Arewa Post
Sahihan labaran ciki da wajen Najeriya.
10/05/2026
Hotunan Yadda Gwagwaren Katsina Hakimin Raɗɗa, Muhammadu Dikko Raɗɗa Ya Kai Ziyara Fadar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll, Jiya Asabar
04/05/2026
DA DUMI-DUMI: Hon. Mahmud Sadis Buba, wanda aka fi sani da Abun Al-ajabin Sarkin Zazzau ya karɓi Form ɗin tsayawa takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar yankin sabon garin Zaria a jihar Kaduna.
Me za ku ce?
04/05/2026
Ɗan Tsohon Shugaban Kasa, Honarabul Yusuf Buhari Yana Cigaba Da Tattaunawa Da Al'ummar Mazaɓar Majalisar Tarayya Daura Da Sandamu Da Kuma Maiaduwa A Jihar Katsina
30/04/2026
DA ƊUMI-ƊUMI: An Fara Raba Riguna Da Kuɗi Naira Dubu Goma Ga Matasa Domin Taron Tarbar Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Gombe Aminu Yuguda (AG) Wanda Zai Gudana A Yau Alhamis.
Ko me kuka fahimta?
28/04/2026
Kungiyar “Arewa Media Writers” Ta Yi Allah-Wadai da Amincewa Da Sabon Bashin Dala Miliyan 516.3 Domin Aikin Titin Sokoto–Badagry
Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ƙarƙashin jagorancin Comr Haidar Hashim Kano, ta yi Allah-wadai da matakin da Majalisar Wakilai ta ɗauka na amincewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓo bashin dala miliyan 516.3 domin aikin titin Sokoto–Badagry.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce wannan mataki na ƙara ɗora wa ƙasar nan nauyin bashi a daidai lokacin da tattalin arziƙin al’umma ke cikin mawuyacin hali, abin da ke haifar da damuwa kan makomar tattalin arziƙin Najeriya.
Ƙungiyar ta jaddada cewa yawan karɓar bashi ba tare da cikakken bayani kan hanyoyin biyan sa da kuma tasirin sa ga rayuwar al’umma ba na nuna rashin tsari da hangen nesa daga bangaren gwamnati da majalisun dokoki.
“Abin takaici ne yadda ake ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakai ba tare da la’akari da halin ƙunci da talauci da al’umma ke ciki ba. Wannan na ƙara tsananta wahalhalun da jama’a ke fuskanta a yau,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan yadda Majalisar Dattawa ta amince da irin waɗannan shirye-shirye ba tare da zurfin nazari da la’akari da ra’ayin al’umma ba, lamarin da ta ce bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Ta ƙara da cewa ci gaba da jingina ci gaban ƙasa da bashin ƙasashen waje na iya jefa Najeriya cikin matsin tattalin arziƙi a nan gaba, tare da barazana ga ‘yancin tattalin arziƙin ƙasar.
Don haka, “Arewa Media Writers” ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dattawa da su sake nazari kan wannan mataki, su fifita hanyoyin inganta tattalin arziƙi cikin gida ba tare da dogaro da bashin waje ba.
A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da irin waɗannan matakai tare da riƙe shugabanni da alhakin duk wata doka ko shawara da za ta shafi rayuwarsu.
Comr. Muhammad Kwairi Waziri
National Editor I, Arewa Media Writers
28/04/2026
YANZU-YANZU: Jam'iyyar APC Ta Fara Siyar Da Form Na Tsayawa Takara A Ofishin Ta Ga Masu Sha'awar Yin Takara A Jam'iyyar
27/04/2026
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Allah Ya Yi Wa Ɗan Amar Fagachin Katsina, Alhaji Ibrahim Iro Maikano Rasuwa A Wata Asibiti Dake Abuja Yau Litinin
Allah Ya Jikansa Da Rahama!
26/04/2026
Ɗan Gidan Marigayi Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya Yusuf Buhari Na Cigaba Da Yawan Neman Zaɓe.
Wane Fata Kuke Masa?
23/04/2026
YANZU-YANZU: Peter Obi Ya Ziyarci Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed A Gidan Gomnatin Jihar
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya kai ziyara ta musamman ga Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a gidan gwamnatin jihar da ke Bauchi.
Daga Muhammad Kwairi Waziri
23/04/2026
Tsohon ɗan takarar Majalisar Jiha na Ƙaramar Hukumar Kabo a shekarar 2023, Hon. Rabi'u Sayyadi Kazode, ya fice daga jam’iyyar PDP.
Tun a ranar Litinin 20/4/2026 tsohon ɗan takarar ya bayyana ficewarsa daga tsohuwar jam'iyyar tasa, inda ya miƙawa shugaban jam'iyyar PDP a mazaɓarsa ta Masanawa takardar ficewar ta sa.
Yayin ficewar ta shi, ya godewa jagororin PDP dake mazaɓarsa, haka kuma ya jaddada cewa yanzu lokaci yayi tunda wasu tsirarun mutane sun rusa PDP, to dole mu tafi gidan da zamu ceci yankinmu da jiharmu baki ɗaya.
Daga karshe ya godewa dukkan masoyansa da magoya bayansa fiye da mota hamsin da s**a masa rakiya zuwa mazaɓarsa, inda ya shelanta musu komawarsa APC tare da umartar mabiyansa baki daya da su koma mazabunsu su yankin katin jam'iyyar APC don tunkarar zaɓen 2027 insha Allah.
Malam Shekarau Kainuwa Dashen Allah .
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Nsukka Street Abuja
Abuja