Fim Magazine
The best place for authentic stories about Hausa movies, culture, writing, and music
09/05/2026
Ganawar Ribaɗu da JD Vance: Nijeriya da Amurka sun ƙarfafa alaƙar tsaro
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar ƙara zurfafa hadin gwiwa a fannin tsaro, yaki da ta’addanci da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Yammacin Afrika.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Asabar.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, ya kai ziyarar aiki ta kwanaki uku a Amurka, inda ya gana da manyan ƙusoshin gwamnatin ƙasar.
A yayin ziyarar, Ribaɗu ya isar da saƙon Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jajircewa wajen ɗorewar dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Ribaɗu ya gana da Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, da sauran manyan jami’an diflomasiyya da na tsaro na Amurka.
Babban maƙasudin wannan ganawa shi ne duba yadda za a inganta raba bayanan sirri da kuma ƙarfafa ayyukan soji na haɗin gwiwa.
Ribaɗu ya jaddada muhimmancin taimakon juna don magance matsalolin tsaro da s**a addabi yankin Sahel, musamman Ayyukan ta’addanci da tsageranci, safarar miyagun ƙwayoyi da mak**ai da laifukan da ake aikatawa ta hanyar yanar gizo.
Hukumomin Amurka sun jinjina wa Nijeriya a matsayin ta na jagora a yankin Afrika, musamman wajen jagorantar yaƙi da ta'addanci a tafkin Chadi.
A nata ɓangaren, Nijeriya ta bayyana cewa tana amfani da dabarun ƙarfin soja da kuma tattaunawa da inganta rayuwar jama'a don magance tushen matsalar rashin tsaro.
"Nijeriya tana godiya ga Amurka bisa taimakon da take bayarwa a ɓangaren horar da jami'ai, ba da bayanan sirri, da kuma tallafin jinkai," inji Ribaɗu.
A ƙarshen taron, ɓangarorin biyu sun amince su ci gaba da tuntuɓar juna a kai a kai ta hanyar haɗin gwiwa na musamman don tabbatar da cewa dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla sun fara aiki yadda ya k**ata.
09/05/2026
Dakaru sun ga bayan ’yan ta’adda masu yawa, sun ceto mutum 50, inji hedikwatar tsaro
Rundunar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun kasar nan sun samu nasarar ragargazar dimbin ’yan ta’adda, inda s**a k**a wasu da dama tare da ceto mutum sama da 50 da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan.
Wadannan nasarori sun faru ne a yayin ayyukan kakkaba da sojoji s**a gudanar tsakanin ranar 30 ga watan Afrilu zuwa 7 ga watan Mayun 2026.
Daraktan Yada Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja. Ga yadda nasarorin suke kasance a kowacce shiyya:
• Arewa maso Gabas (Operation HADIN KAI): Rundunar ta dakile hare-haren ’yan ta’adda a Magumeri da ke jihar Borno. Haka kuma, wasu daga cikin maharan sun mika wuya, yayin da aka k**a masu kai musu kayan abinci da mak**ai.
• Arewa maso Yamma (Operation FANSAN YAMMA): Sojoji sun yi artabu da ’yan fashi a jihohin Katsina da Zamfara, inda aka kashe da dama tare da kwace babura da mak**ai.
• Arewa ta Tsakiya (Operation SAVANNAH SHIELD): An ceto wadanda aka yi garkuwa da su tare da k**a masu safarar harsasai har guda 250 a cikin birnin Abuja.
• Jihar Filato: Jami'an tsaro sun bankado wata masana’antar kera mak**ai ba bisa ka’ida ba a Jos ta Kudu, inda aka k**a mutanen da ake zargi da kera bindigogi.
• Jihar Benuwai da Kogi: An samu nasarar ceto wasu yara dalibai da aka sace daga gidan marayu.
Janar Onoja ya kara da cewa, dakarun Operation DELTA SAFE a Kudancin kasar da kuma Operation UDO KA a Kudu maso Gabas duk sun samu nasarar k**a masu garkuwa da mutane da kuma dillalan mak**ai na kungiyar IPOB/ESN.
"Rundunar sojin kasa a karkashin jagorancin Shugaban Hafsun Tsaro, Olufemi Oluyede, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun rayu cikin lumana da kwanciyar hankali." — Maj. Gen. Onoja
Wannan gagarumar nasara ta nuna cewa jami’an tsaro sun sake zage damtse wajen ganin sun kawo karshen matsalolin tsaro da s**a addabi sassan kasar nan.
08/05/2026
Ƙwaƙudumar kasa biyan tulin bashin da manyan bankuna s**a bayar laifin daraktoci da manyan masu hannayen jarin su ne, ba laifin CBN ba
Ashafa Murnai Barkiya
Yayin da ake fama da gagarumar matsalar yawan maƙudan kuɗaɗen da bankuna s**a bayar bashi, kuma biyan bashin ya gagara, akwai masu ɗora laifin kan Babban Bankin Nijeriya (CBN), a matsayin sa na mai kula da kuma sa-ido kan dukkan bankunan Nijeriya.
