuma ku tuntube mu ta wannan number
+2347070073670
Bitkova Academy makarantar ku abin alfaharin ku
16/03/2026
Assalamu alaikum,
Zamu ci gaba da registration na ajin 2026A na Bitkova Academy har zuwa Asabar 28th March.
Bayan wannan rana, za a rufe rajista gaba ɗaya.
📅 Asabar 4th April – shi ne ranar da ajin 2026A Cohort zai fara karatu.
Idan kana son koyon Cryptocurrency, Trading, da damar Web3, wannan shi ne lokacin da ya dace ka shiga.
Kar ka bari a baka labari. Link na registration yana kasa.
Bitkova Academy
Makarantarku, abin alfaharinku 💙
14/03/2026
Ramadan Reminder| Day 25
Manzon Allah ﷺ ya ce:
Azumi da Al-Qur’ani za su yi ceto ga bawa a Ranar Alƙiyama.
Azumi zai ce:
“Ya Ubangiji! Na hana shi abinci da sha’awa da rana, ka ba ni izinin in yi masa ceto.”
Al-Qur’ani kuma zai ce:
“Ya Ubangiji! Na hana shi barci da dare saboda yana karantani, ka ba ni izinin in yi masa ceto.”
Sai Allah Ya ba su izinin su yi masa ceton.
(Sahih Jam'i 3882)
Ma’ana a takaice:
Wannan hadisin yana nuna cewa azumi da karatun Al-Qur’ani ibadu ne masu girman lada, har ma za su tsaya su kare mutum a Ranar Alƙiyama.
Darussa daga hadisin:
Azumi ibada ce da za ta yi ceto ga mutum a lahira.
Karatun Al-Qur’ani musamman a Ramadan yana da babbar lada.
Hada azumi da karatun Al-Qur’ani yana daga cikin manyan ayyukan Ramadan.
Allah ya sa azuminmu da karatun Al-Qur’aninmu su zama dalilin cetonmu a Ranar Alƙiyama.
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌍https://bitkova.com/our-hub
13/03/2026
Ramadan Reminder | Day 24
Manzon Allah ﷺ ya ce: Allah Ya ƙasƙantar da mutumin da Ramadan ya zo masa, sannan watan ya wuce bai samu gafarar Allah ba.
(Sunan al-Tirmidhi 3545)
Ma’anar Hadisin:
Ramadan wata ne na rahama da gafara. Allah yana ba bayinsa dama su tuba, su ƙara ibada, su nemi gafara. Idan mutum ya samu wannan wata amma bai yi anfani da shi ba, wannan babban hasara ne gare shi.
Darussa daga hadisin:
1️⃣ Ramadan babbar dama ce ta neman gafarar Allah.
2️⃣ Kada mu yi sakaci da ibada, sallah, Qur’ani, azumi da addu’a a watan Ramadan
3️⃣ Lokaci yana wucewa da sauri, don haka a yi anfani da Ramadan kafin ya ƙare.
4️⃣ Babbar hasara ne mutum ya rasa gafara a wannan wata mai albarka.
Allah Ya sa mu dace da samun gafararSa a Ramadan.
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌍https://bitkova.com/our-hub
13/03/2026
Allah ya karɓi ibadunmu yasa muna cikin mutanen da za'a ƴanta daga wuta zuwa aljanna a cikin wannan wata mai albarka.
Shigo Bitkova Academy domin samun ingantaccen ilimin zamani da gogewa daga ƙwararrun Malamai.
🌍https://bitkova.com/our-hub
Bitkova Academy,
Makarantar ku, abin alfaharinku
13/03/2026
Alhamdulillah, ina cikin tsananin farin ciki.
Bitkova Academy ta zamo gidan alkhairi.
Ga ilimin cryptocurrency, ga Ramadan with Habibi.
Gaskiya, wannan an masa Bull run ɗinsa.
Allah ya kaimu lokaci.
