Syed Abdullahi m Inuwa

Syed Abdullahi m Inuwa

Share

SAYING OF AHLUL BAYT (AS)

09/12/2025

Wannan shine Ayatullahi Sayyid Mujtaba Al-Hussain (Wakilin Sayyid Ali Khamna'i ne na ƙasar Iraqi) a jiya ya sake bayyana da'awa da manufar ƴan gwagwarmayar tabbatar da addinin musulunci tun daga Imam Khumaini da Sayyid Ali Khamna'i da su Sayyid Hassan Nas**rullah har kawo kan Sayyid Zakzaky (H).!

Ya ce Imam Khumaini (Q.S) bai taɓa kira zuwa ga Shi'anci ba shi yayi kira ne zuwa ga tabbatar da tsarin Musulunci ya zama shi ke iko a doron Ƙasa, A ƙarƙashin haka mutane s**a bi shi sannan dayawa sun zama ƴan Shi'a ne saboda kyawawan ɗabi'unsa, haka Sayyid Hassan Nasa**rallah ya gudanar da rayuwar sa har yayi Shahada, Hadafinsa shine kishin Musulunci tare da taimakon raunana batare da yi musu tayin yin Shi'a ba.! A Nigeria ma hakan Sheikh Zakzaky (H) hakan yasa Miliyoyin mutane su zama ƴan'uwa cikin lalama s**a rungumi Mazahabar iyalan Manzon Allah (s.a.w.w).!

Jiya kenan 8/12/2025 da yake ganawa da Muballigai daga ƙasashe Ma banbanta.!

04/12/2025

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Rayuwa duniya tamkar mafarki ce, amma mutuwa gaskiya ce. Dukkan mai rai zai dandani mutuwa, kuma babu wani lokaci da zai wuce idan lokaci yayi. Yau shekara guda kenan da rasuwarta, amma kamar yau ne. Murmushinta, halayyarta, da kaunarta – har yanzu suna zaune a zuciyoyinmu. Ta bar rabo, amma ba ta bar zamu manta da ita ba.
Mun yarda da ƙaddarar Allah, kuma muna roƙonSa da ya sa ta cikin bayinSa na gari, ya azurta ta da hutu cikin kabari, ya cika kabarinta da haske, rahma, da jinƙai. Muna roƙon Allah da ya haɗa mu da ita a cikin Aljannatul Firdaus in sha Allah.

01/12/2025

I'm not a Nigeria 🇳🇬 or a Kenyan 🇰🇪 or a Niger 🇳🇪 nor a South African 🇿🇦 or cameroon 🇨🇲. I'm an African and that is what I want to be. ✊🏾

Photos from Syed Abdullahi m Inuwa's post 01/12/2025

Malam dabbobin daji sun ga ta kan su. Nan fa da ka ke gani kwarangwal din kawunan dabbar Bison ne cunkus. Ana maganar fiye da kwarangwal dubu hamsin, kaga kenan dabbobi dubu hamsin kenan.

Shekaru dari biyu da s**a shude, akwai miliyoyin dabbar Bison da ke rayuwa a nahiyar Amurka amma an farauce su fiye da kima wanda yai sanadiyar ƙarancin su matuƙa, wanda dabbobin da s**a rage ƙasa da dari ne a gandun dajin Yellowstone na ƙasar Amurka.

Sakamakon haka, a shekarar 1885, 'yan majalisun ƙasar Amurka s**a rattaba hannu a dokar da ta hana farautar Bison wanda sakamakon haka ne dabbar ta farfado daga gushewa daga doran ƙasa.

A yanzu, akwai kusan Bison rabin miliyan daya da suke rayuwa a gandun dajin Yellowstone na ƙasar Amurka.

Manyan abubuwan da s**a janyo ƙarancin su shine matsananciyar farauta da kuma dokar da ƙasar Amurka ta saka na farautar su don kada mutanen Indiya 'yan asalin ƙasar Amurka, wato native Indians su samu abincin ci, wanda wannan dabbar itace babban abincin su domin kawar dasu daga ƙasar.