To sai dai kuma idan aka yi la'akari da yanayin yadda manya da ƙananan bankuna ke bayar da basuss**an, to fa dole ne kacokan a ɗora laifin kan daraktocin bankunan da matsalar ta shafa da kuma manyan masu zuba jari a bankunan.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da CBN ya bada umarni ga wasu bankuna cewa kada su raba ribar ƙarshen shekara-shekara, saboda ɗimbin bashin da bankunan s**a bayar, wanda ba a biya ba, har ya riƙe wa bankunan wuya.
A irin wannan tsomomuwar bashin ne kamfanin ɗanyen mai da iskar gas, Nestoil mallakar Ernest Obiejesi ya ci bashin Naira Tiriliyan 2.9 a hannun wasu manya da ƙananan bankunan Nijeriya.
Masu Hannun Jari Ba ‘Yan Kallo Ba Ne:
A ƙarƙashin Dokar Kamfanoni da Harkokin Kasuwanci ta 2020 (CAMA 2020), masu hannun jari ba ‘yan kallo ba ne kawai, su ne ke da cikakken iko a harkokin shugabanci. Sashe na 238 ya bai wa taron gaba ɗaya iko, yayin da sashe na 271 zuwa 274 ke tanadin yadda ake naɗawa, cirewa da kuma biyan daraktoci.
Wannan yana nufin masu hannun jari ne ke zaɓar waɗanda za su tafiyar da banki, su kuma amince da albashin su da ladar su—wannan kuwa yana tasiri kai tsaye ga yadda suke gudanar da aiki.
Sashe na 238 ba kawai ƙa'ida ba ce, ginshiƙi ne na gaskiya da ɗaukar nauyi. Yana tabbatar da cewa masu kamfani ne ke zaɓar shugabanni, yana hana ƙungiyoyin daraktoci zama masu cin gashin kan su ba tare da kulawa ba. Haka kuma yana tabbatar da gaskiya a cikin tsarin naɗi, yana rage yiwuwar nadin ɓoye ko na son zuciya.
Wannan tsarin yana ƙarfafa ɗaukar alhaki, domin daraktoci sun san cewa masu hannun jari ne s**a zaɓe su kuma za su iya cire su idan sun gaza.
Haka kuma yana taimaka wa masu kula (regulators) su san wane ne ke jagoranci da kuma yadda aka kai ga hakan.
A lokacin rikici, wannan sashe yana nuna cewa daraktoci ba su zo ne bisa kuskure ba—an zaɓe su ne da niyya, don haka dole a duba har da rawar masu hannun jari.
Amma a aikace, sau da yawa masu hannun jari kan goyi bayan faɗaɗa bayar da bashi domin samun riba mai yawa a lokacin bunƙasa tattalin arziki, sai kuma su koma baya su ɗora laifi kan wasu idan abubuwa s**a lalace. Wannan hali yana haifar da matsala.
Daraktoci Sun Rigaya Sun Fuskanci Tsauraran Dokoki:
Ra’ayin cewa daraktoci ba su da alhaki a doka ba gaskiya ba ne. CAMA 2020 ya fayyace wajibai:
Sashe na 305 ya fayyace cewa: Wajibi ne daraktoci yu yi aiki cikin gaskiya don amfanin kamfani.
Sashe na 306: Su yi aiki da ƙwarewa da kulawa.
Sashe na 309: Su guji rikicin son-kai, son-rai da son-zuciya.
Haka kuma dokar bankuna ta BOFIA 2020 ta ƙara tsaurara wannan:
Sashe na 19 ya ce: Dole ne a bayar da bashi bisa ƙa’idojin banki masu kyau da fa'ida.
Sashe na 20: Ya hana bayar da bashi ga masu alaƙa da masu bayar da bashin, ba tare da bin ƙa’ida ba.
Idan aka karya waɗannan dokoki, akwai hukunci ciki har da tara, kora ko ma hukuncin kotu.
Saboda haka, tsarin doka ya riga ya tanadi yadda za a ɗauki mataki. Ba duk wani bashin da ya lalace ne sak**akon laifi ba—banki kasuwanci ne mai haɗari.
CBN Na Aiki Cikin Tsarin Da Doka Ta Gindaya:
Masu s**ar CBN suna mantawa cewa Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Hadahadar Kuɗi, wato 'Banks and Other Financial Institutions Act' (BOFIA 2020), ta tanadi yadda za a ɗauki mataki a hankali:
Sashe na 33: Ya hana rabon riba da ƙari don kare jarin banki.
