Majalisul Azah
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Majalisul Azah, Digital creator, Abuja.
23/08/2025
ZAMAN MAKOKI WAFATIN MANZON ALLAH (S,A,W) DAGA GARIN GOMBE.
A yau asabar 29 ga watan safar aka Shiga rana ta biyu kuma ta qarshe na zaman makokin annabin rahama muhammad (s,a,w) wanda yan'uwa musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub El-Zakzaky (H) s**a saba gabatarwa duk shekara a cikin garin gombe.
Anfara da gabatar da waqoqi na juyayi (zikrah) daga mawaqa tare da amsawa da nuna alhini daga mahalarta.
Daga bisani sheikh muhammad adamu abbare ya cigaba da jawabai da cire darussa daga rayuwar ma'aikin (s,a,w) inda yake cewa manzon allah (s,a,w) shi haskene wanda ya haskaka ilimi da addinin musuluci a duniya bakidaya wanda ya zamo a lokacinsa ba inda labarinshi bai shigaba a fadin duniya.
Ya cigaba da cewa bayan wafatin ma'aikin Allah banu umayya sun ta qoqarin bata komai na addini tun aiko annabi har wafatinsa ta hanyar hadisan qarya da saka qiyayya na iyalan gidan manzon allah da muzan tasu a tsakanin al-umma Kuma abun baqin cikin da wasu sahabbansa akayi wannan ta'asar, musamman karya alkawarin mubai'a da s**ayiwa imam ali amirul mu'uminin (As) da barin jikin manzo(s,a,w) a kwance a cikin gida ba'amai sallah aka bizneshiba zuwa wajen nada sabon khalifa wanda a duk duniya ba wani malami ko sarki da aka taba yiwa irin wannan ace allah ya karbi rayuwarsa amma kafin akaishi saida aka nada sabon Khalifa babu shi amma sai manzo(s,a,w) saboda tsananin qiyayya, dama sauran abubuwan da s**a auku bayan wafatin manzo (s,a,w).
Daga qarshe Sheikh Muhammad abbare ya ja hankalin yan'uwa akan cewa kada mudauka cewa abinda aka yiwa manzon allah a wancan lokacin baza'a iyan yinshiba a wannan lokacin saboda haryanzu wannan rudani da qarerayi da akayi su ke aikin kuma suketa barna a cikin addinin musulunci, ta hanyar a sakama shakku akan jagora Kuma yace a kula.
Daga qarshe akayi addu'a tare da ziyarar Manzo (s,a,w) aka sallami kowa daga wajen majalisin.
Ga kadan daga cikin Hotunan majalisin.
'irar Gombe Media
29/Safar/1447
23/August /2025
08/08/2025
DAGA GARIN GOMBE:
-Ayau Juma'a 14 ga watan safar Yan uwa musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub El-Zakzaky (H) na garin gombe s**a gabatar da zikrah na qarshen watan almuharram wanda ba'a samu akayi saboda wasu Dalilai domin qarfafa Yan uwa akan al-amrin tattakin arba'een na abah Abdullah imam hussein (As).
Angudanar da zikran a fudiyyar Pantami tare da Yan uwa Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub El-Zakzaky (H) ,Tareda taken taron (Maudu'i) Allah ya baqanta rayuwa bayanka ya abah Abdullah, Inda malam Abdullahi abubakar yayi jawabai akan wannan Maudu'in tare da cire darussa daga cikin shi, Daga qarshe aka rufe majalisin da addu'a.
GA kadan daga cikin Hotunan
'irar Gombe Media
14/safar/1447
-8/August /2025
24/07/2025
SANARWA! SANARWAR!! SANARWAR!!!
Ana sanar da Ƴan'uwa na garin Gombe cewa gobe juma'a 25/07/2025, in Allah yakaimu, akwai gagarumar Muzzaharan tunawa da Waƙi'ar ƙudus na Shekarar 2014 wanda ake kira da (25 July), Muzzaharan zata farane da Misalin ƙarfe 2:00 na yamma bayan sallar jumma'a a masallaci ƙofar sarkin Gombe, ana bukatar duk wanda yake da tutar kasar Palesting ya tawo da ita.
Bayan kammala Muzzaharan ne, za'a ɗora da gudanar da Zikrar tunawa da gwarazan Shahidan wannan Rana ta 22 July a Muhallin Fudiyya Pantami da misali karfe 4:00 na yamma, kar a manta azo da baƙeken kaya.
'irar gombe Media
28/almuharram/1447
24/July/2025
Labbaika Ya Hussain(as)✊
Labbaika Ya El-Zakzaky(H)✊
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Abuja
Opening Hours
| 09:00 - 17:00 |