YouKay Media Stream

YouKay Media Stream

Share

Elevating businesses through innovative digital media strategies, creating engaging experiences that resonate with your target market. RC -8516635

05/12/2025

Alh. Ahmad Muhammad Sani CON @45 .
Allah ya karawa Sarki lafia ...

01/12/2025

A watan July 2026 kowace jam'iyya za ta gudanar da zaben Primary Election.

Tun a watan February 2026, kuma duk mai rike da wani mukamin gwamnati da yake son zai yi takara zai ajiye mukaminsa, in ji hukumar zabe ta kasa (INEC).

01/12/2025

A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaba Tinubu a ranar Litinin, Badaru Abubakar ya ce ya sauka daga muƙamin nasa ne saboda dalilin da ya shafi lafiyarsa.

Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin da ministan ya yi, kuma zai sanar da wanda zai maye gurbinsa a makon nan.

Photos from Sawaba FM 104.9 Hadejia's post 29/11/2025
28/11/2025

A wani rahoton da Sahara Reporters ta fitar, ya nuna cewa gwamnatin Jihar Jigawa ta ware Naira miliyan 800m domin gina da kuma kayayyata masaukin shugaban kasa (Presidential Wing) a fadar Gwamnatin Jiha, da kuma Naira miliyan 50m don gina sabon wajen wanki da guga (laundry facility) na Gwamna.

Binciken ya kuma gano cewa tsakanin Janairu zuwa Satumbar 2025, an kashe Naira miliyan 672 wajen siyan motocin gidan gwamnati, ciki har da Naira miliyan 437 da aka kashe cikin watanni uku kacal (Yuli–Satumba).

Rahoton ya kuma ce an samu sabbin motocin alfarma a fadar gwamnati, duk da cewa gwamnati ta musanta cewa an sayi sabbin motoci, tana cewa Gwamna Namadi har yanzu yana amfani da tsoffin motocin da ya gada.

Jam’iyyar APC ta bayyana rahoton a matsayin jita-jita ne, yayin da wasu majiyoyi ke zargin cewa kudaden siyan motocin sun yi yawa fiye da kima kuma an yi amfani da gurbatacciyar hanya wajen gudanar da kwangilolin.

Har yanzu ba a sani ba ko nawa za a ƙara kashewa kan motocin gidan gwamnati kafin ƙarshen shekarar 2025.

26/11/2025

Did you ever see a driverless car ?

26/11/2025
26/11/2025

Wata Sabuwa !!

Dan majalisar tarayya Hon Ahmed Idris Wase ya gabatar da korafi akan umarnin Shugaban Kasa Tinubu na janye 'yan sanda daga bawa manyan mutane (VIP) kariya

Hon Ahmad yace sakamakon wannan umarni na Shugaban Kasa Tinubu ya jefa rayuwar manyan mutane da 'yan siyasa cikin barazana, saboda masu garkuwa da mutane sunce zasu fara kamasu da zaran an janye 'yan sanda

Har zuwa yanzu akwai manyan 'yan siyasa da basu bari an janye 'yan sanda daga jikinsu ba, wasu suna ganin cewa Civil Defense basu da horon da zasu iya basu kariya

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Dutse?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address


Yalwawa Quaters Bypass Dutse
Dutse
0234