Sashe na 34: Ya bada damar cire daraktoci amma sai da hujja mai ƙarfi.
Wannan yana nuna cewa matakan suna zuwa ne a hankali:
Kariya kafin hukunci:
Dakatar da rabon ribar ƙarshen shekara-shekara da aka yi yanzu wata hanya ce ta kare tsarin banki, ba rauni ba ne. Wannan ya yi daidai da ƙa’idojin ƙasashe na duniya.
Shugabanci Tsari Ne Na Haɗin Gwiwa:
Shugabancin banki a yau ya haɗa da ɓangarori da dama:
Daraktoci, masu hannun jari, masu bin-diddigin lissafi, wato 'auditors', kwamitocin duba afkuwar matsala da tantance bashi.
Daraktoci masu zaman kan su suna taka muhimmiyar rawa wajen hana almubazzaranci.
Wasu Matsalolin da ke Haifar da Kasa Biyan Bashi ga Bankuna:
Rikicin bashin da ya faskara a biya, wato 'bad bebt', yana da alaƙa da:
Sauyin farashin kayayyaki, matsalar canjin kuɗi, raunin tsarin tattalin arziki da sauran su.
Idan manyan masu karɓar bashi sun gaza biya, tasirin yana shafar dukkan bankuna.
Buƙatar Tsari Mai Ɗorewa:
Masu hannun jari su riƙa taka rawar gani. Daraktoci su bi dokoki da ƙa’idoji. Tsarin bankuna ya ƙarfafa ɗabi’a mai kyau. CBN ta ci gaba da aiki cikin doka, k**ar yadda a yanzu yake maida himma kan haka ɗin.
A ƙarshe, ɗora laifi kacokan kan CBN kawai ba daidai ba ne. Tsarin doka ya riga ya rarraba alhaki tsakanin:
Masu hannun jari, daraktoci, masu gudanarwa.
A duk inda aka samu laifi, to akwai hukuncin da doka ta tanada. Amma inda matsalar ta samo asali daga yanayin tattalin arziki, dole ne a ɗauki mataki cikin hikima.
Abin da ɓangaren banki ke buƙata ba zargin juna ba ne, sai dai tsarin gaskiya da ɗaukar alhaki daga kowane ɓangare—tun daga hukumar daraktocin banki, har zuwa masu hannun jari. Idan ba a yi haka ba, ko wane irin tsauraran matakan da aka ɗauka ba za su kawo canji mai ɗorewa ba.
07/05/2026
Shugaba Tinubu Ya Shiga Takarar Wa’adi Na Biyu Yayin Da Mataimakinsa Shettima Ya Mika Fom ga APC
A yau Alhamis 7 ga watan Mayu ne, Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kaddamar da neman takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a hukumance ga uwar jam’iyyar APC ta kasa.
A wani gagarumin taro da aka gudanar a dakin taro na *Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre* Mataimakin ya jagoranci mambobin jam’iyyar da s**a hada da gwamnoni, da yan majalisun tarayya, da sauran masu madafun iko na da da na yanzu, inda ya miƙa fom din neman takarar ga Shugabannin jam'iyyar a wani mataki na nuna goyon bayan masu madafun iko ga kudurin sake zaben shugaba Tinubu zango na biyu.
Da yake jawabi jim kadan bayan mika fom din, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bayyana shugaban a matsayin jagora mai juriya wanda ya yi nasarar Jan ragamar Najeriya zuwa tudun-mun tsira a yayinda guguwar matsalolin tattalin arziki ta so yin awon gaba da ita. Kashim ya kafa hujja da ajandar "Renewed Hope" a matsayin babban dalilin cancantar Shugaba Tinubu ga zagaye na biyu inda ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin ta kawo sun fara samar da sak**ako mai kyau, duk da tsaurin da s**a zo da shi a karon farko.
"Kalubalen shekarun da s**a gabata ba su raunana Shugaba Tinubu ba; maimakon haka ma sai kara masa kwarewa da s**a yi," in ji Shettima, inda ya ci gaba da cewa
"Wannan gwarzantaka da kwarewa da ya kara ne ya sa mu ke fatan kara masa wata dama"
A nata bangaren, uwar jam’iyyar ta kasa ta nuna cikakken goyon bayanta ga takarar, inda
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ya karbi takardun takarar, ya ce ayyukan shugaba Tinubu a sassa daban-daban na farfado da kasar sun sa sake zaben nasa ya zama dole.
Yilwatda ya yi nuni da kyautatuwar tattalin arziki da karuwar kwarin gwiwar kasashen duniya ga makomar Najeriya a matsayin hujjojin da jam’iyyar ta dogara da su wajen amincewa da takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shi ma shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya yaba da garambawul din na shugaban Tinubu, wanda ya bayyana a matsayin harsashin farfadowar kasa mai dorewa.
