Jewel Update

Jewel Update

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Jewel Update, Media/News Company, Gombe.

Jewel Updates is a Modern Media and Technology Company Providing Digital Media, Content Creation, News and Information, Digital Marketing, Technology Solutions, and Digital Skills Development.

18/09/2026

Mutuwar tarin alumma Jihar Naija ya ta da hankali matuka..!

18/09/2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta tura jami’ai da kayan aiki na musamman zuwa ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye, gabanin zaɓen cike gurbin Majalisar Wakilai da za a gudanar ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar ranar Juma’a, rundunar ta ce an tura jami’ai zuwa ofisoshin INEC, cibiyoyin tattara sak**ako, rumfunan zaɓe da sauran muhimman wurare.

Rundunar ta kuma sanar da takaita zirga-zirga da rufe harkokin kasuwanci daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a ranar zaɓe, sai dai ayyukan da s**a shafi muhimman hidimomi.

Sai dai ta ce ma’aikatan ayyukan gaggawa ba za su yi amfani da ƙararrawar mota, motocin da ba su da rajista ko motocin da aka rufe lambobin rajistarsu ba.

’Yan sanda sun bayyana cewa jami’an tsaro na doka da aka amince da su ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Tsaron Zaɓe (ICCES) ne kaɗai za su samar da tsaro a lokacin zaɓen.

Sun kuma hana ƙungiyoyin tsaro na sa-kai, jami’an tsaro masu zaman kansu da sauran ƙungiyoyin da ba na hukuma ba shiga aikin tsaron zaɓen.

Rundunar ta gargaɗi ’yan siyasa da jama’a kan yaɗa labaran ƙarya, tayar da tarzoma, ɗaukar mak**ai ko mallakar abubuwan da za su iya jawo matsala a rumfunan zaɓe.

Ta kuma yi kira ga iyaye da masu kula da matasa da su hana ’ya’yansu shiga harkar daba ko a yi amfani da su wajen tayar da rikici.

Rundunar ta ce za ta k**a tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana aikata abin da zai kawo cikas ga gudanar da zaɓen cikin lumana.

Ta buƙaci mazauna ƙananan hukumomin da abin ya shafa su ba jami’an tsaro haɗin kai, tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

18/09/2026

Rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta hana zirga-zirga da rufe harkokin kasuwanci a ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye, gabanin zaɓen cike gurbi na mazabar tarayya ta Gombe/Kwami/Funakaye da za a gudanar ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026.

Rundunar ta ce dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma, sai dai ga masu gudanar da muhimman ayyuka.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an ɗauki matakan tsaro domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana, sahihanci da kuma ba tare da tashin hankali ba.

Sanarwar ta ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ya bayar da umarnin tura isassun jami’an tsaro da kayan aiki zuwa ofisoshin INEC, cibiyoyin tattara sak**akon zaɓe, rumfunan zaɓe da sauran muhimman wurare a ƙananan hukumomin da abin ya shafa.

Rundunar ta kuma bayyana cewa waɗanda ke gudanar da muhimman ayyuka ba za su yi amfani da sirens, motocin da ba su da rajista ko kuma motocin da aka rufe lambobin rajistarsu ba.

Haka kuma, ta ce hukumomin tsaro na doka da ke ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Tsaron Zaɓe (ICCES) ne kaɗai aka ba izinin samar da tsaro a lokacin zaɓen, yayin da ƙungiyoyin tsaro na gwamnati, masu zaman kansu da kungiyoyin sa-kai ba su cikin waɗanda aka amince da su.

Rundunar ta yi gargaɗi kan yaɗa labaran ƙarya, daba, nuna mak**ai da kuma ɗaukar abubuwan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya a rumfunan zaɓe.

Ta kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su hana amfani da ’ya’yansu wajen aikata daba ko tashin hankali na siyasa.

Rundunar ta ce za ta k**a tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana aikata wani abu da zai kawo cikas ga gudanar da zaɓen cikin lumana.

Ta buƙaci jama’a da su ba jami’an tsaro haɗin kai tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa ko ta lambobin gaggawa 08150567771 da 09036435359.

18/09/2026

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta raba kayan zaɓe masu muhimmanci zuwa ƙananan hukumomi uku da za su gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai ta tarayya mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye.

An raba kayan ne ranar Juma’a a harabar Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Gombe, a gaban wakilan jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Zaɓen da za a gudanar ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, na da masu rajistar zaɓe 495,851 da ake sa ran za su kada ƙuri’a a faɗin mazaɓar.

Kwamishinan Zaɓe na jihar Gombe, Alhaji Umar Muktar Gajiram, ya ce an raba kayan zuwa ƙananan hukumomin da abin ya shafa domin a kai su rumfunan zaɓe.

Ya bayyana cewa an gudanar da rabon kayan a fili, tare da halartar masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da gaskiya da ƙara amincewar jama’a kan tsarin zaɓen.

Gajiram ya yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da s**a rattaba hannu a kai.

Ya ce zaman lafiya a lokacin zaɓe nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa, ba INEC kaɗai ba, yana mai buƙatar dukkan ɓangarori su tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana da tsari.

