Zaidu Ibrahim Ririwai
Ririwai
24/11/2025
Shahararren jarumin fina-finan Bollywood na ƙasar Indiya, Dharmendra, ya rasu yana da shekara 89 bayan fama da jinya.
Dharmendra ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jarumai a tarihin Bollywood, inda ya taka rawar gani a daruruwan fina-finai tun daga shekarun 1960 zuwa 2000.
Rahotanni sun bayyana cewa jarumin ya daɗe yana fama da matsalolin lafiya kafin rasuwarsa a yau, lamarin da ya tayar da hankalin masoyansa a faɗin duniya.
A shekarun baya-bayan nan, Dharmendra ya kasance yana gudanar da wasu ayyuka na musamman a masana’antar fim, duk da ƙarancin lafiyarsa.
Tuni manyan jarumai a masana’antar Bollywood da dubban masoya s**a fara cika gidansa domin bayyana alhini da kuma jajantawa dangin mamacin bisa wannan babban rashi
28/02/2022
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Bauchi