Ita ma kungiyar Gwamnonin APC ta bakin Shugabanta kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma wanda gwamnoni 12 s**a rufa wa baya ta nuna goyon baya na bai-daya ga takarar
Gwamnonin da s**a halarci taron su ne na jihohin Plateau, Ogun, Niger, Kaduna, Ondo, Katsina, Borno, Cross River, Taraba, Yobe, Nasarawa, da Bayelsa.
A yanzu dai mika tikitin takarar a hukumance ya kawo karshen rade-raden da ake yi game da aniyar shugaban ta neman wa'adin Mulki na biyu k**ar yadda ta bayyana irin hadin kan Shugabanni na bai daya da ake dakon gani a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC.
Shugabannin jam’iyyar sun yi kira ga mambobinsu da su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu don "kare fatan Najeriya.".
07/05/2026
Tsauraran matakai da ƙa'idojin da CBN ya gindaya, dangane da bashin naira tiriliyan 2.9 da kamfanin Nestoil ya kasa biyan wasu bankunan Nijeriya
*Yadda katutun bashin ya jawo jinkirin raba ribar ƙarshen shekarar 2025 a wasu manyan bankuna
Daga Ashafa Murnai Barkiya
Kamfanin ɗanyen mai na Nestoil mallakar attajiri Ernest Obiejesi ya jefa wasu manya da ƙananan bankunan Nijeriya cikin halin ƙaƙanikayi, kwatagwangwama da jangwangwama, yayin da bashin naira tiriliyan 2.9 da bankunan ke bin sa s**a maƙale, ake ta haƙilo da turnuƙun shari'ar neman yadda za a biya bashin a kotu.
Baya ga cukumurɗar shari'a da ake tafkawa, a ɗaya gefen kuma wasu manyan bankuna uku da s**a fi bin Nestoil bashi mai tarin yawa, sun kasa biyan ribar ƙarshen shekarar 2025, sak**akon wasu tsauraran matakan da CBN ya gindaya na ƙin amincewa bankunan su raba ribar ga masu hannayen jari, har sai an tantace matsayar bashin da s**a danƙara wa Nestoil Limited tukunna.
Manyan bankunan da s**a fi Afkawa cikin wannan tsomomuwar basuss**an Nestoil sun haɗa da United Bank of Africa (UBA) da kuma Access Bank a baya-bayan nan, waɗanda har yau ba su bayyana rabon ribar ƙarshen shekarar 2025 ba. Shi ma FCMB tuni ya afka cikin wannan jula-jula.
Sak**akon bayanan ƙididdigar ciniki da ribar shekarar 2025 na UBA ya nuna asarar kuɗi daga tanadin bashin da ya kai Naira biliyan 331, yayin da asarar da Access Holdings ya yi wajen rage darajar rance (impairment) ta ƙaru da kashi 209, zuwa Naira biliyan 287.3.
Jimillar bashin da bankunan Nijeriya s**a bayar ga ɓangaren hadahadar mai da iskar gas zuwa ƙarshen 2024 ya kai Naira tiriliyan 21, inda manyan bankunan da s**a fi hulɗa da Nestoil s**a haɗa da UBA, First Bank, Access Bank, FCMB, Union Bank, Ecobank da kuma African Export-Import Bank.
Tsauraran Matakan da CBN Ya Ɗauka Kan Nestoil da Bankunan da S**a Danƙara wa Kamfanin Bashi:
A ƙarƙashin tsauraran matakan, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, Babban Bankin Nijeriya ya hana waɗannan bankuna biyan ko raba ribar ƙarshen shekara-shelara, har sai sun kammala tanadin dukkan basuss**an da ba a biya ba.
A ranar 13 ga Yuni, 2025 dai CBN ya hana bankunan da abin ya shafa su raba ribar ƙarshen shekara-shekara, k**ar yadda wata sanarwar da aka fitar, mai ɗauke da sa-hannun Daraktan Kula da Mu'amalar Bankuna, Dakta Olubokola A Akinwunmi.
Yanayin Bashin Nestoil:
Matsalar bashin bankunan yanzu ta ta’allaƙa ne kan rashin ikon Nestoil wajen biyan basuss**an haɗin gwiwa da aka ba kamfanin, a lokacin da ake sa ran ƙarin samar da mai.
Rashin biyan bashin da Nestoil ke yi ya ƙara matsin-lamba ga bankuna, musamman waɗanda s**a fi hulɗa da kamfanonin mai masu zaman kan su.
Baya ga tanadin asarar bashin, bankuna na ƙoƙarin karɓo bashin nasu.
Masu bada rance sun samu umarnin kotu a watan Oktoban 2025, wanda ya riƙe kadarorin Nestoil—ciki har da kuɗaɗen banki, gidaje da kayayyakin mai—a fiye da bankuna 20.