01/12/2025

Duk Almajirin Malam Zakzaky to Ɗalibin Hauza ne.!

Indai za ka saurari Tafsirin Malam ka ji an Halatta an Haramta an an kawo litattafai na ruwaya ko na hukunce hukuncen a fiƙihu ko a karanto ma sahihin tarihin Annabi (S) da Iyalan gidan sa, to za ka ji duk yana karantowa ne daga litattafan Maraji'an Hauza ne. Malam Zakzaky yana taƙalidi da Sayyid Ali khamna'i shi kuma Sayyid Ali khamna'i kafin ya zama Marji'i yana taƙalidi da Imam Khumaini kuma dukkan su Hauza ce ta haife su.! Mu kuma wanna ilimin nasu Malam yake bamu.!

Malam Zakzaky a jawaban da da Tafsiran sa yana yawan ce wa a tashi a nemi ilimin a je a naɗe ƙafa a nemi karatu. Wlh sai da na ɗan fara karatu a nan sannan na gane ashe iya jin wannan karatun a gaban Malam ya ishe cikakken ilimi duniya da lahira, wannan Hauzar da ke a gaban Malam Zakzaky yana koyarwa wlh a yanzu dai banga wata Hauza da ta kai ta bayar da tantagaryar tataccen Ilimi ba. To Malam ne fa a karatu sai ya niƙa maka ya tankaɗe ya dafa ya zuba a kwano ya saka ma a baki. Wlh duk wanda ya zauna a gaban Malam aka yi tafsirin Alqur'ani da shi har aka sauke, to a yi masa Rawanin Hauza don ya cancanta.

In ji Husaini Ahmad.

27/11/2025

__Daga hagu Sheikh Sayyid Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H) ne, a dama Marhum Sheikh Ɗahir Usman Bauchi (RH) ne, a wata ziyara da Sayyid Zakzaky (H) Ya kai wa Shehi shekaru masu tsawo, zai iya kasancewa cikin Shekarun 80s, Allah Ta'alah Ya jiƙan Shehi Ɗahiru Bauchi, Ya ƙara wa Sayyid Zakzaky (H) da tsawon rayuwa 🤲🏾

27/11/2025

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

05/11/2025

Cin zaɓen Zohran Mamdani ba wata tsiya ba ce dan Allah. Musulmi ne ɗan Shi'a kamar yadda Shah Reza Pahlawi ya ke Musulmi ɗan Shi'a. Zohran ɗan juma ne da ɗan jummai shi da su Trump.

A wajen Zohran Hamas ƙungiyar ta'adda ce, Dufanan Aƙsa ma aikin ta'addanci ne, ƙasashen Venezuela da Columbia mulkin danniya ake yi. Ya na da aƙidar yarda da ƴancin ƴan luwadi da madigo wato LGBTQ.

Ni kam mai waɗannan mugayen aƙidun ko a Vatican ya ci zaɓe, fuska zan yi kamar ban san ya ci ba. Ɗan Democrat ne, masu aƙidar yaɗawa da taimakon ƴan LGBTQ, irinsu Obama da su Biden, ba wani abin murna a wajena.

Mun manta da me ke shugabanci, ba wa ke shugabanci ba!

Photos from Syed Abdullahi m Inuwa's post 05/11/2025

Tunawa Da Shahadar Sayyidah Zahra (As)

Dubban Musulmai Muminai Sun Cika Gidan Sayyadina Ali Domin Mika Jajen su da Tuna ranar da wasu la'anannu s**a Shahadantar da matarsa ɗiyar Annabin Rahama Fatima (As).

Allah ka la'anci wanda s**a kashe Nana Fatima👏

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Bauchi

Opening Hours

Monday 12:00 - 00:00
Tuesday 12:00 - 11:00
Wednesday 12:00 - 00:00
Thursday 12:00 - 11:00
Friday 12:00 - 17:00
Saturday 12:00 - 17:00
Sunday 12:00 - 17:00