Awafss. TV

Awafss. TV

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Awafss. TV, TV Channel, Unguwan bauchin bauchi nuru quaters bauchi, Bauchi.

ALKITABU WASSUNNAH ALA FAHAMI SALAFUSSALIH (AWAFSS)

📖 Kiran Al-Qur’ani da Sunnah
🕌 A kan fahimtar Salafussalih
🎓 Ilimi • Tarbiyya • Da’awah
🤝 Haɗin kai da gyaran al’umma
📍 Bauchi State, Nigeria

Manufa: Isar da sahihin ilimi da inganta tarbiyya bisa

27/08/2026

DUNIYA A ADABIN HAUSAWA (RANAR HAUSA)

Hausawa sun yi amfani da hikima da karin magana wajen bayyana hakikanin rayuwar duniya. Ga wasu daga cikin maganganunsu:

1. Duniya mai ya yi.

2. Duniya budurwar wawa.

3. Duniya makaranta ce.

4. Duniya makwantar rikici.

5. Duniya a bita a sannu.

6. Duniya mai ban mamaki.

7. Duniya ba ta rago ba ce.

8. Duniya ba matabbata ba ce.

9. Duniya gidan kashe ahu ce.

10. Duniya ce, gashi nan ga ta.

11. Duniya mu bita a sannu, domin mai ɗauka tana ajiyewa ce.

12. Duniya sai da karatunta nutsu.

13. Duniya masakin kunu ce; ɗan Adam ya ɗanɗana ta a hankali.

14. Duniya gidan hira ce.

15. Duniya kamar shiga ɗakin mota ce: shiga da kai, fitowa da baya.

16. Duniya rumfar kara ce.

17. Duniya da wuya zama.

18. Duniyar wasu aljannar wasu ce.

19. Duniya da daɗi, a kan bar ta.

20. Duniya ta fi ƙarfin babu.

21. Duniya ƙwallon mangwaro ce.

22. Duniya rawar yammata ce.

23. Duniya a ido take; an saya da uwa, an saya kwalli.

24. Duniya birgimar hankaka ce: ka ga baki, ka ga fari.

25. Duniya ce ta fi bagaruwa iya jima.

26. Duniya juyi-juyi ce; ƙwado ya faɗa ruwan zafi.

27. Duniya mai ɗauka da ajewa.

28. Duniya uwar rufi ce; ko ba ki son mutum, ya sani.

29. Duniya mai ido a tsakarka ce, ba ki ganin gabanki.

30 Duniya, ina zaki da mu ne?

Darasin da ke cikin waɗannan maganganun

Waɗannan hikimomin suna tunatar da mu cewa:

Duniya ba madawwama ba ce.

Rayuwa tana cike da sauye-sauye.

Farin ciki da baƙin ciki suna bin juna.

Kada mutum ya yi girman kai saboda abin da yake da shi.

Kada talauci ko wata jarabawa ta sa mutum ya yanke ƙauna.

Ya kamata mutum ya yi amfani da lokacin duniya wajen aikata alheri.

Ya kamata mu yi rayuwa cikin haƙuri, hankali da tawakkali.

Duniya hanya ce zuwa Lahira, ba ita ce makoma ta ƙarshe ba.

Allah Ya tsare mu daga sharrin duniya.

Allah Ka sa mu gama da duniya lafiya.

Allah Ka sa duniyarmu ta yi kyau, Lahiram mu ta yi kyau.

Allah Ka kyautata ƙarshen rayuwarmu, Ka sa mu cika da imani
Awafss. TV

Photos from Awafss. TV's post 26/08/2026

ALHAMDULILLAH
MASHA ALLAH

Yauma kamar kowane sati angudanar da karatun littafin USULUSSALASA cikin koshin lafiya Wanda Ustaz Salmanu Mahmood Adam ya gabatar a karkashin wannan kungiya mai albarka ALKITABU WASSUNNAH ALA FAHAMI SALAFUSSALIH Allah yasa mu amfana da abunda muka saurara AMEEN
✍️✍️✍️
_________________________
Ibrahim Ahmad Mubarak
(Babban Yayah)
_________________________

Awafss. TV
Awafss Sunnah

20/08/2026

ASSALAMU ALAIKUM
Ana Sanar da mambobin wannan kungiya cewar akwai karatu da za'a gabatar Ranar ASABAR insha allahu

Za'a gabatarda wannan karatu insha Allah amasallacin da shugaba yake karatun USULUSSALASA Wandake unguwar nitel bauchi Allah yabada ikon halarta AMEEN

SANARWA DAGA OFISHIN SHUGABAN KUNGIYA TA JIHA
___________
_SALMAN MAHMOOD ADAM_
___________

18/08/2026

Alamomi 50 na ƙaunar Manzon Allah ﷺ:

Imani da shi (saw ) gasgatawa da yarda da biyyaya da sallamawa ,fifitawa
da miƙa wuya da amincewa a fili da ɓoye babu nuƙu-nuƙu ba munafinci:

1. Son Manzon Allah ﷺ fiye da sauran mutane.
2. Son shi fiye da son kai da dukiya.
3. Bin Sunnarsa a cikin rayuwa.
4. Ƙoƙarin sanin tarihinsa da sirarsa.
5. Yawaita salati da sallama a gare shi.
6. Girmama sunansa idan an ambace shi.
7. Son Sahabbansa رضي الله عنهم.
8. Son Ahlul Baiti da mutunta su.
9. Kare mutuncinsa daga zagi da ƙarya.
10. Ƙin duk abin da ya saɓa wa koyarwarsa.
11. Yin biyayya ga umarninsa.
12. Nisantar abin da ya hana.
13. Yin koyi da kyawawan halayensa.
14. Tausayi da jinƙai ga mutane kamar yadda ya koyar.
15. Gaskiya da amana.
16. Haƙuri a lokacin jarabawa.
17. Tawali’u da rashin girman kai.
18. Afuwa ga wanda ya yi maka laifi.
19. Kyautata wa maƙwabta.
20. Girmama iyaye.
21. Kyautata mu’amala da iyali.
22. Tausayi ga yara.
23. Jinƙai ga marasa ƙarfi.
24. Kyautata wa dabbobi.
25. Yawaita zikiri da addu’a.
26. Kula da salla kamar yadda ya koyar.
27. Son Alƙur’ani da karanta shi.
28. Yin aiki da koyarwar Alƙur’ani.
29. Son masallaci.
30. Son tarayya da mutanen kirki.
31. Nisantar munanan ɗabi’u.
32. Guje wa ƙarya da yaudara.
33. Guje wa gulma da cin mutunci.
34. Rashin zaluntar kowa.
35. Rikon amana.
36. Cika alkawari.
37. Yin sulhu tsakanin mutane.
38. Ƙoƙarin yada zaman lafiya.
39. Koyar da Sunnarsa ga wasu.
40. Kare Sunnarsa daga gurɓatawa.
41. Yin farin ciki idan an samu damar bin Sunnarsa.
42. Jin takaici idan aka yi watsi da Sunnarsa.
43. Son abin da yake so na alheri.
44. Ƙin abin da ya ƙi na sharri.
45. Yin addu’a domin samun kusanci da shi a Aljanna.
46. Yawaita ambaton kyawawan halayensa.
47. Karanta hadisan Manzon Allah ﷺ da fahimtar su.
48. Aiwatar da koyarwarsa ba wai magana kawai ba.
49. Gabatar da Sunnarsa a kan son zuciya.
50. Rayuwa da ƙaunarsa har ƙaunar ta bayyana a cikin ɗabi’a, ibada da mu’amala.

Allah ya sanya mu cikin waɗanda suke ƙaunar Manzon

17/08/2026

ANA IYA HAƊA NEMAN DUNIYA DA LAHIRA ?

Ana iya haɗa neman duniya da neman lahira waje guda, domin Musulunci bai umurci mutum ya bar duniya gaba ɗaya ba. Abin da ake buƙata shi ne duniya ta kasance a tafin hannu, ba a zuciya ba, kuma a yi amfani da abin da aka samu na duniya wajen samun yardar Allah.

Hanyoyi 10 na haɗa su waje guda

1. Ka nemi halal – Kasuwanci, aiki, noma ko sana’a, amma ka nisanci haram da zalunci.
2. Ka gyara niyyarka – Ka ce: “Ina neman abin duniya ne domin in dogara da kaina, in ciyar da iyalina, in taimaki mabukata, kuma in yi ibada cikin kwanciyar hankali.” Hakan yana mayar da aikin duniya ibada.
3. Kada duniya ta hana ka sallah. Idan aiki ya yi yawa, kada ka bar farillai saboda neman kuɗi.
4. Ka ba Allah hakkinsa daga dukiyar ka – Zakka, sadaka, ciyar da iyali da taimakon mabukata.
5. Ka samu ilimin addini tare da ilimin duniya. Ka zama mutum mai amfani a addininsa da kuma al’ummarsa.
6. Ka yi amfani da dukiyarka wajen lahira. Gina masallaci, tallafa wa makaranta, taimakon marayu da sauran ayyukan alheri na iya zama sadaka jariya.
7. Ka guji kwaɗayin duniya. Samun dukiya ba laifi ba ne; abin damuwa shi ne dukiya ta mallaki zuciya.
8. Ka tuna cewa duniya hanya ce, ba makoma ba. Manufar ƙarshe ita ce samun yardar Allah da Aljanna.
9. Ka kasance mai aiki tukuru amma mai tawakkali. Ka yi amfani da sababbin hanyoyi, sannan ka dogara ga Allah.
10. Ka yi addu’ar da Alƙur’ani ya koya mana:
﴿رَبَّنَا آتِنَا فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي الْآخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ النَّارِ﴾