Ana ci gaba da ƙoƙarin karɓar kadarori duk da ƙalubalen shari’a da ake fuskanta daga Nestoil.
Bankuna na shirin ƙwace kadarori, gidaje da kayan mai, wanda zai iya haifar da dogon rikicin shari’a da zai kulle kuɗaɗe masu muhimmanci, tare da barazana ga wadatar kuɗi a fannin banki.
Barazanar Bashin Nestoil ga Tsarin Banki:
Masana na gargaɗin cewa dawo da waɗannan kuɗaɗe ba zai zama mai sauƙi ba.
CBN yanzu ya fifita kare jarin bankuna, ta hanyar hana biyan ribar ƙarshen shekara-shelara har sai basuss**an da ba a biya ba sun sauka ƙasa da kashi 5.
Adadin basuss**an da ba a biya ba a fannin banki ya kusa kai kashi 7 a 2025, wanda ke barazana ga daidaiton bankuna idan matsalar bashin mai ta ci gaba.
Muhimmancin Matakin da CBN ya Ɗauka:
Ko da yake dakatar da raba ribar ƙarshen shekara-shelara yana cutar da masu hannun jari, masana na ganin cewa wannan tsauraran mataki na da muhimmanci domin kauce wa irin matsalar rushewar bankuna ta 2009.
Saboda haka hanyar tilasta bankuna su bayyana asara yanzu, CBN na tabbatar da cewa bashin Naira tiriliyan 21 da aka bai wa ɓangaren mai yana bayyana gaskiya, maimakon ɓoye shi.
Wannan matsin lamba daga ɓangaren mai na zuwa ne a daidai lokacin da aka kammala shirin ƙara jarin bankuna, wanda ya taimaka musu su iya ɗaukar irin wannan asara.
Yadda Nestoil Ya Ci Bashin Naira Tiriliyan 2.9:
Bashin Nestoil na Naira Tiriliyan 2.9 ba a lokaci ɗaya kamfanin ya ciwo shi ba. Ya taru ne tsawon shekaru yayin da kamfanin ke faɗaɗa ayyukan sa a yankin Neja Delta, inda ya riƙa karɓar rancen maƙudan kuɗaɗe, bisa tsammanin samun kuɗaɗen shiga daga man fetur, wanda hakan bai da bai tabbata ba.
A watan Disamba 2022, wani rukuni na bankuna 16 ƙarƙashin jagorancin FBN Group tare da Afreximbank s**a haɗa bashin cikin wata yarjejeniya mai suna “Global Facilities” ƙarƙashin dokokin Ingila.
Waɗanda s**a bayar da garanti sun haɗa da Neconde Energy, Obiejesi da kansa da matar sa Nnenna Obiejesi. A watan Oktoba 2025, an bayyana bashin ya kai sama da dala biliyan 1.01 da kuma naira biliyan 430 na daban.
A watan Oktoba 2025, wata kotu a Legas ta bayar da umarnin riƙe kadarorin Nestoil da Neconde Energy a bankuna sama da 20, ciki har da asusun banki, kadarori da kaya na mai. An kuma naɗa mai kula da kadarorin.
An samu rikicin shari’a kan wanda ke da ikon naɗa lauyoyi. A farko kotun ɗaukaka kara ta bai wa masu kuɗin iko, amma a ranar 10 ga Afrilu 2026, Kotun Koli ta soke hukuncin tare da s**ar Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Yanzu ana sa ran shari’ar za ta koma kotun farko, kuma masana na ganin za ta iya ɗaukar shekaru saboda rikitarwa.
Ba Nestoil Ya Haddasa Jinkirin Raba Ribar Ƙarshe Shekara a Wasu Bankuna Ba -Nestoil:
A ranar Talata kamfanin mai na Nestoil ya fito ya ƙaryata labarin da yawancin jaridu s**a buga a ranar Litinin, mai ɗauke da cewa "Bashin Naira Tiriliyan 2.9 da Nestoil ya kasa biyan bankuna, ya haifar da jinkirin biyan ribar ƙarshen shekara-shekara a wasu manyan bankuna uku."
Sanarwar ta yi zargin cewa Shugaban Bankin First Bank ya ɗauki nauyin wasu jaridu s**a buga labarin.
Sai dai kuma ana ganin cewa wannan bayani na Nestoil ba gamsasshe ba ne, domin kamfanin ya kasa yin bayani kan naira tiriliyan 2.9 da bankunan ke bin sa bashi, lamarin da ake ci gaba da tafka shari'a kan waɗannan maƙudan kuɗaɗe.
A kan haka ne Nestoil ya ce bankunan sun ƙi raba ribar ce, wato 'dividends', saboda bin umarnin CBN, amma ba laifin Nestoil ba ne.