12/03/2026
Ramadan Reminder | Day 23
An karɓo daga Ibn Abbas (RA) ya ce:
Manzon Allah ﷺ shi ne mafi kyauta a cikin mutane. Kuma yakan fi yawan kyauta a watan Ramadan, lokacin da Mala’ika Jibrilu yake zuwa wajensa. Jibrilu yana zuwa wajensa kowace dare a Ramadan, suna karanta Al-Qur’ani tare. Saboda haka Manzon Allah ﷺ ya fi iska mai gudu wajen yawaita alheri da kyauta.
Sahih Bukhari hadith mai lamba ta 3554
Ma’anar Hadisin:
Hadisin yana nuna cewa kusanci da Al-Qur’ani da yawaita ibada yana ƙara wa mutum son yin alheri da taimakon mutane. Shi ya sa Manzon Allah ﷺ yake ƙara karamci sosai a Ramadan.
Darussa daga Hadisin:
Ramadan lokaci ne na ƙara sadaka da taimako ga mutane.
Karatun Al-Qur’ani yana gyara zuciya kuma yana ƙara son alheri.
Ya kamata mu koyi karamci da halin Manzon Allah ﷺ musamman a wannan wata.
Allah ya sa mu zama masu yawan alheri a Ramadan. 🤲
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌍https://bitkova.com/our-hub
11/03/2026
Ramadan Reminder| Day 22
Daga Abdullah ibn Umar (Allah Ya yarda da su duka) ya ce:
“Manzon Allah ﷺ yana yin ’itakafi a cikin kwanaki goman ƙarshe na Ramadan.”
Ma’anar hadisin a taƙaice:
Ikaaf shine zama a masallaci don tsarkake lokaci daga duk abin duniya, yin ibada, addu’a, karatun Alƙur’ani, da tunani game da Allah.
Darussa 3 daga wannan hadisi:
1. Muhimmancin kwanaki goma na ƙarshe: Wannan hadisi yana nuna cewa Manzon Allah ﷺ yana mai da hankali sosai a cikin kwanaki goma na ƙarshe, domin samun lada da kusantar Allah.
2. Tsarkake lokaci don Allah: Yin ikaaf yana koya mana yadda mu ware lokaci na musamman don ibada, nesa da duniya da damuwarta.
3. Ilimi da ibada tare: Ta hanyar kasancewa cikin ikaaf, mutum yana ƙara karatun Alƙur’ani, addu’a, da tsarkake zuciya, wanda yake ƙarfafa dangantaka da Allah.
Allah Ya sa mu dace da wannan lada a cikin kwanaki goma na ƙarshe.
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌎https://bitkova.com/our-hub
10/03/2026
Ramadan Reminder | Day 21
Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ce:
“Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya shiga kwanaki goma na ƙarshe na Ramadan, yana ƙara ƙaimi wajen ibada, yana tsarkake kansa, yana tashi da dare yana yin ibada, kuma yana tashe iyalinsa su yi ibada tare da shi.”
Bukhari ne ya ruwaito shi
Bukhari 2024.
Ma’ana a taƙaice:
Lokacin kwanaki goma na ƙarshe na Ramadan, Manzon Allah ﷺ yana ƙoƙari sosai wajen tsarkake zuciya da jiki, yana tashi dare yana salla da addu’a, kuma yana ƙarfafa iyalinsa su yi haka tare da shi. Wannan yana nuna mana muhimmancin ƙoƙari da himma a cikin kwanaki goma na ƙarshe.
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌎 https://bitkova.com/our-hub
09/03/2026
Ramadan Reminder| Day 20
Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ruwaito cewa Manzon Allah ﷺ ya ce: “Ku nemi Lailatul Qadri a dararen witiri (21, 23, 25, 27, 29) na kwanaki goma na ƙarshe na watan Ramadan.”
Bukhari ne ya ruwaito shi.
Bukhari 2017
Ma’ana a taƙaice:
Manzon Allah ﷺ yana umartar mu da mu yi ƙoƙari sosai wajen neman Lailatul Qadri, musamman a dararen witiri daga cikin kwanaki goma na ƙarshe na Ramadan, domin a can ne mafi yawan yiwuwar samun ta.
Allah Ya ba mu dacewa da cin ribar wannan dare mai albarka.
Kada ku manta muna cigaba da registration na Ajin Cryptocurrency 2026A
🌎https://bitkova.com/our-hub
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
Gombe