17/09/2026

"Bakayiwa Iyayenka Mugu Zato Ba, Baka Yiwa Iyayen Mahaifan ka Mugun Zato ba, Sai Iyayen Manzon Allah? " - Shaik Sani Yahaya Jingir

16/09/2026

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bai wa Maryam Ibrahim Dan’Azumi, wadda ta lashe gasar karatun Alƙur’ani ta duniya a rukunin mata, kyautar ₦20 miliyan.

Maryam ta lashe gasar King Abdulaziz International Qur’anic Competition da aka gudanar a Makka, Saudi Arabia.

A wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Talata, Oluremi Tinubu ta yaba wa Maryam bisa wannan gagarumar nasara, inda ta bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga Najeriya da kuma abin ƙarfafa gwiwa ga ’ya’ya mata.

Maryam ta halarci taron tare da mahaifinta, Ibrahim Dan’Azumi, da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da wasu jami’an gwamnatin jihar.

Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma yaba wa iyayen Maryam da malamanta da masu ba ta shawara, bisa gudunmawar da s**a bayar wajen iliminta da haɓaka baiwar da Allah ya ba ta.

Ta kuma bayyana cewa za ta taimaka wa Maryam wajen neman ci gaba da karatunta har zuwa matakin digiri na gaba.

Haka kuma, Oluremi Tinubu ta tuno da ƙanwar Maryam, Hajara Ibrahim Dan’Azumi, wadda ita ma ta lashe wata babbar gasar karatun Alƙur’ani ta duniya a Jordan a shekarar 2024.

A nasa jawabin, Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana nasarar Maryam a matsayin abin alfahari ga jihar Gombe da Najeriya, yana mai cewa ta fara samun nasarori ne daga gasannin cikin gida kafin ta kai matakin gasar duniya.

Da take jawabi, Maryam ta gode wa Uwargidan Shugaban Ƙasa bisa karramawar da ta yi mata, tana mai cewa gasar Saudi Arabia ta ba ta damar samun ƙwarewa da kuma gogewa a matakin duniya.

Ta kuma bayyana fatan cewa nasarar da ta samu za ta ƙarfafa sauran matasa ’yan Najeriya su dage wajen neman ilimi da haɓaka baiwarsu.

15/09/2026

Da Ga Ficeccen Malamin Addinin Musulunci Shaik Nuru Khalid daya fita daga addinin Musulunci ya dawo

15/09/2026

With Abba Sani Pantami – I just made it onto their weekly engagement list by being one of their top engagers! 🎉

15/09/2026

Wata kotu a Iraƙi ta yanke wa wani mahaui hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 10, bayan k**a shi da kilo 75 na naman alade da yake sayar wa mutane a matsayin naman sa a birnin Najaf.

Majalisar Shari’a ta Ƙoli ta Iraƙi ta ce Kotun Manyan Laifuka ta Najaf ta same shi da laifin sayar da naman da bai dace da lafiyar ɗan Adam ba.

Najaf na daga cikin biranen da Musulmi ’yan Shi’a ke ɗauka a matsayin masu tsarki, kuma birnin na karɓar miliyoyin mahajjata da masu ziyara a kowace shekara.

Rahotanni sun ce mahaucin, wanda aka k**a a farkon watan Satumba, ya riƙa sayar da naman aladen ne a matsayin naman sa.

Kotun ta dogara da wata doka ta shekarar 1998 da ta haramta sayar da naman kare, jaki ko wasu nau’o’in nama da ba su dace da cin ɗan Adam ba.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, yayin da wasu mazauna Najaf s**a bayyana cewa sun daɗe suna sayen naman daga wajen mahaucin ba tare da sanin cewa naman alade ba ne.

© Aminiya

15/09/2026

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da ya tabbatar da sakin dukkan kuɗaɗen da aka ware wa kwamitocin raya yankuna a kan lokaci.

Tinubu ya bayar da umarnin ne a taron North Central Development Commission da aka gudanar ranar Litinin, inda ya ce gwamnati za ta ci gaba da bai wa kwamitocin goyon bayan kuɗi da na siyasa domin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.

Sai dai shugaban ya bukaci kwamitocin da kada su dogara da kuɗin gwamnati kaɗai, yana mai ba su shawarar su nemi haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin bayar da tallafi da cibiyoyin samar da kuɗaɗen raya ƙasa.

Ya ce ya k**ata a mayar da hankali kan ayyukan layin dogo, sufuri ta jiragen sama, masana’antu, tsaro, zuba jari, ilimi, kiwon lafiya da bunƙasa ƙwarewar matasa.

Tinubu ya kuma gargaɗi shugabannin kwamitocin kan cin hanci, wariya, siyasantar da ayyukan raya ƙasa da kuma almundahana da dukiyar gwamnati, yana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, Abdullahi Sule, ya ce yankin na da isassun albarkatun ƙasa da na ɗan Adam da za su iya bunƙasa tattalin arzikinsa.

Sule ya jaddada cewa bai k**ata a tsaya ga haƙo albarkatun ƙasa kawai ba, sai an sarrafa su a cikin yankin domin ƙara musu daraja da samar da ayyukan yi.

Want your business to be the top-listed Media Company in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Gombe
1238

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jewel Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Gombe.