Hoto: Ernest Obiejesi, Shugaban Nestoil
Yadda ƙarfin laƙani da dafa'in CBN ke hana girgizar tattalin arzikin duniya yi wa Nijeriya barazana
Daga Ashafa Murnai Barkiya
Manyan sauye-sauyen da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aiwatar, sun zama ƙaƙƙarfar kariya ga girgizar tattalin arzikin duniya, suna kuma taimakawa wajen tabbatar da amincewar masu zuba jari da kuma ƙara hasashen bunƙasar tattalin arziki.
Sauye-sauyen da CBN ƙarƙashin jagorancin Olayemi Cardoso ya gabatar sun shirya tattalin arzikin ƙasar don jure ƙalubalen da ke tasowa daga waje, ta hanyar samar da matakan kariya da ke tabbatar da ɗorewar tattalin arziki. Shugabannin kasuwanci na cikin gida da na ƙasashen waje sun amince cewa yanzu Nijeriya na da kyakkyawan matsayi don tunkarar girgizar tattalin arziki daga waje, tare da ci gaba da samun amincewar masu zuba jari.
Daidaituwar farashin canjin kuɗi da ci gaba da shigowar kuɗaɗen waje cikin asusun ajiyar ƙasa na bayar da dama mai kyau ga ɗorewar tattalin arziki da bunƙasa mai ɗorewa.
Tattalin arzikin Nijeriya ya samu gagarumin sauyi a ‘yan shekarun nan sak**akon waɗannan gyare-gyare. K**a daga daidaita farashin canjin kuɗi, ƙara tsauraran dokoki, inganta tsarin gaskiya a harkokin kasuwar canjin kuɗi, zuwa ƙarfafa sa-ido kan safarar kuɗi, duk sun taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Muhimmin ɓangare na waɗannan sauye-sauye ya haifar da fa’ida mai yawa ga tattalin arziki, ciki har da samar da kariya don daidaito da bunƙasa tattalin arziki.
Duk da matsin lambar da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haifar, tattalin arzikin Nijeriya ya ci gaba da kasancewa mai ƙarfi kuma yana jan hankalin masu zuba jari na duniya.
Masu zuba jari sun ci gaba da neman kadarorin Nijeriya yayin da tasirin sauye-sauyen CBN ke yaɗuwa zuwa muhimman sassan tattalin arziki.
Yadda CBN Ya Fara Gano Laƙanin Bunƙasa Tattalin Arziki:
CBN ta fara aiwatar da tsare-tsare masu ƙarfi don jawo ƙarin jari daga ƙasashen waje da kuma tabbatar da daidaiton farashi da canjin kuɗi. Fiye da shekaru biyu da s**a gabata, gwamnati tare da CBN ƙarƙashin Cardoso sun ‘yantar da kasuwar canjin kuɗi, sun dakatar da bayar da rance kai-tsaye ga gwamnati, sannan aka gyara tsarin tallafin mai.
Haka kuma, gwamnati ta ƙarfafa tara kudaden shiga tare da ɗaukar matakai don rage hauhawar farashi.
Tun bayan aiwatar da waɗannan tsare-tsare, ajiyar kuɗaɗen waje ya ƙaru, kuma mutane na samun damar sayen kuɗaɗen waje cikin sauƙi a kasuwar musayar kuɗaɗe ta hukuma.
Sannan kuma Nijeriya ta sake komawa kasuwannin kuɗaɗe na duniya a watan Disambar da ya gabata, kuma kamfanonin ƙididdiga sun ɗaga darajar ta. Sabon matatar mai na cikin gida mai zaman kan sa yana taimaka wa ƙasar ta ƙara daraja ma'aunin hadahada a duniya.
Manufofin CBN, ciki har da gyaran tsarin hadahadar kuɗi, sun jawo shigowar jari daga ƙasashen waje tare da rage tsoma bakin CBN a kasuwar canjin kuɗi.
Daidaita farashin canjin kuɗi da kuma biyan bashin sama da dala biliyan 7 na kasuwar musayar kuɗaɗe ya ƙara inganta yanayin saka jari, inda Bankin Duniya ya bayyana hakan a matsayin mataki mai ƙarfi don tabbatar da ɗorewar tattalin arziki.
Sannan kuma bambancin haɗarin bashin Nijeriya ya ragu zuwa mafi ƙanƙanta tun daga Janairu 2020, abin da ya nuna ƙoƙarin jawo masu zuba jari da ci gaba da shigar jari daga ƙasashen waje.
Cardoso ya bayyana cewa haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tattalin arziki:
“Gudanar da rage hauhawar farashi a yanayin matsin lamba na buƙatar ƙarfafan manufofi da haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren kuɗi da na gwamnati, don tabbatar da amincewar masu zuba jari. Dole mu maida hankali kan daidaiton farashi da dawo da ƙarfin nauyin aljihun jama’a.”