Ma’ana: “Ya Ubangijinmu! Ka ba mu alheri a duniya, ka ba mu alheri a lahira, kuma Ka tsare mu daga azabar wuta.” (Al-Baqarah: 201)

A taƙaice: Ka yi aiki kamar wanda yake neman arzikin duniya, ka yi ibada kamar wanda yake shirin barin duniya, kuma ka yi amfani da abin da ka samu a duniya wajen gina makomarka a lahira.

Duniya da lahira ba abokan gaba ba ne; idan an yi amfani da duniya yadda Allah Ya so, duniya na iya zama hanyar samun lahira.

Photos from Awafss. TV's post 14/08/2026

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH

Ajiya alhamis 13/08/26 shugaba tareda matemakinsa dakuma wasu mukarrabansa s**akai ziyara ta musamman ga masu gunduma Wanda akasamu nasarar ziyartar mai gunduman Dan amar dakuma hardon bauchi
Yayinda s**a tattauna dakuma samun goyon baya daga garesu

Muna fatan ubangiji yakara daukaka wannan kungiya tamu mai albarka (AWAFSS) ameen

_________________________________
✍🏽✍🏽__Ibrahim Ahmad Mubarak
________(babban Yaya) ___________
ASST. Direct. Social media
__________________________________

12/08/2026

Banbanci 3 tsakanin masu tallata kayan Manzon Allah ﷺ da masu tallata kayan Shehunansu😓

1️⃣ Masu tallata kayan Manzon Allah ﷺ
Suna ƙarfafa mutane su bi Sunnah, su koma ga abin da Manzon Allah ﷺ ya koyar, ba tare da ɗaukaka wani mutum sama da matsayinsa ba.

Masu tallata kayan Shehunan su:
Sau da yawa manufarsu itace su ɗaukaka shehin nasu, su riƙa yaɗa maganganunsa da ayyukansa ko da kuwa sun ci karo da hujja.

2️⃣ Masu tallata kayan Manzon Allah ﷺ
Idan aka kawo musu ingantacciyar hujja daga Alƙur’ani da Sunnah, suna karɓa domin gaskiya ce.

Masu tallata kayan Shehunan su:
Wasu daga cikinsu idan hujja ta saɓa da abin da shehinsu ya faɗa, sai su fara neman hujjar da zata kare maganar shehin, maimakon su mayar da magana zuwa ga Alƙur’ani da Sunnah.

3️⃣ Masu tallata kayan Manzon Allah ﷺ
Babbar tambayarsu itace: “Shin wannan ya tabbata daga Manzon Allah ﷺ?”

Masu tallata kayan Shehunan su:
Babbar tambayarsu ta kan kasance: “Shin Shehimmu ya faɗi haka?”

📌 A ƙarshe:
Mu ba'a ce mu ƙi malamai ba. A’a, muna girmama malamai, amma bamu ɗauki maganar kowa a matsayin ma’aunin gaskiya ba.

Ma’aunin gaskiya shi ne Alƙur’ani da ingantacciyar Sunnah bisa fahimtar Sahabbai.

“Idan kuka yi sabani a kan wani abu, ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa s.a.w.”
(Suratun Nisa’i: 59)
Awafss. TV

12/08/2026

ALHAMDULILLAH

___________________
Kamar yadda akasabu duk sati ana gabatar da karatun littafin USULUSSALASA to yauma insah allahu
Za'a gabatarda wannan karatu insha Allah

---------
Awafss. TV
------------
Salmanu Mahmood Adam
=========
Awafss Sunnah

11/08/2026

ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH
Muna Kara Sanar da al'ummah cewar insha allahu yau me Ranar da za'afara GUDANAR da DAURAH da yardar Allah haka yafarune sakamakon jiya bamusamu damar somawa ajiya litininba Amma yau in Allah ya yarda za'a soma DAURAH kamar yadda aka Sanar za'a guadanar da wannan DAURAH ne amakarantar firamare na dangikka dake Kan titin bakaro anan jihar bauchi damisalin karfe 9am nasafe
Allah yasa mudace amin
Awafss. TV
Salmanu Mahmood Adam
Ibrahim Danjuma
Awafss Sunnah
Mustapha Sh*tu
Umar Yusuf Mullah

07/08/2026

Ana gayyatar kowada kowa Kuma haryanzu kofa abuse take Sai kunzo

Want your business to be the top-listed Media Company in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Unguwan Bauchin Bauchi Nuru Quaters Bauchi
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Awafss. TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Bauchi.