Muhammad nuru

Muhammad nuru

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muhammad nuru, College & University, Gombe.

28/07/2025
31/10/2024

SAKO ZUWA GA IYAYE:
Duk yadda ka kai wajen yiwa danka nasiha, ka sani zai dauki kadan ne cikin maganganun ka yayi aiki dasu

Amma tabbas yaran ka zasu dauki da yawa cikin aiyukan ka wadda baka ce suyi ba, wato abinda s**a ga iyayen su nayi a aikace

Yara suna koyi da hali da dabi'un iyayen su, don haka muyi hattara wajen yin abinda yara zasu koya daga garemu

Dan haka ake so iyaye su zamo masu nagarta, kuma masu kyak-kyawan hali abin koyi ga yayan su.

Mu sani hatta kula da ibada, sada zumunci, kame harshe daga aibata mutane, lizimtar jin wa'azi da zuwa wurarwen karatu, girmama baki, son muatnen kirki duk yaran la na koyi dashi

Haka nan yara na tasirantuwa da dabi'ar kwadayi da son duniya, kiyaye kai daga karya da alfahari, nisantar bokaye, ko jin kida da waka da sanya tufafi daga iyayen su

Hatta juriyar da tawakkalli da kan-kan da kai, kyauta da taimakawa rayuwar wani duk yaran mu na koya daga garemu

Hakika in da kafar gaba ta taka nan ta baya ke takawa, kuma in bishiya ta karkace inuwar ta bata Mikewa. Mu daina mamakin dabi'ar wassu daga cikin mu.. kowa ka duba wa ya haife shi?

Mu duba yadda addini ya nusar damu kan za6ar miji ko mata ta gari don mu samu rayuwa mai dadi da zuriya tagari, don tsatso Yana naso

Ya Allah Muna rokon ka shiryar mana da zuriya kayi masu albarka ka bamu dacewa duniya da lahira, amin

Want your university to be the top-listed University in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Gombe