Shirin Ƙara Ƙarfin Jarin Bankuna:
CBN ya kuma maida hankali kan ƙarfafa bankuna, inda ya ƙaddamar da sabbin ƙa’idojin ƙarin babban jari ga bankuna daga Maris 2026, domin ƙarfafa su da kuma shirya tattalin arziki zuwa darajar dala tiriliyan ɗaya.
Ƙaruwar Shigowar Jari Daga Ƙasashen Waje:
Cardoso ya bayyana cewa Nijeriya na samun kusan dala miliyan 600 duk wata daga kuɗaɗen ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashe daban-daban. Ya ce sauye-sauyen sun taimaka wajen rage tasirin girgizar tattalin arziki daga waje, tare da inganta kasuwar canjin kuɗi da asusun ajiyar waje.
Ya ƙara da cewa bankunan Nijeriya suna cikin ƙoshin nagarta da inganci, kuma sun samu nasarar tara sabon babban jari don tallafawa bunƙasar tattalin arziki da samar da rance ga ƙananan ‘yan kasuwa.
Rahoton Duba Halin Tattalin Arzikin Nijeriya:
Rahoton 'Global Economic Prospects' na Bankin Duniya ya ɗaga hasashen bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya zuwa kashi 4.4% a 2026 daga kashi 3.7%.
Rahoton ya ce bunƙasar za ta samu ne sak**akon ci gaban sashen ayyuka, farfaɗowar noma, da kuma gyare-gyaren tattalin arziki da manufofin kuɗi masu kyau.
CBN ma ya yi hasashen bunƙasa zuwa kashi 4.49% a 2026, yana danganta hakan da ci gaba da sauye-sauye da sassauta manufofin kuɗi.
Batun Tasirin Rikicin Gabas ta Tsakiya:
Shugabar Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), Kristalina Georgieva, ta ce ƙasashen da ke fitar da mai k**ar Nijeriya za su fuskanci ƙarancin illa idan aka kwatanta da masu shigo da mai.
Rahoton IMF ya nuna cewa rikicin ya shafi duniya baki ɗaya, amma tasirin ya fi tsanani ga wasu ƙasashe fiye da wasu.
Georgieva ta ce:
“Dole ne mu fahimci yadda wannan girgiza ke shafar tattalin arziki da kuma matakan da za su rage raɗaɗin da yake haifarwa.”
05/05/2026
Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a Paris
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan masu zuba jari na duniya a birnin Paris na ƙasar Faransa, inda ya jaddada aniyar gwamnatin sa na tabbatar da gaskiya, adalci, da kuma kiyaye ka’idojin kashe kuɗi. Shugaban ya kuma bayyana dalilan da s**a sa aka aiwatar da garambawul ga tattalin arziki cikin gaggawa.
A yayin taron, Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, ya bayyana nasarorin da Nijeriya ta samu, inda ya ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kashi 11.2% (idan aka lissafa da dalar Amurka) a shekarar 2025.
A cewar sa, wannan ci gaba ya nuna cewa burin Nijeriya na ganin tattalin arzikinta ya kai darajar dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030 zai iya tabbata. Oyedele ya kuma lashi takobin cewa gwamnati za ta riƙa wallafa bayanan kuɗi na kowane bayan watanni uku domin tabbatar da gaskiya.
Muhimman Abubuwan Da Aka Tattauna:
• Bashin Ƙasa: Shugabar Ofishin Kula da Basuss**a (DMO), Patience Oniha, ta tabbatar wa masu zuba jarin cewa gwamnati tana amfani da bashi ta hanyar da ta dace kuma za ta tabbatar ba a jefa ƙasar cikin halin kaka-ni-ka-yi ba.
• Tsaro da Man Fetur: Tinubu ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin gyara harkar mai don daina tafka asara, sannan ana shirin rarraba ikon rundunar 'yan sanda (decentralisation) don magance matsalar tsaro da kuma toshe hanyoyin samar wa 'yan ta'adda kuɗi.
• Makomar 2027: Lokacin da aka tambaye shi game da shirinsa na bayan shekarar 2027, Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da ƙarfafa tsarin tattalin arziki da tabbatar da cewa ba a canza manufofin da aka sa gaba ba.
Taron ya samu halartar wakilai daga manyan kamfanoni na duniya, ciki har da:
1. Citibank da Amundi (Faransa) karkashin jagorancin Valerie Baudson.
2. BlueCrest da Ninety One (Biritaniya da Afirka ta Kudu).
3. Kirkoswald Capital, Principal Finisterre, da PGIM (Amurka).
Masu zuba jarin sun yaba da matakan gyara da Shugaba Tinubu ya ɗauka, inda s**a nuna kyakkyawan fata kan makomar tattalin arzikin Najeriya.
05/05/2026
Tinubu ya taya Murtala Garo murnar zama Mataimakin Gwamnan Kano
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Alhaji Murtala Sule Garo murnar rantsar da shi a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a yau Talata.
Gwamnan ya naɗa Garo ne domin cike gurbin da Comrade Aminu Abdulsalam ya bari, bayan murabus ɗin da ya yi biyo bayan sauya sheƙar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.
Murtala Garo, mai shekara 48, gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo, Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu a ƙarƙashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Shugaban Ƙasa ya jinjina wa Gwamna Yusuf bisa wannan naɗin, yana mai bayyana cewa matakin zai ƙarfafa haɗin kan da ake buƙata a cikin sahu da jerin membobin jam’iyyar APC a Jihar Kano.
Haka kuma Shugaban ya yi kira ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki da su mara wa gwamnan da mataimakin sa baya domin ciyar da jihar gaba.
Ya buƙaci sabon mataimakin gwamnan da ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamna domin samar da shugabanci na gari da zai bunƙasa jihar.
A ƙarshe, Tinubu ya yi wa Garo fatan alheri a wannan sabon nauyi da aka dora masa.
Hotuna:
Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa a fannin yaɗa labarai, Malam Abdulaziz Abdulaziz, tare da sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, Barista Sunusi Musa, SAN, da sauran jigajigan 'yan siyasa da manyan jami’an gwamnati, suna cikin shirye-shiryen rantsar da Garo a yau a Kano.
04/05/2026
Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Gwamnatin Tarayya tana so a haɗa gwiwa domin yaƙi da yaɗa labaran ƙarya
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta buƙaci a ƙara haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin magance barazanar yaɗa labaran ƙarya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja yayin bikin Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a Radio House.
Ya ce: “Wannan gwamnati ta ba da fifiko ga haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a kafafen yaɗa labarai da kuma abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin inganta aikin jarida mai inganci da kuma yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.”
Ya bayyana ’yancin ’yan jarida a matsayin muhimmin haƙƙi da kundin tsarin mulki ya tanada, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa kafafen yaɗa labarai damar gudanar da aikin su cikin ’yanci, tsaro da gaskiya.
“Gwamnatin Tarayya ta amince da ’yancin ’yan jarida, kuma za ta ci gaba da samar da yanayin da zai bai wa kafafen yaɗa labarai damar yin aikin su cikin ’yanci, tsaro da gaskiya,” inji shi.
Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai na ƙarfafa gaskiya da samun bayanai ta hanyar cigaba da hulɗa da kafafen yaɗa labarai, aiwatar da dokar ’Yancin Samun Bayanai, da kuma saka hannun jari a hanyoyin sadarwa na jama’a.
Ya kuma bayyana haɗin gwiwar Nijeriya da UNESCO wajen kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai ta Duniya (IMILI) a Abuja a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa ilimin kafafen yaɗa labarai da bayanai da kuma inganta sadarwa mai kyau a wannan zamani na dijital.
Ministan ya buƙaci ’yan jarida da su ci gaba da kiyaye ƙwarewa da ƙa’idojin aiki, yana mai jaddada cewa dole ne ’yancin aikin jarida ya tafi tare da ɗaukar nauyin da ya rataye a wuyan jama'a.
“Ainihin gwajin ’yancin ’yan jarida ba wai a cikin furucin mu yake ba, a cikin ayyukan mu yake, yadda ’yan jarida ke gudanar da aikin su cikin tsaro, yadda ake yaɗa bayanai cikin gaskiya, da kuma yadda jama’a suke amfani da su yadda ya k**ata,” inji shi.
A nata jawabin maraba, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem Ukaire, ta bayyana taron a matsayin wata dama ta ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta wayar da kan jama’a.
Ta yi kira da a ƙara haɗin kai tsakanin hukumomi domin magance ƙalubalen yaɗa labaran ƙarya, musamman la’akari da yadda kafafen sadarwa na zamani suke ƙara yaɗuwa.
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar ta ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gina tsarin bayanai mai ƙarfi da zai tallafa wa dimokiraɗiyya, haɗin kan ƙasa da cigaba mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar Sufeto Janar na ’Yan Sanda, wanda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Anthony Okon Placid, ya wakilta; da Darakta-Janar na DSS, wanda Daraktan Tsare-Tsare, M.O. Chukwuka, ya wakilta; da Babban Sakataren Hukumar Kula da Aikin Jarida ta Nijeriya, Dakta Dilli Ezughah; da kuma Shugabar Ofishin UNESCO a Abuja, wadda Shugabar Sashen Sadarwa da Bayanai, Ms Yachat Nuhu, ta wakilta.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
19 Chelsea Chibuzor Street Off NICON Junction Maitama
Abuja